Skip to content
Part 17 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

“Baba ni ina son shi”

Hindu ta furta kalaman da ko a mafarki batayi tunanin zata iya gayawa Abba su ba, duk kuwa kusancin da yake tsakanin su, saboda kunya. Anty ma tun satin daya fita sai ta WhatsApp ta tura mata sakon cewa tayiwa Abba magana Hamza yace zai turo. Amman yau tura ce ta kai bango. Kiri-kiri take ganin yanda duka yan gidan suka juya mata baya kan maganar Hamza. Kuma Zaid ne, duk shi yaja da zancen binciken shi, batama ga matsalar shi akan maganar aurenta ba, yanzun ma da take tsugunne a gaban Baba idanuwanta cike suke taf da hawaye.

“Mahaifiyar shifa ba’a san asalinta ba.”

Zaid ya fadi, bayan wannan, har kauyane su Appa saida yasa aka bincika mishi, kuma ya samu tabbacin labarin su, kasancewar mahaifin Hamzan maraya. Amman ita mahaifiyar kanta batasan inda danginta suke ba tunda ta dawo Najeriya. A ganin Zaid ta fannin uwa da uba Hamza bashi da wasu dangi tsayayyu, sai yan uwan shi guda biyu. Duk da kowa a unguwar ya bada shaida me kyau akan mahaifin Hamza, haka shi kanshi Hamzan duk da ance yana da zafin rai, amman abin hannun shi bai rufe mishi ido ba tun bayan samun shi.

Kawai akwai wani abu tattare da Hamzan ne da yaki kwantama Zaid shisa ya labe bayan rashin tsayayyun dangin da Hamza bashi dasu ya cewa Anty ayi mata magana ta hakura. Amman ta kafe, shisa ma yazo da maganar wajen Baba.

“Kai da bakin ka kace kowa ya fada maka iyayen shi mutanen kirki ne.”

Hindu tayi maganar tana share hawaye.

“Ta shi kije abinki.”

Baba ya fadi, ta kuwa mike dan bataga wanda ya isa yasa ta rabu da Hamza akan wannan dalilin ba, balle yanda yake nuna mata kauna a cikin satin. Kusan kullum sai yazo makarantar su, dan ma batada wani lokacin da zasu fita, haka suke takawa cikin makaranta suna hira, tana bala’in jin dadin yanda ake binsu da kallo cike da sha’awa. Tana kuma jin dadin yanda ko abu ya sai musu shi yake rikewa, kuma har kofar aji yake rakata, su gaisa da wasu cikin Malaman da suka san shi, dan ya farfada musu ita ce zai aura. Da yawa a ciki kuma sun nuna jin dadin su da maganar.

Shine Zaid zai yi mata kafar ungulu a cikin lamarinta. Ita zata zauna da Hamza, idan rashin tsayayyun dangin shi bai dameta ba, bataga dalilin da zaisa ya dami kowa ba.

“Yana da asali me kyau Zaid, tana kuma son shi. Babu wani dalili mai kwari na hana mishi aurenta…”

Baba ya fadi, numfashi Zaid ya sauke.

“Wallahi Baba akwai wani abu a tattare dashi da baiyi mun ba, na rasa mene ne, amman har raina bana son shi da Hindu, in dai za’a bi shawarata a hakura. Allah ya kawo mata wanda yafi shi.”

Murmushi Baba yayi, yana da tabbaci duk yanda Zaid yake kaunar Hindu bai kai shi ba.

“Babu wani abu a tattare dashi banda kaunar kanwar ka da kakeyi, kuma wannan shine soyayyar da zaka nuna mata, kasan tunda mace ce dole irin ranar nan zata zo daman….da zaka mikama wani amanarta.”

Kai Zaid ya jinjina, Allah ne shaidar shi, yayi duk kokarin da zai iya. A wannan matakin yanajin addu’a ce kawai take rage mishi.

“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi.”

Ya furta.

“Amin. Yawwa, ko kaifa.”

Mikewa kawai Zaid yayi ya fice daga dakin Baban yana nufar nasu Hindu, kwankwasawa yayi hadi da sallama, sai da yaji ta amsa mishi tukunna ya tura dakin ya shiga. Tsaye yayi a bakin kofa yana kallonta, yanayin fuskarta ya tabbatar mishi da cewar kuka tayi.

“Nasan kina jin haushina, kina ganin kamar na shiga abinda ba hurumina ba, ba ko yaushe nake jin abu akan mutum bai zamana gaskiya ba. Ina miki fatan alkhairi a ko da yaushe, Allah ne shaida bayan Anty da Baba, kece ta farko a cikin jerin sunayen da suke fita bakina duk sujjadar da zanyi.”

Haka kawai tunda ya fara magana take jin hawaye na zubar mata, da batama yi kokarin goge su ba, tunda taji suna tukundedeniya da juna wajen fitowa tasan bata isa ta tsayar da su ba.

“Yanzun ma bazan daina ba, Allah yasa shine alkhairin ki. Nasan kuna tsorona, kuna ganin kamar ba zaku iya tunkarata da kowacce magana ba, Hindu wayata kawai zaki kira idan kina bukatata, kina jina? Kar halina ya taba nisantaki da neman taimakona idan kina bukatar hakan”

Bai jira amsarta ba ya fice daga dakin, saboda bayason kukan da takeyi. Gabaki daya sai taji maganganun shi sun karya mata zuciya, tana so ya yarda da zabinta, tana so ya yarda tayi hankalin da zata san abinda ya kamace ta da akasin hakan. Ta jima tana kuka kafin taje ta wanko fuskarta. Tana dawowa taga wayarta tayi haske, dauka tayi ta duba, taga Baba ne yai mata text.

“Ranar juma’a ko asabar, sai su zabi daya. Ki sanar dani.”

Murmushi tayi, zuciyarta na samun natsuwa, itama text din ta tura ma Hamza.

“Baba yace ko juma’a ko asabar.”

Dan ya matsa mata da maganar har fada sukayi da tace mishi Baba yace a dakata tukunna.

“Ki fada musu, Hindu ki fada musu bazan iya rabuwa dake ba gara ma su bani dama in turo.”

Shine abinda ya fada mata, yaki kwantar da hankalin shi duk yanda take kokarin ganin ta kwantar mishi da shi

“Yau baccin da zanyi daban ne.”

Ya dawo mata da shi yana dorawa da

“Zan kira ki.”

Suna Kano tun ranar alhamis, yau litinin, kwanan su hudu, sosai tayi kewar shi, duk video calls din da sukeyi, duk kuma aikin da yakeyi sai ya mata ko da text ne. Haka ta wuni a daki, daman karatun jarabawa takeyi, Hamza yace karta bashi kunya, mutane biyu kenan yanzun a rayuwarta da bataso suga gazawarta ta fannin karatu, shi da Baba. Basu kara waya da shi ko magana ba har dare, tunda ta fita taga irin kallon da Anty take binta da shi ta rufama kanta asiri tayi zamanta a daki. Abincin dare ma Asma ce ta zubo musu, Hindu na ganin ita Anty tabi maganar Zaid batare da ko Hamza tagani ba, balle ta bashi dama ya nuna mata yanda suke kaunar junan su, kuma ba haka bane ba, kamar yanda Zaid yakeji Hamza yaki kwanta mishi haka itama Antyn, sai dai tana addu’a sosai akan maganar.

Gajiya tayi ta yanke hukuncin lekawa whatsapp dinta taga ya ake ciki, ko group din ajine ma ta shiga, ba za’a rasa abinda zai sakata dariya ba, dan shaftar su bata karewa sam. Haka suke fama kullum, status ta shiga, ta ga Hamza ya saka minti daya daya wuce, ba sosai yake saka status ba, yana iya sati daya bai saka ba, idan yasa ma bazai wuce zane ba, ko hoton su shi da su Fodio. Budewa tayi tana cin karo da hoton AbdulHafiz da Nabila, tana sanye da alkyabba, shikuma da manyan kaya, kanshi nade da rawani, sunyi mata kyau na gaske, har ranta tana son ganin fuskar Nabila gabaki daya.

Yanzun ma idanuwanta kawai take iya gani

“Wedding bells”

Hamza ya rubuta, yana saka Hindu tambayar

“Bikin shi ya matso ne?”

Kafin tayi gaba tana sake ganin wani hoton

“Saraki na Fulani. Allah ya kaimu lokacin”

Sai take ji kamar ta janyo juma’a ko asabar, tasan ranar da zata fara duba kasancewar irin hakan a tata rayuwar, sauran hotunan ta gama gani da sukai matukar yi mata kyau, kafin taga Hamza ya amsata

“Eh saura kwana talatin, sun sa ina jin kamar ace namu ne.”

Murmushi Hindu tayi, kafin ta amsa shi ya sake fadin,

“Nace ma AbdulHafiz sai munfi su yin kyau, yana mun musu.”

Sosai ta murmusa yanzun, ya sosa mata inda yake mata kaikayi, tunda suka fara maganar aure tagane Hamza na da burin biki dai-dai da nata.

“Ka kyale shi, zamu bashi mamaki in shaa Allah.”

Ta amsa.

“Allah yasa alkhairi, kace ina mishi fatan alkhairi.”

Ta fara rubutu, kiran shi ya shigo, ta daga ta kara a kunnenta

“Ga AbdulHafiz din ki fada mishi da kan ki.”

Hamza ya fadi, kafin ta numfasa taji sallamar shi data amsa a kunyace

“Ina wuni… Ya aiki?”

Ta fadi muryarta can kasa

“Alhamdulillah. Ya makaranta?”

Amsa shi tayi da,

“Mun gode Allah. Allah yasa alkhairi ya kaimu lokacin lafiya.”

Bata taba tunanin murya zatai mata kwarjini haka ba sai yanzun da taji ta AbdulHafiz, kuma a cikinta zaka fahimci natsuwar da take tattare da shi.

“Amin thumma amin. Na  gode. Allah ya kaimu naku. Ga Hamzan.”

Tana jin muryar Hamza tace

“Ban shirya ba kawai ka mika mishi wayar.”

Dariya ya yi

“Wai me yasa AbdulHafiz yakewa mutane kwarjini haka?”

Wannan karin ita tayi dariyar.

“Yaushe zaka dawo?”

Zata iya rantsewa girar shi ya daga mata kafin ya amsa

“Bawani nan, sai yau? Ba kinayi kamar ni kadai nake kewarki ba.”

Runtsa idanuwanta tayi tana sake bude su, ta tsokalo ma kanta rikici.

“Yi hakuri, ina kewarka Allah. Yaushe zaka dawo?”

Saukar da murya yayi.

“Ban sani ba fa, kinga bikin AbdulHafiz ba’a saka da yawa ba, idan mun dawo zamu fara hidimar tafiya Gombe ne, gara mu rage aiki sosai sosai. Gobe dai zanyi magana da Appa, sanda zan dawo in shaa Allah muna kirga kwanakin bikin mu”

Murmushi tayi.

“Allah ya kaimu, yanzun zan kara wasu satika ban ganka ba?”

Tayi maganar, kewar shi na danneta, kamar tayi fuka-fuki taje Kano tagan shi ta dawo.

“Zaki ganni harki gaji idan na dawo, In shaa Allah. Idan bakiyi bacci ba zamu karayin magana, yanzun zamu fita dasu AbdulHafiz.”

Kai ta jinjina mishi tana dan sauke wayar daga kunnenta taga tara da rabi.

“A dawo lafiya, ka kula da kan ka, kace Fodio ya kulamun da kai.”

Tanajin dariyar shi ta cikin wayar kafin ya kashe, yanzun harta saba da yanayin yanda Hamza ya kare wayoyin shi, baya jiran sallama, daya gama fadar abinda zai fada yake kashewa. Sauke wayar tayi da murmushi a fuskarta, Instagram tahau dan tasan yau zata ga soyayya, tana hawa shafin AbdulHafiz din ta fara zuwa, ta kuwa ci karo da hoton daya dora, na Nabila din, an saka shi a baki da fari, da alkyabba a jikinta, da alamu a zaune take, ta daga hannunta ta kare rabin fuskarta da shi.

“Allah ya bani aron rayuwa mai tsayi a tare da ke Fulani, ban tana tunanin kwanaki talatin zasuyi mun yawa har haka ba.”

Zuciyarta Hindu taji ta cika fam, kamar ta sace AbdulHafiz din haka take ji, wani irin burgeta kalar soyayyarsu takeyi, amman ko da wasa har yanzun Hamza bai taba saka hotonta ba, kwanaki ya saka na Mansy a avi din shi, tabi ta cire, ta jira yayi mata magana yanda zasuyi tashin hankali, sai baice mata komai ba. Ranta yayi matukar baci, har yanzun idan ta tuna sai taji ran nata ya kara baci. Musamman idan tazo taga AbdulHafiz din yanda duke gurzar soyayyar su shida Nabila, ta tabbata ita take kara musu yawan mabiya a Instagram din. Fita tayi tana komawa shafin Nabila, hotuna biyu ne ma ta saka, wani jiya, wani kuma yau.

Na jiyan ta fara dubawa, AbdulHafiz ne zaune a cikin mota, da murmushin nan har dimple din shi ya fito sosai .

“Bacci ya kaurace ma idanuwa na, ina jiran wayewar garin da zata kusanta ni da zama taka.”

Bude comment section din tayi, tana lalubo na AbdulHafiz da tasan dole ne sai yayi magana.

“Soyayyar ki alkarya jikar Shehu.”

Tashi zaune Hindu tayi, tana tunanin yanda za’ayi su fara wannan soyayyar da Hamza. Hoto na biyu ta shiga, ita da AbdulHafiz dinne,a wani falo, tana zaune akan kujera ya tsaya daga bayanya ya daga yatsun shi guda biyu yana dariya.

“Saraki”

Kawai ta rubuta sai hoton zuciya. Shima kuma da hoton zuciyar ya bata amsa, ko da bata saka komai ba, yanayin hoton zai fada maka kalaman da basu rubuta ba. Sai take jin kewar Hamza ta danneta fiye da kullum. Twitter din shi taje tana kai daman, taga Mansy tayi tagging din shi a wani abu da yaren fulatanci, tsaki taja, ta duba DM din shi tana ganin sakon Mansy din

“Na kira ka baka dauka ba. Ina kewar ka sosai.”

Wannan karin tsakin da Hindu taja sai da Asma da take kwance, kunnuwanta manne da earpiece ta juyo tana cire guda daya ta kalli Hindun.

“Ba dake nake ba.”

Hindu ta fadi, Asma ta mayar da earpiece dinta, dan mp ce ma, ta saka karatun Qur’ani tana bi dan yafi mata sauri wajen rikewa, kafin lokacin da zasu bayar da hadda yazo sai taga har taci karfin karatun.

“Wawiya kawai, mata sai kace mayya.”

Hindu take fadi kasa-kasa kafin ta goge sakon. Yanzun haka takeyi mata, in dai zata ga sakonta sai ta goge, idan tayi unfollowing da blocking da Hamza yahau yake sake following ya budeta, sai ta kyale shi, sakone in ba ya rigata hawa ba sai dai suyi waya. Gabaki daya Mansy ta gama bata mata rai, tana cikin farin cikinta, da ta sani ta tsaya ma taci gaba da kallon soyayyar su AbdulHafiz da yafi mata, addu’a tayi tana juya kwanciya, taja ma Hamza, ba zata jira shi ya dawo ba. Baccinta tayi cike da mafarkin bikin su da Hamzan.

*****

Basu dawo Kaduna ba sai satin bikin AbdulHafiz, washegari zasu wuce Gombe, shisa suna isowa ya fara sauka gida dan yaga Anna, ruwa kawai ya watsa, yaci abinci ya bar gidan, sallar Magriba ma a hanya ya tsaya yayi. Hindu kawai yake son gani har wani iri yake ji saboda kewarta. Ranar da yayi wa Anna maganarta, tambayar farko da tayi mishi shine

“Yar gidan wacece ita din?”

Dan bataso ya dauko yarinyar da zata saka mishi ido a abinda yake da shi, yarinyar da kudin shi zai zame mata abin alfahari, tafi son yarinyar duk da zai dauko mata a matsayin suruku, kudi ya zama dalili aqalla na biyu na auren shi, hakan zai rage mata tsoron za’a shiga tsakaninta da danta. Duk bayanin da Hamza yayi mata kasa samun natsuwa tayi, har sai da Appa ya tabbatar mata da cewa yarinyar yar mutunci ce, kuma suna da tasu wadatar dai-dai misali. Auta ce ma ta tsare shi da tambayoyi sai da ya zageta

Yana son su, Allah ne shaida zai yi komai saboda kannen shi, sune dalilin farko na sakashi jajircewa wajen ganin ya samu kudi, saboda bayaso su sha kalar wahalar dashi ya sha, yana so komai yazo musu da sauki, amman ba zai dauki su saka mishi ido akan abinda na huruminsu bane, ko hotonta da Auta tace ya nuna mata haka yace mata.

“Me zakiyi da shi? Saurin me ki ke yi?”

Dan murmushi autar tayi.

“Kawai zan ganta ne, ko ta dace da kai.”

Girar shi ya daga mata duka biyun yana daure fuska sosai.

“Kina so ki bani kunya ne Auta? Kina so ki zama irin kannen mijin da suke kushe zabin Yayyen su ko? Ni ban san abinda ya dace dani ba sai kin tayani? Bana so, kina jina? Zamuyi fada dake sosai idan kika fara wannan halin.”

Ko Anna da ta dinga mishi tambayoyi akan Hindu dole ce ta saka shi amsawa, Anna ce, babu yanda zaiyi da ita. Amman ya tsani yanda ake magana akan dangin miji, bayason yanda suke yankewa yaran mutane hukunci batare da sun basu damar nuna asalin halayen su ba, sai kaji daga ganin hoto ana fadin,

“Ga idon ta na a tsaye, da ganin wannan yarinyar fitsararriya ce.”

Sai anje lahira an saka su a layi su farayi kamar masu ciwon asma, babu wata kwakkwarar shaida sai suyita yanke ma yaran mutane hukunci, ba tun yanzun ya saka a ran shi soyayyar da yake ma su Auta ba zata sa ya basu fuskar da zasu raina mishi yarinyar duk da zai kawo a matsayin mata ba, koya take kuwa, idan harya ce itace zabin shi dole su girmama hakan. Da Appa ya nemi zabin shi akan ko wata nawa ya kamata a saka, haka yace a tambayi Anna daman, ita kuma tace ko wata uku ko biyu, dan ta kaku taga Hamzan ya nutsuwa waje daya.

Wata ukkun kuwa akasa ana dai-daita shi dana Khadee, sosai Hamza ya natsu akan karasa gidan shi, da suka tafi Kano ma Abdallah ya bari kan komai tunda batare dashi aka je ba, kuma ginin yana tafiya kamar yanda ya tsara abin shi, tare kuma da kudaden da suke ajiye a bankin shi. Tunda aka saka ranar kullum cikin maganar yanda bikin zai kasance suke yi shi da Hindu, dan biki yake so ayi na kece raini, tunda harya yanke hukuncin yin aure, kowa zai shaida yayi aure. Wani numfashi ya sauke da yayi parking din motar shi a cikin gidansu Hindun yana kiran wayarta ya fada mata ya iso.

Kafin ta karaso ya fito daga cikin motar, tana ajiye kujerun da ta dauko musu taji ya rike hannunta, kafin tayi wani yunkuri ya riketa a jikin shi yana sauke numfashi.

“Na yi kewarki…”

Kwacewa tayi jikinta na bari, sai ware mishi idanuwa takeyi har yaja kujera ya zauna, sai da ya sake kama hannunta yana zaunar da ita. Gani takeyi kamar wani yagan su, ga wa’azin da Khadee ta turo mata shekaranjiya kan yan mata da samarin da suke wannan ‘yan rungume rungumen zamanin kafin aure. Sai taji kamar dan ita da Hamza akayi wa’azin, ko da hannunta ne sai ya rike duk yanda zata nuna mishi bataso, tun da aka sa ranar kuma tayima kanta alkawari daman ba zai sake tabata ba, balle da taji yanda albarkar auren duk take zirarewa tun kafin ayi shi, ga tarin rashin yardar da yake biyo bayan auren.

Banda zunubin da in ba tuba sukayi ba, sahihin tuba irin wanda ta dingayi kafin ya dawo yanzun nan cikin wasu dakika ya kwance mata hannun agogo yana dawowa da shi baya, tayi niyyar har sai ta zama mallakin shi inda duk wani riko da zaiyi mata zai zamana cike da lada.

“Bansan sau nawa kake so ince maka ka daina tabani kafin kaji ba, kana ta zubar mana da albarkar auren.”

Numfashi Hamza ya sauke, da tasan yanda yake kokawa da kanshi a duk rana akanta da bata ce mishi haka ba, da tasan irin matan da yabi a Kano dan in yazo karya riketa da bataga gajen hakurin shi ba, itace mace ta farko da yake kasa controlling kan shi a kanta.

“Bana so inyi fada da ke nikam, nayi kewarki da yawa.”

Ya fadi yana gyara zaman shi hadi da zuba mata idanuwan shi, hakan yasa ta danyin murmushi, itama bata son yin fadan da shi.

“Nima nayi kewarka ai.”

Dan tabe mata baki yayi, tana ganin yanda yanayin ya kara mishi kyau.

“Bawani, saura kwana 72 a daura mana aure.”

Dariya Hindu tayi

“Kai ko?”

Ta fadi, yana da kuna mata fuska.

“Ke baki damu ba shisa ba kya lissafawa, nikam dana damu kinga ina kirgawa ai.”

Ya karasa maganar yana saka hannu a aljihun shi ya cire zoben daya siya. Azurfa yaso siya, Fodio yace ya sai mata gold zaifi duk wani tarkacen tsaraba da zaiyi mata, yaga mata naso, dan kanwar Fodio din suka kira suka shiga kasuwa tare. Dubu dari da goma wanda ya siya, badan bashi da halin siyan wanda yafi shi ba, kawai sauran sun mishi girmane sosai, wannan din dai yafi mishi kyau sosai, in an tashi hada lefe ya saka mata wani a ciki, Anna ma tace mishi za’a saka.

Hannunta ya kamo, kafin tayi magana taga ya kama yatsanta na biyun yana zira mata zobe, kasa mishi magana tayi, ta ware idanuwanta ganin yanda zoben yake daukar ido a cikin hasken lantarkin da yake gauraye da gidan.

“Bansan me zan siyo miki ba.”

Ya furta yana dago hannunta ya kalli zoben a jikin yatsanta.

“Karki cire, nasan karami ne, zan sai miki wanda ya fishi girma.”

Kallon shi tayi, wata irin soyayyar shi na cika mata zuciya fam, kafin a hankali ta zame hannunta daga cikin nashi, tana dago yatsunta, gyara ma zoben zama tayi, tana dan kara matse shi dan mai adjusting ne, ya zauna mata daras kamar dan hannunta akayi.

“Ban san me zance ba.”

Ta furta, dan godiya tayi kadan.

“Kice kina sona.”

Ya furta yana sake rike hannunta.

“Ina son ka.”

Ta fadi, tana saka shi dan dumtsa hannunta da yake rike da shi.

“Bai fito daga zuciyarki ba.”

Murmushi ta yi.

“Ni na fada maka haka?”

Kai ya jinjina.

“Ni ne naji a muryar ki… Ki sake fadamun, ya fito daga zuciyar ki kamar yanda nake fada mishi.”

Numfashi Hindu ta sauke.

“Ina son ka.”

Murmushi ya yi yana sumbatar hannunta hadi da mikewa, ya tabbatar wayar shi daya bari su Fodio sun mishi kira yafi goma, tunda akwai abubuwan da zasuyi kafin goben su wuce Gombe.

“Ina zaka je?”

Ta bukata tana shagwabe mishi fuska.

“Kin gani ko? In rike ki kice nayi laifi, bayan ke kike karamun son ki.”

Hamza ya fadi yana kallonta, murmushin da tayi na saka shi sauke numfashi.

“Su Fodio na jirana, zamuyi abubuwa da yawa. Zan kiraki, dan Allah kiyi hakuri, dana dawo zaki samu lokaci na.”

Kai kawai Hindu ta iya daga mishi, ya mika mata hannun shi, duk yanda zuciyarta take mata ihu, sai da ta mika mishi nata hannunta ya taimaka mata ta mike.

“Ki kulamun da kanki. Ina son ki da yawa, kin san hakan ko?”

Kai ta daga mishi, hannunta ya sumbata kafin ya saki yana zagayawa ya shige motar shi, kujerun ta hade waje daya tana jansu gefe, kafin ta wuce gida. Sai da safe zata nuna ma Anty zoben, dan tasan yanzun tana wajen Baba, zata yi fada tace ita duk irin wannan gara ya bari saiya aureta, amman abune da ko an sami matsala za’a iya mayar mishi da abin shi tunda ba siyarwa za’ayi ba, tasan Anty zata bar mata abinta, wayama da Hamzan ya sake mata, Anty ta fara fada, Zaid da kanshi yace ta kyale mata wayar, idan biyane ma Allah ya rufa musu asiri za’a iya biyan shi. Haka tayi zaune tana kallon hannunta, sai da ta hau whatsapp dan ta fada mishi yanda taji dadin kyautar, tana lalubo lambar shi, zuciyarta tai tsalle, ware idanuwa tayi tana bude profile din shi.

Ba gizo idanuwanta sukayi mata ba, hotonta ne a dp din Hamza, a karo na farko daya saka hotonta, da sauri ta wuce Twitter din shi tana ganin ya saka hotonta a header din shi, bai dai saka a avi ba. Kwanciya tayi kafin shauqi yasa ta narke, ita kadai take murmushi, ta kasa daina kallon kanta a header din shi na twitter, ta tabbata Mansy zatayi kwana bakin ciki yau.

“Tsohuwar mai tallar goro yau za’a kwana ana juyi.”

Ta furta a ranta, tanajin kamar taga Mansy din ta fada mata yanda Hamza yayi mata nisa har abada, yanda Hamza nata ne ita kadai, ba kuma zata rabashi da kowace mace ba, sai dai su kalla daga nesa subar mata abinta.

Next >>

<< Mijin Novel 16Mijin Novel 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×