Skip to content
Part 31 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Ba kirga kwanaki yakeyi ba yanzun, saboda wani irin tsayi da suke mishi wajen wucewa. Rayuwar ma gabaki daya bayajin dadinta, saboda cikin watanni ukun nan ta kowacce fuska rayuwar ta hade mishi waje daya. Su Anna basuce suna fushi da shi kai tsaye ba, amman bayan gaisuwa babu wata magana mai tsayi da take hada su, bai samu fuska har a wajen Appa da zai roki su sake zuwar mishi wajen Hindu ba. Hatta AbdulHafiz har yanzun bai huce da shi ba, ko yayi kokarin fada mishi damuwar shi baya saurare, satin daya wuce ma kai tsaye AbdulHafiz din yace,

“Ka daina wahalar da mu biyun Hamza, kaga abotar nan mun gwada a baya batayi wani amfani ba, tunda ko shawara ce na baka banda kimar da zaka dauka…shisa na daina maka shishshigi a lamurranka, kai dai muci gaba da maganar aiki ana gaisuwar mutunci zaifi.”

Shisa ya kyale su, ya barma Allah lamurran shi. AbdulHafiz ne yake sa ran zaije ya taya shi bama su Anna hakuri daman, shima kuma ta bangaren shi babu wani sauki. Gidan Fodio din ma da yakan kwana yabari, tunda in dai ba yana falo zasu fita shi da Arafat ba sai dai ya fito yaga basa nan. Ko abinci suka siyo basa tahowa da shi.

“Mantawa nake ka saki Hindu… Sai ina dauka kana da aure har yanzun zaka koma gida kaci abinci.”

Arafat yace mishi ranar karshe da yai magana sunyo take away basu taho da shi ba. Abin yayi mishi ciwo ba kadan ba, a fuskar shi suke sake goga mishi laifin da ya riga daya karbi yayi, kuma gani yake duk AbdulHafiz ne ya zuga su suke mishi wannan abubuwan. Wai a ciki harda Abdallah ma, jiya da yazo wajen aiki a makare yake tsokanar shi magana ya dankata mishi

“Ba zaka gane dalili ba, wanda ya rike auren shi da kyau ne kawai zaifi fahimtar dalilin makarrata.”

Komai ya hade mishi waje daya, babu wanda yake kokarin fahimtar shi, kafar sada zumunta ta WhatsApp kawai yakan hau, shima idan ya roki Hindu yana son ganin yaran shi da zai rantse duk ganin da zai musu a kullum kara girma sukeyi, sai ta turo mishi hotunan su, duk maganar da zaiyi bayan hoton ba zata taba amsa shi ba. Ko kiranta yayi maganar su bata wuce ta wasu dakika, da yaji lafiyar su Suhana take kashewa, har mamaki yake. Hindu da aiki idan ya fita a tsayin rana bai kirata ba sai tayi mita.

“Idan baka so kaji muryata, ni ai ina so inji taka.”

Amman yanzun kamar bataso ma take amsa wayar shi, text baisan adadin wanda ya tura mata naban hakuri ba, bayajin ya taba bada hakuri a rayuwar shi mai yawan wanda ya ba Hindu, amsa daya ya samu a tsayin watannin nan.

“Na fada maka komai ya wuce, wallahi komai ya wuce har raina.”

Amman kuma taki amsa tayin auren shi da yake sake yi mata. Idan gidansu yaje dan yaga yaran shi, Asma take bama su ta kawo mishi, harya gama zaman da zaiyi ba zata taba fitowa ba. Idan ma daukar su yayi ya kaiwa Anna, harya dawo dasu sai dai tasa aje a amso su. Ita kanta Anna yafi ganin fara’arta yanzun duk idan ya kai mata su Amna. Yau ma yana zaune a Office shi kadai, daga inda yake yana jin hayaniyar hirar su Fodio, zuciyar shi ciwo takeyi, duk yayi zuru-zuru ya fita hayyacin shi.

Wayar shi da take ajiye akan tebir ta fara ruri, jikin shi har kyarma yake wajen dauka da yaga Hindu ce,

“Hello”

Ya furta kafin ta amsa yana dorawa da,

“Ya kuke?”

Yanajin kukan da baisan na waye ba.

“Amna ce take kuka ko Suhana?”

A gajiye Hindu tace,

“Waka sani rigimammiya?”

Murmushi yayi.

“Suhana…”

Dan jim Hindu tayi.

“Mama da Anty zasu fita yau ana wani suna haka. Ni yanzun ina makaranta, ina da test amman bansan ya zanyi ba.”

Hindu take fada mishi, baima san ta koma makaranta ba, sam bata bashi labarin komai daya shafi rayuwarta yanzun. Motarta ya jima da kai mata abinta harda takardun, kuma yana jin dadi duk in yaje gidan yaga motar, bayan su Suhana yanzun bashi da wani abu nashi da yake tare da ita sai dai motar. Yana tura mata kudi saboda su, duk da kullum cikin siyayyar duk wani kaya da zasu burge shi yakeyi. Ya gwada sai mata sau daya tai wani irin warware shi, bai kara gwadawa ba. Yanzun tsoronta ma yake ji, tsoron yai wani abu da zai sake tunzutata taki hakura ta dawo mishi yakeyi sosai.

“Karki damu, bari inzo in dauke su.”

Yanajin numfashin da ta sauke.

“Nagode…”

Kafin ta kashe wayar, mikewa yayi yana fita da sauri, kan shi tsaye ya nufi mota ya bude yana nufar hanyar da zata hada shi da makarantar su Hindun.

*****

A bakin ajinsu ya hangota, takawa yake yana son tabbatar da abinda idanuwan shi suke hango mishi tun daga nesa. Rabon daya saka ta a idanuwan shi tun a asibiti. Watanni ukku cir bai ganta ba, tayi wani irin kyau, tayi jiki. Sai yake ganin kamar ya shekara ukune bai ganta ba, gashi tayi mishi wani irin kwarjini, banda jan jambaki babu wata kwalliya a fuskarta, sosai tayi mishi kyau cikin shigar abayarta kamar ko da yaushe. Sai wani da yake tunanin cikin yan ajin su na yanzun ne yana rike da Amna, ita kuma ta rike Suhana da take jijjigawa a hankali.

Ko da ake ce mata raino abune mai wahala bata tabbatar ba sai da yazo kanta, raino harna yara biyu. Danma kowa a gidan yana tayata hidimar su, shisa take samun sauki, Suhana ce take da wata irin rigima, gashi inta fara kuka kome zakai ba zatayi shiru ba sai tayi niyyar hakan da kanta. Amna kuwa in ba yunwa take ji ba ko batajin dadin jikinta da wahalar gaske kaji kukanta. Amman Suhana ko wanka za’ayi har makota sai sun sani. Hannu Hamza ya mika yana karbar Suhana ya sabata a kafadar shi yana jijjigata, magana yake mata a hankali cikin harshen fulatanci yana shafa bayanta, kamar haka take jira kukan ta ya fara rissina.

Cikin mintina kasa da biyar hartayi shiru, da alama bacci take shirin yi ma, kallon su Hindu takeyi, tana kallon yanda Hamza yakeyi da Suhana kamar raino na daya daga cikin abinda aka haife shi da iyawa. Suit ne a jikin shi mai guda uku, bai saka ta saman ba, daga ta cikin mai dogon hannu sai kuma yar jacket din saman. Dan murmushi tayi, da gaske takeyi ranar da tace mishi komai ya wuce mata, saboda a sujjada ta dinga zubar da hawayenta tana rokon Allah daya yaye mata dukkan damuwa.

Yanzun kam hamdala kawai takeyi saboda yanda komai ya nutsar mata, ita ce yau take kallon Hamza, gashi a gabanta amman kyawun shi bai mata wani abu ba, asalima salaf take jin zuciyarta a kan shi. Sai takejin kamar ba kalar kaunar da ake fadi taiwa Hamza ba, kamar dai-daito da yayi da kalar mijin burinta ne abinda ta so a tattare dashi ba komai ba, yanzun kuma da ya bude mata idanuwanta sai take kallon shi a shi kadai, take kallon shi babu tarin dukiyar nan, babu izza da kyawun shi. Hamza take kallo, Hamza da yai wasan cikar shekara da auren su, Hamza daya shigo mata a buge a darenta na farko.

Hamza take kallo daya sa kirjinta daukar zafi kamar ana hura wuta a cikin shi, sosai yanzun idanuwanta suke a bude tana ganin Hamza da yasa ta kuka kamar ba zata daina ba. Sai takejin kamar ba watanni uku bane da rabuwar su saboda inda take hango shi da matukar nisa a rayuwarta. Shi din bakomai bane a wajenta yanzun sai Baban su Suhana, ko dazun da zata fito da Mama take mata maganar yanda zatayi da su Suhana, ko za’a dauko mata yar aikine da zasu dinga zuwa makaranta da ita tana tayata raino idan basa nan, kai ta girgiza ma Anty.

“Zan kira Baban su yazo ya karbe su, shima ya dana yaji.”

Ko abu ya kawo sai take tsintar kanta da fadin.

“Baban su Suhana ne ya kawo.”

Ya tashi daga Hamza a idanuwanta, saboda idan ta kira shi da hakan zai zamana akwai wani kusanci a tsakanin su da yake ita da shi kadai, amman idan tace Baban su Suhana, kusancin zai biyo ta kan yaran ne tukunna ya hadata dashi. Hakan kuma yayi mata har a zuciyarta. Bata bukatar wata mai raino, courses biyune ta ajiye daman ko da ta dawo makaranta, saboda tana tsoron ga ciki, kamar ba zata iya ba. Tunda project dinma a lokacin kaf zanen Hamza ne yayi mata su, har aka kusan kamata wajen kare kanta, danma yasa tayi rubutun da kanta, kuma yayi mata bayani da yawa a kai, da bata haye ba, tsaf za’a gane ba ita tayi ba.

“Muje sai in baka kayan su, suna mota”

Ta furta tana mika hannunta ta karbi Amna.

“Na gode Faruk.”

Ta furta tana yin gaba, Hamza ya bita a baya, har kasan zuciyar shi yake jin yanda ko arzikin gaisuwa bai samu ba wajen Hindu. Suna zuwa mota ta dauko jakar kayayyakin da tasan duk zasu bukata, har madarar su da sai sunga haza suke sha ta hada musu. Tasan yana da kujerun su a duka motocin shi, na tata motar ma shiya siyo ya kawo. Ta dai raka shi har mota ne ya zaunar da su.

“Idan Suhana tayi fitsari baka canza mata pampers ba kuka zatayi, bata son jin lema a jikinta ko kadan.”

Kai ya jinjina mata, yana kallon fuskarta, kewarta na danne shi, yanda take mishi bayani zakai tunanin ba zata sake ganin su Suhana bane ba, murmushi yakeyi.

“Hindu…”

Ya kira a hankali.

“Amna bataso a kwantar da ita akan bayanta, zata farka…”

Gyara tsayuwar shi yayi.

“Hindu…”

Ya sake kira, sai lokacin ta kalle shi.

“I got this, I got them… Na ‘yan awanni ne, ki yarda dani, zan iya.”

Kai ta jinjina mishi, yanayin fuskarta yana nuna mishi ko kadan bata yarda zai iya kula da su ba, kuma haka dinne, duk da tun suna jarirai suna awa har biyu tare da shi, wani lokacin fiye da haka. Kewar yaranta takeyi tun kafin subar wajen, ko a gida wani ya karbe su, alkunya kawai take, dan ji takeyi inba ita ba babu wanda yake fahimtar abinda suke so, babu wanda zai kula dasu kamar yanda ita din zata kula da su.

“Dana fito zan kira ka, in suna kuka ka kirani dan Allah, kaji.”

Kai ya daga mata.

“Ayi test lafiya. Allah ya bada sa’a.”

Kallon shi takeyi kamar zai tafi da wani bangare na zuciyarta. Harya shiga mota yana kallon tana kokarin leka su Suhana duk da tinted ne gabaki daya gilasan shi. Kai kawai ya girgiza yana dariya, da har yanzun tana karkashin ikon shi, da test din yau an hakura da shi, zai jata su shiga mota su tafi gida, saboda yasan da wahala ta sami nutsuwa harta iya rubuta wani abin kirki. Yana hanya ne yaga kiran Fodio, bai daga ba sai da ya sauka daga titi yai parking, ba zai amsa waya yana tuqi da su Suhana a motar ba

“Ina kaje?”

Fodio ya tambaya.

“Hindu na da test a makaranta, shine naje na karbo su Suhana…”

Baima karasa maganar ba Fodio ya katse shi da fadin.

“Ka zo dasu gidana dan Allah, mu ma can zamu tafi yanzun.”

Numfashi Hamza ya sauke yana daga girar shi.

“Me yasa? Ni gida zan wuce.”

Shi suke shama kamshi, duk da yasan su duka suna zuwa ganin yaran, lokutta da dama sai sun dawo su fada mishi, ko Hindu ta dauki hotin abinda suka kai mata ta tura mishi ma yake sanin sunje din. Rayuwa ta hada shi da abokan da mutane da yawa suke addu’ar samu.

“Bana so inyi zagi saboda kana tare da su Suhana, dan Allah ka kawo mana su, kaji.”

Dariya kawai Hamza yayi yana kashe wayar. Gidan Fodio din ya nufa kan shi tsaye, sun ma riga shi karasawa, saboda sunfi shi kusa da gidan daga Office, tunda yai parking, yana budewa ya fito yaga Fodio harya bude murfin motar yana rankwafawa ya kwance Amna daga cikin kujerarta ya dauketa, sai yaga kamar ta kara kiba, kumatunta kawai na saka dariya kwace mishi, tafi Suhana haske, yanda yaran suke kama da Hindu suna kuma kama da Hamza batare da sunyi kama da junan su ba yana matukar bashi mamaki.

Hamza kuwa Suhana ya dauka, yana juyawa AbdulHafiz na miko hannu ya karbeta, da Nabila batayi bari ba da yanzun yana rike da nashi shima, amman haka Allah ya tsara, komai na da lokaci. Su Amna dinma jin su yake kamar daga jikin shi suka fito. Wani abu Suhana tayi da baki.

“Allah karkiyi mun rashin kirki Suhana, ke kullum sai munyi fada ne?”

AbdulHafiz ya karasa yana dangwale mata hanci, sake kwabe fuska tayi.

“Ko kinyi kuka ba ajiye ki zanyi ba…”

Yai maganar yana gyara mata zama a kafadar shi, tare suka shiga gidan su duka. Kan su bai dauki caji ba sai da yaran biyu suka kaure da kuka. Su hudun sun rasa yanda zasuyi da su, musamman Suhana da ko fida taki kamawa. Hakan yasa Hamza fadin

“Ko Pampers take so a sake mata.”

Wani tsalle Fodio yayi yana komawa gefe.

“Ku cireni a lissafin nan.”

Ya fadi, yana son su Amna, amman ba zai taba kashin yara ba. Shi a nashi tsarin rayuwar ma sam bai hango yara ba har yanzun, aure ne abinda ya fara sakawa a ciki yanzun, shima ya kasa furtawa a fili wani yaji saboda tsoron da yake ji, amman ya san yana bukatar mace ko dan karya komawa neman su ta hanyar da bai kamata ba. Amman yara kuwa yana da sauran tafiya a gaba kafin ya fara hasaso rayuwa da su.

“Bari kuga Husband material, yadi goma, riga harda yar ciki.”

Arafat ya fadi yana fara kokarin cirewa Suhana skirt din da yake jikinta. Su duka tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah, batama bata pampers din ba, rigima ce kawai da take ji, yana sabata a kafada kafin a miko mishi wani pampers din tana tsula mishi fitsari

“Inalillahi… Suhana kinsan wanne kayane kikai wa fitsari? Kinsan dubu nawa kika fitsare?”

Ya fadi kamar zai fashe da kuka, dole Hamza ya karbeta suna mishi dariya. Sai da suka samu duka yaran biyu sukai bacci tukunna Hindu ta kira shi.

“Na fito yanzun.”

Kai yake girgiza mata.

“Wallahi ba yanzun zan dawo dasu ba, kinsan wahalar da muka sha kafin suyi bacci…”

Yana jin tayi jim kafin ta kashe wayar, shima pillow ya dauka daga kan gadon yana kwanciya kasa, gefen katifun su Suhana da suke kwance a kai suna baccin su, kamar basu da wata damuwa a duniya. Idanuwa ya kafa musu yana kallon su har shima baccin ya dauke shi.

*****

Links din hannuwan rigar shi ya dauko yana ajiye su akan gado, sannan ya dauki daya ya saka a hannun, yana daukar dayan ma. Cikin wani lokaci ya fito tsaf, cikin yadin shi ruwan madara. Da wahalar gaske ka kalle shi baka kara kallon shi ba. Kallo daya zakayi wa fuskar shi kaga kwanciyar hankalin da take shimfide, zuwa yanzun bayajin shi cikin kuncin da baisan dalilin shi ba, bayajin kirjin shi kamar an danne. Bai dauka zai iya shekara daya batare da mace ba. Azumin shi yake duk Alhamis da litinin yana rokon Allah daya kare mishi zuciyar shi. Da kan shi ya goge Twitter da Instagram. Baice zai daina gabaki daya ba, amman sai ya yadda da fin karfin zuciyar shi da yayi

Sau biyu yana kusan komawa ruwa sanadin Instagram, na biyun hotunan su Suhana da Hindu ta turo mishine ya taimake shi, hotunan yagani yasa shi goge manhajojin biyu gabaki daya. Temptation bala’i ne, idan kana fama da kanka abu kalilan, abinda kake ganin bai kai ya kawo ba zai dawo maka da komai baya. Shisa ya goge, babu yarinyar da zata saka shi karya alkawarin daya daukar ma Ubangijin shi, alkawarin tuba sahihi, tuban da yake fatan ba zai koma ruwa ba, bazai karya alkawarin da yayiwa su Suhana na ganin basuyi dana sani kona rana daya daya kasance sun fito daga jikin shi ba.

A hankali kwanaki suka tafiyar mishi suna juyewa watannin da suka cike shekara, a cikin wannan lokacin yaga kokarin da yayi ya samar mishi yafiyar su Anna, a cikin lokacin ne ya ajiye duk wata izza da yake ji ya roki AbdulHafiz ya yafe mishi dan yagaji da yanda yake mishi kamar bare, kamar basu da wata alaka data wuce aiki. Shekara daya daya dauka yana bin Hindu kamar babu zuciya a kirjin shi kan ta sake bashi dama, amman tayi biris da shi, ita kanta harta kammala bautar kasarta.

“Ni karatu zanci gaba, ba aure bane a gabana Hamza, na farkon da nayi kaine shaida akan yanda ya kare…”

Shine abinda ta fada mishi, ya roki Anna tayiwa Appa magana a taya shi lallashin Hindu, tace mishi,

“Ba zan shiga maganar nan ba, ba zamuyi amfani da girman mu da yarinyar nan take gani mu tirsasata ba, ka lallabata da kanka, idan kuna da rabon sauran zama zata dawo. Amman kam kayi hakuri, ni da Appan ka mun yanke hukuncin ba zamu shiga zancen ku da Hindu ba.”

Maganar Anna ta kara kashe mishi jiki, duk da har a zuciyar shi yana son Hindu, yana azabtuwa da rashinta, musamman yanzun da yake ganin yanda ta kara kyau, ba a gane hankali ta fuska, tunda ba’a rubuce yake ba, amman zai iya rantsewa akwai hankalin da yake gani a fuskarta da baya gani a da. Duk da shima AbdulHafiz yace mishi su Suhana sun saka har kunyar mutane ya fara ji yanzun, duk da rikicin shi na banza yana nan babu inda yaje. Yanzun ma Fodio ne ya bashi karfin gwiwar sake tunkarar Hindu, ya dauka yagama ganin abin mamaki sai daren jiya da wayar Fodio na hannun shi yana duba design brief din wani abokin wasan Fodio din da yake son ayi mishi zane ya turo, kiran waya ya shigo.

Sosai Hamza yake kallon wayar, ganin Mansy, mikawa Fodio wayar yayi, ba ya manta da ita bane ba, yakan tunata lokaci zuwa lokaci, amman tunani ne na inda rayuwa ta kaita, ba wani abu ba, har ranshi yana mata addu’ar shiriya, ta samu dalilinta kamar yanda ya samu nashi, sosai yake kallon Fodio da yanayin yanda yake wayar da Mansy

“Tun yanzun zakiyi bacci kibar ni?”

Yanayin yanda Fodio ya ajiye maganar nasa wani abu tsirgama Hamzan da bashi da alaka da kishi, sai tsantsar mamaki da tsoron da baisan dalilin shi ba, har Fodio ya sauke wayar daga kunnen shi Hamza na mishi kallon tuhuma.

“Karka tambayeni yaushe ya fara, nima ban sani ba.”

Fodio ya furta yana samun waje ya zauna. Suna dan hira da Mansy sama-sama lokacin da take tare da Hamza, ko in tazo wajen shi, ko idan ya raka shi wajenta. Abu daya yasani tun a lokacin, da badan yarinyar Hamza bace zai taya shima, sai dai su din basa hada nema ko da na banza ne. Ta kitchen din gidan shi ranar da ta dawoma da Hamza mota yaji duk maganganun su. Baisan me yasa ya kirata a ranar ba, yasan labarinta, yasan rashin iyaye har biyu na daya daga cikin tushen lalacewar ta, zai fahimci wannan bangaren fiye da kowa.

Bai kirata ba sai karfe goma na dare a ranar, amman kuka takeyi har lokacin, ko muryarta bata fita sosai.

“Ina tunanin rayuwata Fodio…ina tunanin abubuwan da zasu faru da na tashi da iyayena duk da ba zai taba zama hujja a gareni ba.”

Har zuciyar shi yaji maganganunta, saiya tsinci kan shi da kiranta a kullum dan yaji lafiyarta. Sai ya sake tsintar kan shi da takawa har inda take dan ya dubata da idanuwan shi. Ya fahimci dalilin Mansy da yayi mata maganar tayi aure.

“Wa kake ganin zai aureni batare da bincike ba? Wa kake ganin iyayen shi zasu yarda ya aureni bayan sun san rayuwar da nayi? Sirri irin nawa baya boyuwa komin gyaran da akai mishi…”

Shisa da yawan karuwai wa’azi baya shigar su, saboda in basuji ba sunga yan uwan su da tuba baiyiwa rana a duniya ba, duk da inda za’a tonosu a basu ikon magana zasu bada labarin yanda tuban ne zabi mafi alkhairi da sukayiwa rayuwar su, duk da mutanen da suke yawo da zunubai mabanbanta basu karbe su ba, ko da malamai suka zama akwai mutanen da zasu furta.

“Abin da a baya kowa yasan tsohuwar karuwa ce.”

Kamar zunuban su ba zasu yafu ba, suna manta yanda ba’a shiga tsakanin bawa da Ubangijin shi, suna manta yanda Rahma ta Ubangiji ce, wanda yaso a cikin bayin shi yake nufa da samunta. Shisa da yawa suke zabar zama inda suke tunda ko sun tuban baya wanke laifukan su na baya a idanuwan mutane. Akwai irin su Mansy da yawa, akwai iyaye da yawa da ba zasu taba barin yaransu su auri irin Mansy ba.

“Ba zaka hadamun zuri’a da karuwa ba.”

Sukan kafa hujja da zance irin wannan, sosai suke manta a cikin mummuna Allah yana fitar da me kyau, a cikin me kyau Allah yana fitar da mummuna, dan da yawa idan aka bincika asali, iyayen su mutanen kirkine, kaddara ce kawai basu tsallake ba. A ranar Fodio yasan idan aure zaiyi ba zai samu macen da yaji ta dace da rayuwar shi kamar Mansy ba. Bashi da wanda zai damu dayai bincike a kanta ballantana bayanta ya dami wani, indai tana da wakilan da nashi zasu samu da maganar aure shikenan. Yasan rayuwar shi ta baya ba zata hana shi samun macen kirki ya aura ba.

“Ka san wacece Mansy, Fodio ka sani.”

Hamza ya fadi yana son karin tabbacin Fodio din yasan abinda yakeyi. Ya tuba shikam, shisa yake addu’ar Hindu ta dawo mishi, ya yarda da nagartarta, ba zai iya wahalar neman wata matar ba, ba zai iya duk wannan fargabar ba, dariya Fodio yayi da bata da alaka da nishadi

“Da in auri macen da zata canza mun, gara in auri macen da zata canza mun.”

Kallon shi Hamza yayi, dan magana daya ce ya maimaita, kai Fodio ya jinjina mishi.

“Canji biyu nake magana, mata nawa ne zaka aure su a kintse sai bayan auren su canza maka? Canjin da sai kayi dana sanin auren, gara in auri Mansy da halayenta da zata canza mun, nasan dukan mu da zuciya daya zamuyi, Allah zai taimake mu ba zamu taba dana sanin auren juna ba.”

Yakinin da yake muryar Fodio shi ya taba zuciyar Hamza fiye da maganganun shi, dan ba fahimtar su yayi ba, har ranshi baiga dalilin da zaisa ya auri Mansy ana zaune lafiya ba. Allah ya shirye su duka ya hada kowa da rabon shi.

“Sai dai in kana da matsala da aurena da ita, matsala daban da bata shafi halayenta ba.”

Da sauri ya girgiza ma Fodio kai, daga ranar daya karbi mukullin motar shi ya yanke alaka da Mansy gabaki daya.

“Bani da wata matsala da Mansy.”

Numfashi Fodio ya sauke.

“Mansura, sunanta Mansura.”

Murmushi kawai Hamza yayi yana girgiza kai, sosai Fodio ya bashi karfin gwiwar sake tunkarar Hindu. Yau zasu gama maganar nan duk yanda take kauce mata, hular shi ya dora saman kan shi yana daukar mukullan mota ya sauko kasa yana ficewa daga gidan.

<< Mijin Novel 30Mijin Novel 32 >>

1 thought on “Mijin Novel 31”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×