Skip to content
Part 23 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Tunda Hamza ya tashi wajen karfe hudu tana jin shi, sai da ya fice daga dakin tukunna ta bude idanuwanta. Akwai wani abu da ya zo yayi mata tsaye da bashi da alaka sam-sam da abinda ya faru shekaranjiya. Tasan jiya ne ya zame mata daren farko, da shima yazo mata ba’a yanda ta tsammata ba. Har ranta taso jin yanda ita din take daban da sauran matan da take da tabbacin Hamza ya yi mu’amala da su a baya, taso ya fada mata ita din daban ce, ko dan mutuncin ta da ta kawo mishi. Ta so jin tarin alkawurra a bakin shi, a kasan irin wahalar da tasha, kunnuwanta a bude suke cike da shirin jin duk wannan abubuwan.

Bata ce sai ya bata kujerar makka kyautar kawo mutuncinta ba, duk da tasan yana da halin hakan, amman idan ya fada mata yanda ita din daban ce, yanda bai san abinda ya dingayi da rayuwar shi kafin ita ba zata ji dadi. Gaya mata ya samu duk abinda yake nema a jikin mace a tare da ita, yayi mata alkawari cewa tunda gata, shi da wasu matan sai dai kallo daga nesa, yanda ta tsammaci zai rikice a kanta ba haka taji abin ba sam-sam. Ga labaran da ta dinga ji da wanda ta dinga karantawa kala-kala, sam basu ko da kusan karya gado yanda ta hasaso ba, bata majin idan akwai mutum a dayan dakin zaiji su.

Jin shigowar Hamza yasa ta saurin lumshe idanuwan ta. Shikam kaya yaje ya dauko daga bangaren shi, a kan gadon daga gefe ya ajiye su yana wucewa bandaki. Da gaske ne akwai nutsuwar da tazo mishi tare da macen da ta kasance ta shi, halalin shi, bai tashi da Hindu manne a kirjin shi yanajin wata irin dauda ba. Kuncin da kan ziyarce shi duk lokacin da yabi sauran matan da dana sanin da yake ji sam babu su yau, asalima sai yake jin shi daban, ita ma Hindun sai ya jita daban. Ba sai wani ya fada mishi dan ita din halalin shi bace ba. Sai dai a kasan duk wannan yana tunanin ace ya sami mata masu yawan gaske da zasu zama halalin shi.

Sai dai tunda shi ba basarake bane ba, musulunci hudu ya halarta mishi zai iya samu ta wannan hanyar, ko a mafarki kuwa bai hango kan shi da mata hudu ba, yana da halin rike su, amman ba zai iya ba. Da ace kwana bibbiyu ne, idan yayi hudun za’a kwashe su a zuba mishi wasu kamar yanda ake kiwon kaji zai so hakan. Har cikin kasusuwan jikin shi yake jin wani irin tsoro na ziyartar shi, sau daya ya kasance da Hindu, amman kamar ba zata rike shi ba, ita din kadai ba zata yi mishi ba. Ba kuma yason inda tunanin shi yake kai shi, shisa ya sakar ma kanshi ruwan sanyi, yana yin tsalle gefe babu shiri, hadi da mika hannu ya kashe shawa din yana maida numfashi. Ruwan ya yi mishi bala’in sanyi, dole ya dai-daita zafin.

Bai fito ba saida ya dauro alwala, ya zame towel din jikin shi yana sake kaya, zuwa lokacin yana jin kiran sallah kasa-kasa. Kafar Hindu ya fara bubbugawa a hankali, su duka ba wani baccin kirki suka samu ba, amman idan tayi sallah sai ta sake komawa, shima idan ya dawo ya gama tilawa da azkar din shi bacci zai koma.

“Hindu…”

Ya kira a hankali yana sake dan dukan kafafuwanta, tana jin shi tunda ba bacci take yi ba. Wani malolon bakin ciki ne taji ya taso mata, ya za’ayi a darenta na farko ya dinga tashin ta kamar tana gidan su. Ko Asma tasan ta tsani a bubbuga mata kafa in za’a tasheta, tama tsani a bubbuga mata ko ina, tunda ba nauyin bacci gareta ba, idan ka kira sunanta ma zata ji. Ya yake so tagane banbancin auren da tayi da kuma gidansu, ita yanzun tana da miji, yanda ta hasaso zai dinga tashin ta daban da yanda yazo yana tashinta yanzun.

Ta dauka daya fito wanka zaizo gefenta ya zauna, saukar ruwan da yake digowa daga sumar shi zata fara ji a wani bangare na fuskarta, kafin lausasan labban shi kan goshin ta yana kiran sunanta cike da soyayya, baya zo yana bubbuga mata kafa yana kiran sunanta gatsau irin haka ba.

“Hindu…”

Tana jin shi sarai, idanuwanta sun fara tara hawayen bakin ciki.

“Hindu ki daure ki tashi, in kikayi sallah sai ki koma baccin.”

Hamza ya fadi yana balle maballan jikin rigar shi, kafin ya kara matsawa yana zama gefen gadon, taji shi, ashe ya iya irin wannan zaman yai mata kerere.

“Hindu…”

Ya kira a hankali yana dora hannun shi a jikinta hadi da dan girgizata, sai lokacin ta bude idanuwanta a hankali tana sauke su cikin nashi, kwan fitila daya ya kunna, babu wadataccen haske a dakin, amman ya isa taga yanda yayi wani irin kyau, fuskar nan fayau da ita, kamar ta kai hannu ta shafi sumar da take kwance luf-luf akan fuskar shi

“Wani abu na miki ciwo?”

Ya tambaya cikin taushin murya, kai ta dan daga mishi a hankali.

“Sannu, tashi ki samu kiyi sallah.”

Ya karasa maganar yana mikewa, hadi da kama hannunta, ya taimaka mata ta mike daga kan gado, hannunta na cikin nashi harta tashi, tana kokarin langabewa a jikin shi ya tare ta.

“Karki karyamun alwala Hindu.”

Shagwabe fuska tayi, idanuwanta cike taf da hawaye, bai kamata sam yace ta samu tayi sallah ba, ina laifin ma tunda ta tashi ya dauketa ya kaita bandakin, wankan ma daya jirata sunyi tare.

“Ni jikina ciwo yake mun.”

Kallonta ya yi, yasan dole jikinta zai mata ciwo, amman ba kamar yanda take nuna mishi ba, shagwaba ce kawai take son yi mishi ba wani abu ba, yasan me yake yi, ba ita bace cikakkiyar macen daya fara kasancewa da ita ba. Hannunta ya dumtsa yana janta zuwa hanyar bandaki, gabaki daya sai langabe mishi take yi, a dole da kyar take iya taka kafafuwanta.

“Hindu masallaci zan tafi fa…”

Hamza ya fadi, haka kawai ya ji dariya nasan kubce mishi, inda yasan wannan rainin hankalin zata yi mishi, daya bata dalili mai karfi nayin hakan. Kallon shi tayi, sosai idanuwanta suke cike da hawaye, shi da yake da sabuwar amarya ina yaga ta fita masallaci.

“Ban hanaka ba ai.”

Ta karasa maganar muryarta na karyewa, numfashi ya sauke, yana rasa abinda ya kamata ya yi, after care din nan sam ba sabon shi bane ba, mace ma bata dade mishi harya tsaya yana lallabata, bai saba ba, komai yana mishi wani iri. Hannun shi ya zare daga cikin nata tunda yana da tabbacin babu abinda ba zata iyayi da kanta ba.

“Yanzun zan dawo, kisa ruwa mai dumi sosai ki yi wankan.”

Ya karasa yana juyawa, cike da mamaki Hindu take binshi da kallo, da gaske ficewa Hamza ya yi daga dakin, da gaske ba zai tayata yin wankan ba, balle tasa ran zai nadota da towel ya daukota ya kawota ya kwantar. Hawayen da suka silalo mata tasa hannu ta share, ta lallaba tana shiga bandakin, shawarar shi ta dauka tayin amfani da ruwa mai dumi sosai. Kafin ta fito kam har jikinta ya yi mata dadi. Doguwar riga ta samu ta saka, ta gabatar da sallar asuba, tana zaune tana azkar, harta idar ta karanta Qur’ani shafi biyu Hamza bai shigo ba. Hakan yasa ta jan jikinta ta mike, hijab din ta cire ta ninke, tana komawa kan gado ta kwanta.

Duka yanda ta hango safiyar yau ba haka tazo mata ba. Ita ma ta hango bayan Hamza ya nado ta ya fito da ita, ya sami kaya ya saka mata ya kums gama lallashinta. Ta mike tayi sallah, kanta tsaye gaban mudubi zata yi ta tsantsara mishi kwalliyar da zata sake rikita shi. Amman ko mai bata shafa ba, turare ma sabo dayi ne yasa tadan fesa ta cikin rigar jikinta tun kafin tayi sallah. Amman baccin da take ji a idanuwanta da kuma disappointment din da ya danneta bai barta da wani zabi ba. Zata dora laifin akan Hamza, daya bata kwarin gwiwa da tayi kwalliyar, tana wannan mitar a ranta bacci ya yi awon gaba da ita.

*****

Sosai take jinta daban, komai na yi mata wani iri, da sanyi-sanyi takeyin komai, jiyan bata zo mata da wani yanayi ba. Sun fita da rana suka ci abinci ita da Hamza. Amman fitar da suka yi da dare tayi mata dadi ba kadan ba, har Havila ya biya da ita ya kwaso mata ice cream. A bangaren shi suka kwana, bata samu dukkan abinda tayi tsammani ba, amman ta sami wani abu daban. Yau kuma tunda suka yi asuba suka koma bacci, basu tashi ba sai wajen goma da rabi, dukkan su wanka sukayi, tunda da dare ya fada mata zasu je su gaishe da Anna. Haka kawai sai zuciyarta ke mata rawa, fargaba na saukar mata.

Ta zabi kaya sunfi kala biyar tana mayarwa, har saida Hamza yace mata.

“Ki kwantar da hankalin ki, Anna bata da matsala.”

Kallon shi ta yi.

“Me zan kai mata? In kai mata turare?”

Dan jim ya yi, kafin ya daga ma Hindu kai, yasan Anna da kamshi, zata so turare. Kai Hindu ta jinjina mi shi.

“Dan Allah ki saka kowanne kaya, kinga yunwa nake ji ni…”

Riga da skirt ta dauka na atamfa, ta wuce tabar shi a zaune, sakawa tayi, ta fito da wata Abaya da Baba ya siya mata, baifi sau biyu ta saka ba, saboda tana bala’in ji da ita. Natsuwa tayi ta daura dankwalinta, ta feshe jikinta da turaruka masu saukin kamshi, shi kanshi Hamzan kallonta yake yi saboda yanda tayi mishi kyau, banda jan janbaki da eyeliner babu wata kwalliya a fuskarta. Saida ta samu leda ta zuba turarukan wuta da aka kawo mata, dana sakawa a cikin kaya, da ma wasu ta ajiye a gefe tukunna ta dora abaya din, tana daureta ta zauna mata das, mayafin ta dauka ta dora a saman kanta tana yafa shi ta baya. Bata wani dauki takalmi mai tsini ba, flat ta saka sai jaka data dauka fara, kalar takalmin.

“Muje?” Ta furta tana kallon Hamza da yake jin kamar su fasa fita, dan dai ya fadama Anna zasu zo, amman Hindun ta yi mishi kyau ba kadan ba.

“Kin yi kyau.”

Murmushi ta yi.

“Kaima haka…”

Ta furta, ya saka shadda, golden mai haske, sai daukar ido take yi, ga kamshin shadda mai tsada daya hadu dana turarukan shi, mikewa ya yi .

“Ina wayar ka?”

Ta bukata, hannu yasa a aljihu, haka kawai yasan hoto zata dauke su, cire wayar ya yi daga key yana matsawa kusa da ita ya daga camera din yana daukar su, sosai sukai hotuna wajen kala goma, dan wani ma saida ya sumbaci kuncinta tukunna suka dauka, dariya suke yi idan suka yi wani style din, kafin cikin Hamza ya yi kara.

“Ke yunwa fa nake ji, ki wuce mu tafi wallahi.”

Dariya tayi tana daukar ledar da yasa hannu ya karba suka fita tare, har mota shi ya bude mata, haka kawai sai take jinta da wani irin muhimmanci a wajen shi, bakomai dan har yanzun bai nadota a towel ba, tasan dabarar da zata yi hakan ya faru, bari dai ta samu ta kama zuciyar Anna. A nutse Hamza yake tukin shi har suka isa gidan, yayi parking yana fitowa. Kallon gidan Hindu take yi, yayi mata kyau matuka duk da baikai na Hamzan ba. Shi ya fara yin gaba suna shiga cikin gidan da sallama, sosai gabanta yake faduwa, kafin matar da tasha ganinta a hotuna, kuma bata gajiya da mamakin cewa itace mahafiyar Hamza ta amsa musu sallamar.

“Ann,” Hamza ya fadi yana karasawa da fara’a a muryar shi, dan rike mata kafadu ya yi yana sumbatar kuncinta.

“Ina kwana…”

Ya furta, Hindu na tsaye tana kallon su.

“Kai ba zaka ce ta zauna ba.”

Ann ta fadi cikin yaren shuwa, duk da Hausa Hamzan ya yi mata, tana mayar da hankalinta kan Hindu hadi dayin murmushi.

“Ina kwana.”

Hindu ta fadi, da alama tanajin Hausa, kafin ta amsa Hamza ya karaso inda Hindu take yana fadin.

“Ki zauna.”

Bata yi musu ba ta sami kujera ta zauna, dan kafafuwanta sun mata wani irin nauyi, kujerar da take fuskantar ta Hindu, Anna ta zauna.

“Nifa yunwa nake ji.”

Hamza yai maganar da harshen Anna din, duk suna saka Hindu jin wani iri.

“Karki damu da shi kinji ko, kin tashi lafiya?”

Sai dai kafin Hindu ta amsa, wata siririyar yarinya da Hindu taga hartafi Hamza kyau ta fito, jikinta sanye da doguwar riga irin ta mutanen saudiyya, kanta daure da jan dankwali ta rigata da.

“Inalillahi…..Ann tayi Hausa….”

Kusan a tare Hamza ma da yake tsaye baki a bude yace.

“Ann!”

Ko kallon su Anna bata yi ba, Hindu kuwa ta kasa daina murmushi, kafin yarinyar ta karaso ta zauna gefen Hindu.

“Matar Yayanmu.”

Kallonta Hindu ta yi.

“Yaaya kagama boye mana ita, yau gata har gida.”

Dariya Hamza ya yi.

“Daman kune da gajen hakuri ai.”

Gaisawa Hindu ta yi da Auta, data mike daga inda take zaune tana fadin, “Nikam ban karya ba.”

Hamza da sauri yace, “Wallahi nima.”

Wannan karin Anna ce ta mike. “Ku gama karyawa, ina zuwa.”

Dan taga Hindu a takure take, yarinyar tayi mata kyau, ta kuma burgeta matuka, sam batayi mata kama da irin tsagerun yaran zamanin nan ba. Tana bar musu wajen, Auta na kama hannun Hindu ta mikar da ita.

“Ki zo muje muci abinci.”

Ba shiri Hindu ta ajiye jakarta tana binsu, har wajen cin abincin, suka zauna. Da kanta yarinyar ta zuba ma Hindu plantain da soyayyen dankali, ta kuma hada mata Tea.

“Auta baki ganni bane halan.”

Hamza da harya gaji da jira ya fadi yana mika hannu ya dauki kofin shayin Hindu, Auta ta kuwa rike mishi hannu.

“Sake mun hannu.”

Kallon shi ta yi.

“Kabar mata nata dan Allah, zan hada maka yanzun.”

Da fulatanci tayi mishi maganar, saboda sam ba sabawa suka yi da yiwa juna Hausa ba. Ajiyewa ya yi kuwa, ta hada mishi nata, ita Hindu duk da yunwar da take ji a kunya ce take, sukam hira suke yi kamar bata wajen, da alama itace ta takura kanta. Auta ma nan tabar su, sai lokacin Hamza ya ce,

“Ke ba zaki ci abinci ba ko? Karki cemun kina jin yunwa Allah.”

Murmushi ta yi, da sauri-sauri take cin dankalin kafin su kara fitowa, sai dai harta gama babu wanda ya fito, falon suka koma suna zama ita da Hamza, da alama flashing ya yiwa Anna, sai gata ta fito.

“Tafiya fa zamuyi Anna.”

Hamza ya fadi, kallon su tayi

“Ayita hakuri kunji, Allah ya baku zaman lafiya.”

Hindu sunkuyar da kanta tayi, Hamza ne ya mike yana daukar ledar daya ajiye ya karasa ya mika ma Anna.

“Wai a baki Anna.”

Da murmushi tasa hannu ta dauki ledar.

“Ma shaa Allah, na gode sosai. Allah yasa albarka.”

Mikewa Hindu tayi.

“Mun gode Anna, Allah ya kara girma.”

Sannan sukayiwa Anna sallama, tace musu Appa ya fita, dan haka suka wuce kawai. Suna fita daga gidan Hindu na sauke wani numfashi da batasan tana rike da shi ba.

“Matsoraciya.”

Hamza ya fadi yana dariya.

“Nace miki Anna bata da matsala baki yarda ba.”

Murmushi tayi.

“Nagani aikam, na dauka kana da kyau sai da naga Auta.”

Dariya ya yi sosai wannan Karin.

“Faruk yafi kowa kyau, duk zaki gansu a hankali, mu biya mu siyi abinda zamuci da rana?”

Kai ta daga mishi

“Har dare ma, mu saka a fridge…”

Kai kuwa ya jinjina mata, suka biya Chicken Republic, sannan suka wuce gida.

*****

Sati biyun nan a jigace tayi su, ta dauka zaiyi mata kadan, yanda ta hasaso satika biyu babu inda zasu kaisu. Amman yanzun da kanta take neman hanyar da Hamza zai fita daga gidan ko na yini daya ne ko zata samu sauki.

“Ba yau zaka koma aiki ba?”

Ta bukata, ganin ya bude system din shi, kallonta ya yi ta kasan idanuwa.

“Kin gaji dani ne?”

Kai ta girgiza mishi a hankali, amman yasan karya take yi, a idanuwanta yake karantar hakan. Kuma dole ta koyi hakurin zama da shi tunda a yanzun ita kadai yake da ita, ganin ya yi shiru ya bata karfin gwiwar yi mishi tambayar da take ta cinta a rai

“Ba zamu je honeymoon din mu ba?”

Saida ya yi kamar baiji taba, tukunna ya dago idanuwa, kafin ya kwashe da wata irin dariya, ganin tana zaune dai tana kallon shi yasa shi fadin.

“Wai da gaske ki ke?”

Kallon shi dai take yi har lokacin, dan sam bata ga abin dariya a maganar da tayi ba

“Da gaske ki ke yi?” Ya furta yana tabbatar ma kanshi.

“Hindu anan ma harkin gaji dani, idan muka tafi wani waje wallahi ba zaki iya ba, kuma kin kusan komawa makaranta ma…”

Dan turo mishi labba tayi, da gaske ne ta kusan komawa makaranta, amman hakan baya nufin zai hana musu zuwa honeymoon dinsu in ya yi niyya, kasar wajen a kwana nawa ma za’a iya zuwa a dawo.

“Ni dai ba wani, a kwana nawa zamu bar kasar mu dawo.”

System din shi Hamza ya ture gefe, saboda har ranshi ta fara saka shi nishadi.

“In zamuje da wacce kasa zamu tafi to?”

Da sauri ta amsa da, “Paris.”

Jinjina kai ya yi. Sosai kasar take burgeta, akwai wata Hawwaty a Instagram, can taga sunje da mijinta, kalar hotunan da suka kashe a wajaje daban-daban sun bala’in burgeta.

“To yaushe ya kamata mu tafi, tunda kinga Monday zaku koma makaranta.”

Dan shiru Hindu tayi, ranta ya yi wani irin kal.

“Ko gobe da safe haka.”

Sosai Hamza yake kokarin danne dariyar shi, amman ganin da dukkan gaskiyarta yasa shi kwashewa da wata dariyar, system din ya dauka yana mikewa, Hindu ba zata kashe shi ba.

“Ko Abuja zamu je ai sai haka Hindu, kinsan samun visa kuwa? Kina magana kamar zamu je Barnawa…. Kibar ni aiki zanyi.” Hamza ya karasa yana dariya, kafin ya fice daga dakin

Sai dai a gabaki daya maganar da tayi bataga abin dariya ba. Yana magana kamar ba zai yiwu subar kasar a gobe ba, a littafi sau nawa ta karanta, rana daya za’a yanke tafiya kasar waje, sai dai a shirya a wuce airport, yanda wasu ma suka mayar da fita kasashen ketare kamar dakinsu, akwai littafin data karanta, gayen ciki duk juma’a a Madina yake sallar juma’a, duk da wannan suna da nasu private jet din, amman ai ba abin mamaki bane ba.

Kwanciya tayi tana daukar wayarta, gara ko hira su danyi da Dimples, Hamza ba zai gaji da disappointing dinta ba sam-sam.

<< Mijin Novel 22Mijin Novel 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.