Bayan Awa Goma
Ya sha kwana zaune, amman wannan ne awanni goma mafi tsayi a rayuwar shi, har Baba da yasan haushin shi yake ji sai da yai mishi magana ya zauna. Tunda duk a asibitin suka kwana, amman yaki, so yake kawai a fito musu da wani labari ko yayane, shi baima san mata suna dadewa haka basu haihu ba. Da ba a jam'i yai sallar asuba ba, tabbas da ba zaisan abinda yake karantawa ba. Ruwa ma Anna ce ta bashi ya samu ya kurba yana jika makoshin shi.
Tunda daddaren Anna da kanta ta. . .