Skip to content
Part 30 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Bayan Awa Goma

Ya sha kwana zaune, amman wannan ne awanni goma mafi tsayi a rayuwar shi, har Baba da yasan haushin shi yake ji sai da yai mishi magana ya zauna. Tunda duk a asibitin suka kwana, amman yaki, so yake kawai a fito musu da wani labari ko yayane, shi baima san mata suna dadewa haka basu haihu ba. Da ba a jam’i yai sallar asuba ba, tabbas da ba zaisan abinda yake karantawa ba. Ruwa ma Anna ce ta bashi ya samu ya kurba yana jika makoshin shi.

Tunda daddaren Anna da kanta ta koma gida cikin kayan babies din da aka siya ta tattaro duk wani abu da take tunanin za’a bukata ta dawo. Amman ba’a sanar da su ta haihu ba sai karfe bakwai na safe, duk wasu maganganu da ake fadi Hamza bayajin su, kalaman farko kunnuwan shi suka tsinta suka koma suna rufewa ruf.

“Ta samu ‘yan biyu duk mata…”

Ba dan baisan yara biyu bane ba, baima san kafafuwan shi sun gaji da tsayuwa ba sai da yaji suna rawa, babu shiri yabi bango yana samun waje ya zauna, numfashi yake fitarwa kamar wanda yayi gudu. Ranar da aka fada musu yara biyu ne ita kadai taje asibitin, tun a hanya take kiran shi in yana kusa su hadu a gida, ba zai manta yanda ta kama hannun shi ta dora cikinta ba.

“Yara biyu, yara biyu ne a cikina.”

Tun da ta samu cikin ranar ne karo na farko da yaji kaunar koma meye a ciki har bayan zuciyar shi, ranar ne yaji kamar yana bangare daya da wani abu mai matukar muhimmanci.

“Zamu basu mamaki…”

Ya furta da murmushi a fuskar shi.

“Sai kowa yazo da tunanin yaro daya zasu ga biyu.”

Kai take daga mishi, sai yanzun yake jin ashe ya adana sautin dariyarta a wani bangare na zuciyar shi. Ya adana abubuwa da yawa a tare da ita, abubuwan da yake kula da su yau da kullum, yanda take zagaya hannuwanta kan cikinshi ta dora fuskarta a bayan shi tana rungume shi duk idan tayi tunanin bai hakura da rigimar da sukayi ba, ko da shine da laifi.

“Fushi kake har yanzun? Ni na hakura kaine za kai mun fushi.”

Takan fadi, abubuwa da yawane suka dawo mishi, sosai yayi nisa cikin tunani, dan sai da yaji an taba mishi kafada tukunna ya daga kai yana kallon Anna.

“Zaka iya zuwa kagansu.”

Ta fadi farin ciki shimfide a fuskarta, ga yaran Ma shaa Allah, so take ta tafi gida yanzun, tunda hankalinta ya kwanta. Ta watsa ruwa, su sa suke tunanin yaro ko yarinya guda daya saiga biyu. Siyayyar kaya bata kare ba, harta gama tsara yanda jikokin nata zasu ga gatan da basu taba tunani ba. Kai ya daga ma Anna yana mikewa da kyar, dakin ne yake juya mishi, ji yake kamar yana yawo akan gajimare. Da kyar ya iya shiga dakin da Anna ta nuna mishi yanajin tana fadin,

“Hindun tana hutawa saboda ta sha wahala sosai, amman zaka iya ganin yaran su…”

Ko kai bai iya daga mata ba, ya tura hannun shi yana shiga cikin dakin. Karo yaci da wata Nurse daya dan daga ma kai, muryar shi dauke da wani yanayi yace,

“Ina yaran?”

Gaba tayi yana binta a baya, yanzun kam jin shi yake yana yawo akan gajimare, jin shi yake kamar a cikin mafarki. Bai sake jin yana wata duniya ta daban ba sai da Nurse din ta dauko yarinya daya tana sakawa a hannun shi, dokawa zuciyar shi takeyi kamar zata fito waje, ya kasa kallon fuskarta saboda yanda zuciyar shi take mishi rawa. Gyara yarinyar da yake ji tana hannun shi batare da yaji nauyinta ba yayi, yana dan gyara dayan hannun shi ana saka mishi dayar, bai iya kallon su ba sai da yaji fitar Nurse din daga dakin. Da wani irin bugun zuciya ya sauke idanuwan shi akan hannun shi na dama, bacci takeyi. Kiran sallah yayi mata cikin kunnanta, yana juyawa yayi ma dayar yarinyar ma. Kafin ya sake mayar da hankalin shi kan yarinyar da idanuwan ta suke a bude.

A duniyar shi kaf ya dauka bayan Anna ba zai sake dora idanuwan shi kan macen da zaiji kaunarta har cikin bargon shi ba, macen da zaiji yana so ya kare daga duk wani abu naqi da Allah ya saka a karkashin ikon shi. Sai ga mata biyu a hannun shi, mata biyu da in yana da iko ko sauro ba zai kusanto inda suke da sunan cutarwa ba. Mutane da yawa sun dauka hawaye shine karshen karayar zuciya, akan yaran da suke hannun shi idan idanuwan duka ake bukatar gani a kasa zai ciro su ya ajiye.

“Suhana…”

Ya furta daga wani lungu na zuciyar shi yana kallon yarinyar da idanuwanta suke a bude kamar tasan abinda yake faruwa. Fassarar sunan ta shine “Kyakkyawa”. Shine kuma suna na farko da yazo cikin kanshi daya kalleta, watakila dan jinin shi ce, dan ta fito daga wani bangare na jikin shi, ko da bata da kyau zuciyar shi ba zata taba yardar mishi da hakan ba. Dakyar ya iya dauke idanuwan shi daga kan Suhana yana kallon dayar yarinyar da take bacci. Akan ce jarirai basu da kama, amman yan biyun da akafi sani da identical a turance tun suna jarirai kamannin su iri dayane. Nashi yaran basu zo a wannan jinsin yan biyun ba, kowacce kamanninta daban yake.

Kallon yarinyar da yakeyi ne yasan labarin nutsuwa yake ji, kwanciyar hankali na daya daga cikin abubuwan daya manta yanda ake jinsu, sai yanzun, bai taba cin karo da wata halitta mai nutsuwar yarinyar da tayi kwance luf a hannun shi tana bacci ba, a duniya yara sunfi kowacce halitta yarda, ko idanuwanta bata bude ba, ballantana tasan waya dauketa, ta bashi dukkan yardarta tun kafin tagan shi

“Amna…”

Sunan ya kubce daga labban shi, sau daya suka taba maganar sunayen yara da Hindu, tace mishi tunda sun zabi barin sanin jinsin yaran har sai sun haifesu, sunayen ma su bari a haihun, ba zai wahala ba. Yasan yayi sonkai daya zabar musu sunaye batare da yaji ko tana da wani zabi nata ba.

“Daga yau, zuwa ranar karshe da nake da aron ta, ba zan taba yin abinda zai baku kunya ba, ba zakuyi dana sanin fitowa daga jikina ba”

Ya furta a cikin zuciyar shi yana kallon yaran. Kafafuwan shi ciwo suke, amman bayaso ya zauna ya tashi Amna, bayaso ko motsi mai karfi yayi

“Ke me yasa ba zakiyi bacci ba? Ko yunwa kike ji?”

Yake maganar yana kallon Suhana da yasan karonta ne na farko da taji yaren fulatanci. Dariya yayi me sauti yana sake kallon su. Wani dan labule ne tsakanin inda yake tsaye da gadon da Hindu take a kwance, karasa takawa yayi yana shiga wajen, baisan ko idanuwanta biyu ba ko kuma takun tafiyar shine ya tashe ta, sai lokacin yayi dabara yana zama kan kujera.

“Hey…”

Ya furta yana kallonta, amman idanuwanta ba a kanshi yake ba, yana kan yaran da yake hannun shi. Ta gansu, ta karbe su, dan an saka mata su a hannuwanta tun da sauran jini a jikin su, ta rike abubuwa da yawa masu daraja da hannuwan, amman sune na farko da taji har cikin tsokar jikinta. Bata kara fahimtar kaunar da take tsakaninta da Baba ba saida ta rungume su a kirjinta, sai take hasaso kalar kusancinta da Anty. Tana kara wata daraja ta daban a idanuwanta, tana da tabbacin wannan matakine da mata suke takawa a rayuwar su duk ranar da suka rike nasu yaran a hannuwan su.

Ranar zaka kara sanin darajata ta uwa, ranar da zaka fahimci dalilin da yasa take dora duk wani farin ciki naka a saman nata, yanda rayuwarta kacokan take tsayawa saboda taka ta cigaba. Kamar mahaifiya a duniya da zagayenta babu, duk yanda kake tunanin ka fahimci muhimmancinta ba zaka gane ba sai ranar da bayanka yai amsawar farko da ciwon nakuda.

“Na kasa yarda suna hannuna, yaranmu Hindu, muna da yara.”

Kai ta iya daga mishi saboda idanuwanta da taji sun cika taf da hawaye, dayan hannunta da babu karin ruwa, duk da akwai plaster a jiki ta dan mika mishi, tana saka shi yin dabara ya mike ya taka har bakin gadon, sosai ya rankwafa yana mika mata yarinyar da take bacci har lokacin, tana nade tsaf cikin farin towel yanda ko kayan jikinta baka iya gani.

“Amna”

Ya furta bayan ta karbi yarinyar, hakan yasa Hindu ware mishi idanuwa cike da son karin bayani,

“Peace…”

Ya fadi ma’anar sunan da harshen Turanci, dan ya tsaya a tsakanin nutsuwa da kwanciyar hankali, ya rasa asalin ma’anar da yaren Hausar da har yanzun mutane da yawa suke rainata a bakin shi. Har a ranshi ma baiyi niyyar musu magana da wannan yaren ba, Idan Amna taji zatayi kishin yanda ya yanke hukunci yi musu Fulatanci. Idan suna da rabon jin nata yaren duk in suna tare da ita zasu tsinta. A bakin shi kuwa da yaren Appa zasu tashi, da jinin Fulanin da yake ji har a kasan zuciyar shi.

Rike yarinyar Hindu tayi tana lumshe idanuwanta, kaunarta na ratsa duk wani lungu da sako na ruhinta. Kujerar Hamza ya janyo sosai yana zama. Hannunta da yagani a kumbure ya mika nashi ya kama, tana janyewa da sauri kamar wanda yake shirin goga mata wani abin, a cikin idanuwanta yake fara ganin abinda yasa zuciyar shi mummunar bugawa, kafin kwakwalwar shi ta fara fahimtar da shi kuskure na biyu mafi girma da yayi bayan na korar ta, shine kin furta kalaman ya dawo da ita kafin ta haihu, ganin ya fahimci hannunta da ta janye yasa ta jinjina mishi kai tana tabbatar mishi da gaske ita ba halalin shi bace yanzun.

“Zan ma Appa magana, sai a sake daura mana aure, muna da igiya daya a tsakanin mu…”

Yake fadi cikin tsantsar tashin hankali, musamman da tun da ya bude bakin shi take girgiza mishi kai, hawaye da yake cikin idanuwanta yana zubowa.

“Auren mu ya rigada ya kare…”

Wannan karin shine yake girgiza mata kai, idan kukan take so yayi shima zaiyi, zaiyi komai dan karta rabashi da kanta.

“Ya kare Hamza… Ya kare…”

Kan dai yake girgiza mata.

“Ki kalle su, karki raba musu iyaye daga zuwansu.”

Ko tana da hannun share hawayenta ma ba zatayi ba, tunda basu daina zubowa ba, nakuda takeyi da tabbacin ba zata taba komawa auren Hamza ba, Allah ta roka ya bata shi, tana nakuda take rokon ya musanya mata da mafi alkhairi idan har Ya kadarta mata sake wani zaman auren, zatayi, zata sake daga farko batare da maimaita kuskuren da tayi a baya ba. Yara da yawa sun tashi batare da iyaye ba, wasu ma mutuwa ce gabaki daya ta rabasu. Tun kafin ta haihu take fadin yanda yara ba zasu taba zama dalilin da zata zauna a auren da batayi niyya ba.

Har Mama ca tayi bata da hankaline da taji hirar, bata dandana zafin nakuda ba. Yanzun ba nakuda ba, ga yarinyarta nan a hannunta, ga dayar nan a hannun Babanta, amman ba zata taba koma mishi ba.

“Na miki alkawari na saba, nasani, zan canza saboda su, karkiyi tunanin zan kalli yarana inyi musu karya, wallahi zan canza Hindu, karki rabani da ke, kiyimun kowanne hukunci banda wannan…”

Kai ta sake girgiza mishi tana saka shi jin wani abu ya bude a zuciyar shi. Mikewa yayi, yana mika mata Suhana da tayi bacci a jikin shi yana juyawa. Idan abinda yakeji kuka ne zai balle da shi ba zaiyi a gaban yaran shi ba, ba zasu fara ganin raunin shi kafin suyi girman fahimtar karfin zuciyar shi ba. Ko daya kama hannun kofar ya bude yana fita, janta yayi a hankali, batare daya kalli inda yake tunanin su Appa suna tsaye ba ya taka yana nufar hanyar da zata fitar da shi daga asibitin. Ko babur ne zai hau zuwa gida, idan yaje ya nemi kudin da zai bashi, sam baima ji Abid da yake kwala mishi kira ba sai da yasha gaban shi.

“Abid ka kaini gidan Fodio.”

Ya furta, Abid din na daga mishi kai, suka karasa wajen motar shi, ya bude ya shiga ya zauna yana jan murfin. Har Abid ya zagaya ya shiga baima sani ba, dan ya nutsu yana jin yanda ba tsaga daya zuciyar shi takeyi ba, wajaje ne daban-daban yake budewa yana sanar dashi ba iya kirjin shi ciwon zai tsaya ba.

*****

Babu kowa a gidan sai Fodio, yana zaune kan kujera a falo da Mug a hannun shi da Hamza baisan ko meye a ciki ba. Sallamar Hamzan ya amsa da wani irin sanyi murya. Shima baice mishi komai ba ya wuce daya daga cikin dakunan baccin gidan zuwa bandaki. Wanka ya fara yi yanajin kamar an sake mishi fatar jikin shi saboda iskar da yake ji tana shigar shi ta ko ina. Sai da ya fito ne ya kula da dakin Fodio ne, cikin kayan shi ya sami riga da wando, yasan su duka basa rabuwa da sabon kayan ciki ko dan abokai baki, ko bukatar hakan ta taso a tsakanin su.

Har turare ya samu ya dan fesa, sai da ya dafe kirjin shi saboda ciwon da yaji yana mishi. Sannan ya samu ya fito yana dawowa falon. Waje ya samu ya zauna. Sai yanzun ya kalli Fodio da idanuwan shi sukayi zuru-zuru, abinka da mai hasken fata, kamar jini ne kwance kasan idanuwan shi da yake nuna alamar rashin wadataccen bacci, duk abinda Hamza yake ji bai hana shi fadin,

“Fodio lafiyar ka kuwa? Kaga yanda ka rame?”

Kallon shi Fodio yayi.

“Me kayi?”

Ya tambaya a madadin amsa tambayar da yayi mishi.

“AbdulHafiz bai fada mana ba, yace ba hurumin shi bane ba, in kana so muji zaka fada mana da kanka. Me kayi Hamza?”

Numfashi Hamza yaja yana gyara zaman shi cikin kujerar, da wani irin yanayi a fuskar shi yace,

“Kuskure, Fodio kuskure nayi”

Dan daga mishi kafadu Fodio yayi.

“Rayuwar mu cike take da tarin kuskure Hamza”

Da sauri Hamzan ya kalle shi

“Ba za kai mun fada ba?”

Kai Fodio ya girgiza mishi

“Zan maimaita maka abinda kasani ne, kayi kuskure, baka kyauta ba…duk kasan wannan Hamza.”

Fuskar shi Hamza ya saka a cikin hannuwan shi yana jin duniyar tayi mishi tsaye waje daya.

“Kana da sa’a daya, in dai zaka tsarkake zuciyar ka, idan zaka roki Allah da dukkan zuciyar ka zai yafe maka.”

Bude fuskar shi Hamza yayi, Fodio na jinjina mishi kai.

“Haka AbdulHafiz yace mun, tunda raina bai zo wuyana kafin in gane kuskuren da nayi ba ina da sauran rabo. Kasan AbdulHafiz, ya jamun ayoyi da Hadisai yana kara kashe mun zuciya.”

Murmushi Hamza yayi mai sauti, badan ya samu saukin abinda yake ji ba, sai dan AbdulHafiz ne, kaunar shi a wajen su mai girma ce, shisa yake jin abinda AbdulHafiz din yayi mishi har kasan zuci, shi kan shi Fodio din da murmushin a fuskar shi.

“Hindu ta haihu.”

Hamza ya furta muryar shi can kasan makoshi, wannan karin murmushin da Fodio yayi har cikin idanuwan shi ya kai.

“Kace mun ba wasa kake mun ba.”

Hamzan kan shi baisan murmushi ya kwace mishi ba, murmushi tun daga zuciyar shi

“Amna da Suhana…”

Yatsun shi biyu Fodio ya daga ma Hamza da ya jinjina mishi kai yana murmushi.

“Congratulations Man… Allah ya raya mana su.”

Abinda bai taba faruwa da Hamza ba yaji yanzun, yanayi ne daya dauka bakowa Allah yake halitta da shi ba, kunya, kunyar ma ta Fodio.

“Amin”

Ya amsa da wani yanayi da yasa Fodio kwashewa da dariya, har ran shi ya dauka zai jima wani abu bai saka shi nishadi ba, amman daya daga cikin kyautar da Allah yayi wa dan Adam ita ce mantuwa.

“Kunya ta kake ji yau?”

Hararar shi Hamza yayi, zai magana kenan wayar Fodio da ta hau ruri ta hana shi. Dagawa Fodio din yayi, kwata-kwata Hamza bai gane kan maganar ba tunda bayajin me ake fada daga dayan bangaren

“Dan Allah daga nan zuwa gobe ku nemomun duk kauyukan da akace suna cikin wahalar neman ruwa, ko guda nawa aka samu kuyi mun magana ina jira.”

Shine ma dan abinda ya fahimta a maganganun Fodio, kafin ya sauke wayar daga kunnen shi. Ganin yanda Hamza yake kallon shi yasa yanayin daya gani cikin idanuwan shi tun zaman shi ya dawo, kamar maganar da yake shirin yi na da ciwo tun kafin ya fito da ita.

“Ina son gina iya rijiyoyin da nake da hali a madadin Ashir…banda wani abu da zan mishi, Hamza ban da shi.”

Fodio ya karasa maganar muryar shi na karyewa, cikin idanuwa Hamza ya kalle shi.

“Idan ka gina rijiya ko da daya a madadin Ashir, ina da tabbacin da zai dawo duniya ko na rana daya zai nemoka, zai fada maka yanda kake daya daga cikin masu kaunar shi da bai tabbatar ba sai da ya rasu.”

Kai Fodio yake girgiza ma Hamza, yanajin idanuwan shi na cikowa da hawaye.

“A wajen na bar shi, a wajen, Hamza ko gawar shi ban tsaya an dauke ba, wacce irin kauna ce wannan?”

Numfashi Hamza ya sauke, shima yana bukatar lallashin nan, ba Fodio bane kawai cikin yanayi.

“Ban sani ba…ban sani ba Fodio…”

Cewar Hamza a gajiye, yana dorawa da,

“Kawai nasan ina fatan in rigaka mutuwa, abinda ban tabayi ba, saboda ina so in samu abinda Ashir yake shirin samu yanzun… Zunubaina masu yawa ne.”

Shiru ya biyo bayan maganar Hamzan, ba dan basu da sauran abin fadi ba, sai dan su duka kowa da tunanin da yakeyi, wayar Fodio din ce ta sake yin ruri, wannan karin daya duba mikawa Hamza yayi ganin Mansy ce, ajiyar zuciya ya sauke yana karbar wayar hadi da daga kiran ya kara a kunnen shi.

“Hello…”

Ya furta, jin muryar shi na sa Mansy fadin,

“Alhamdulillah, ina kaje? Inata kiran wayarka a kashe, na maka text yafi a kirga baka karanta ba ma, lafiya dai ko?”

Numfashi Hamza yaja yana fitarwa a hankali.

“Lafiya kalau…”

Yana jin itama ta sauke numfashi.

“Motar ka zan kawo maka daman, ina kofar gidan Fodio, ko ina zan kai maka?”

Mikewa Hamza ya yi.

“Ki shigo ciki.”

Jin ta danyi shiru yasa shi sake fadin.

“Ni nace ki shigo…”

Sannan ya kashe wayar yana mikawa Fodio daya karba ya ajiye a gefe shima yana mikewa, kitchen ya nufa dan ya ajiye mug din da yake hannun shi. Hamza kuma ya fita daga gidan. Mansy harta shigo da motar ciki, ta bude ta fito. Ganin shi yasa ta karasowa tana samun shi. Sai dai yanayin fuskar shi ya tsorata ta, sosai yanayin fuskar shi yasa zuciyarta dokawa, hannu ya mika mata tana saka mishi mukullin a ciki

“Yau ne rana ta karshe da wani abu zai hadamu Mansy, zaki tafi, zaki goge lambata, zaki gogeni a duk wani shafi na sada zumunta da kike dani, kamar yanda zanyi dana dauki wayar ta…”

Cikin bayanannen tashin hankali da firgici take kallon Hamza.

“Ina da yara Mansy, ina da yara har guda biyu yau da safen nan. Ba zan koma baya in goge rayuwar da nayi ba, bama ni da tabbacin laifukana ba zai taba su ba…”

Hamza yake fadi wani irin tsoro na shigar shi.

“Me kake ce mun? Ta ina kake so in fara? Ni bance zaka aureni ba tuntuni, ka fadamun da bakinka ba zaka aureni ba. Bance kai ka fara bata ni ba, amman kana da hannu a ciki…”

Mansy tayi maganar hawayenta na zuba, itama tsoron ne bayyane a fuskarta, firgicin inda zata fara daga nan, badan Hamzan ne kawai namijin da ta taba bi ba, ba kuma dan shi kadai ne take tare da shi ba. Duk da ya sha fada mata yanda ba zai taba aurenta ba, ta kuma dauka har zuciyarta ta yarda da hakan, sai yanzun, sai yanzun da yake tabbatar mata rabuwa da shi take jin akwai bangaren zuciyar ta da yake ganin kamar Hamza zai kasance a rayuwar ta har karshe.

“Ina da laifuka da yawa na yarda, amman ba zan bari ki doramun na bacinki ba Mansy, ba zaki karamun da wannan ba, babu abinda ya faru a tsakanin mu da babu amincewar ki, zamu raba laifin ne dai-dai…”

Hamza ya fadi yana dorawa da,

“Wa’azi ya kamata in miki, amman banda wannan kalaman, laifukana ba zasu barni ba. Karki sake nemana, idan har akwai wani bangare na zuciyar ki da ya taba mutunta abotar mu zaki bar rayuwata.”

Hannu tasa tana goge fuskarta.

“Na gode, n agode da komai.”

Ta karasa muryarta a karye tana juyawa, shine namiji na farko a rayuwar ta da ya taba kokarin kareta batare da alhakin hakan ya rataya a wuyan shi ba, namiji kwara daya da tasan zata kira a kowanne lokaci ya taimaka mata idan bukatar hakan ta taso, namiji na farko da ta jingina kanta da shi batare daya tureta ba. Ko bata ba Hamza jikinta ba a idanuwanta taga yanda zai taimaka mata idan da ta roke shi. Shisa yanzun rabuwa da shi yake jijjiga rayuwarta. Sai dai da gaske akwai bangaren daya wuce zuciyar ta da zai cigaba da mutunta abokantar su har karshen rayuwarta. Zata bar shi, zata bar shi kamar yanda ya roke ta, duk da ba ta san inda rayuwa zata kaita daga nan din ba, zata bar shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.9 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mijin Novel 29Mijin Novel 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×