Skip to content
Part 8 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Ita kanta ba zatace ga asalin abinda yake damunta ba, amman sai da ta kwana biyu ko makaranta bataje ba, da yake kowa a gidan ya santa da nacin zuwa makaranta, babu wanda ya takura mata, duk kyaleta sukayi da tace bata jin dadin. Ranar na ukkun ne da taje ta sami assignments sun tarar mata kamar tayi wata daya bataje makaranta ba, da sanyin jiki hadi da dana sani marar misaltuwa ta dawo gida. Ta rasa ta inda zata fara taro kwanaki biyun da ta rasa a makaranta. Tana cin abinci ta watsa ruwa, hadi da alwalar magriba duk da akwai sauran mintina talatin, bata so idan ta zauna ta sake tashi, har hijab din da zatayi amfani da shi ta dauko.

Assignments din ta fara ragewa na rubutun, tana barin zanen sai da tayi Magriba tukunna ta hau kan drawing board dinta, zanenta takeyi tana sauraren wakokin Ed Sheeran da yake bala’in burgeta saboda kalaman da yake amfani dasu wajen wakar, gajiya tayi wajen tara ta mike tana zuwa ta sake yin alwala tayi sallar isha’i, akwai abinda ya daure mata kai a zanen, ta kasa fahimtar shi, tasan ba za’a rasa wanda ya gane ba cikin yan ajin nasu, zata iya bari da safe in taje makaranta, dan haka tabi lafiyar gado, da yake tana zanen tana ciye-ciye kamar yanda yake sabonta, bata jin yunwa.

Wayarta ta janyo tana shiga Instagram, kafin ma tayi refreshing taci karo da hoton AbdulHafiz, ko tace hannuwan su shi da yarinyar da alama ita zai aura, ba rike suke da junan su ba, nashi hannun akan cinyar shi, nata ma a kan tata cinyar, yasha jan lalle, zoben su iri daya, hakama agogon hannun su, irin wanda masoya suke siye, ya saka caption din

‘Mine’

Sai yayi tagging din handle dinta da tuntuni Hindu tayi following din yarinyar dan ba karamin burgeta sukeyi ba ita da AbdulHafiz, wata irin soyayya sukeyi mai sanyin gaske. Zuwa yanzun tasan cewa AbdulHafiz jinin sarauta ne, amman batasan dan Sarki bane ko hakimi, itama kuma Nabila din, budurwar tashi a jikin profile dinta ta rubuta ‘Royalty’ kuma tana yawan daukar hotuna akan doki, ko cikin gidan Sarauta da Hindu ba zatace Masarautar wanne gari bace ba, ko yaushe baka raba hotunan da Hindu take sakawa da Alkyabba a jikinta, masu kyau, duk da fuskarta zakaga da nose-mask da yake hana maka ganin gabaki daya fuskarta, shi kan shi yaci ado dai-dai da duk wata alkyabba da zata saka.

Garama kwanaki taga AbdulHafiz ya saka wani hoton Nabila da rabin fuskarta ne kawai, kuma an saka hoton a baki da fari, ta hadu harta gaji. Lokaci da dama Hindu kanji kishin Nabila na rashin dalili, saboda yarinyar ta sami duk wani abu da take mafarkin samu, namiji hadadde jinin sarauta ma, ga shi ya iya soyayyar da take sakata cire Nabila tana dora kanta a madadinta lokutta da dama. Ko Hamza takan ga ya saka abinda ya danganci su AbdulHafiz din da caption din ‘Couple crush’.

“Hmmm….”

Hindu ta fadi a fili da ta shiga shafin Nabila taga ta saka hoton AbdulHafiz din da yake dariya ya daga hannu yana kokarin kare fuskar shi kamar bai shirya hoton ba aka dauka, ga dimple din shi daya bayyana yana saka zuciyarta dokawa, Nabila din ta saka caption din

‘Allah ya kai fata Mizani Dikko Na.’

Gyara kwanciya Hindu tayi, duk da zuciyarta ta furta mata.

‘Wata miyar sai a makota.’

Batason barin wannan tunanin yayi tasiri a tare da ita, In shaa Allahu yanda take addu’a babu dare babu rana, itama miyar makotan nan a gidanta za’a dinga yinta. Bata san ko ganin su AbdulHafiz bane ba, ko kuma kalar Samarin da ta dinga haduwa da su, ciki harda Jalil ya sata yin abinda takeyi yanzun ba, kawai tsintar kanta tayi da shiga DM din Hamza tana mishi sallama hadi da rubuta

‘Ban san ko zaka ga sakon nan ba, ban ma san ko zaka karanta ba.’

Tukunna ta tura mishi matsalar da bata gane ba, dangane da assignment dinta tana dorawa da

‘Watakila sanda zaka ga sakon nan ma har na gama. Duk da haka nagode.’

Ta karasa tayi minimizing tana tashi zaune, har wata zufa takeyi kamar wadda tayi gudu, zuciyarta na mata sake-sake kala-kala. Sake kwanciya tayi tana komawa tayi screenshot hadi da komawa whatsapp ta turama Dimples

‘Nama Hamza DM’

Ko mintina biyu batai ba, sakon ya nuna alamar yaje an karanta, harma Dimples din na rubutu

‘Wanne Hamzan?”

Numfashi Hindu taja tana fitarwa, zagin da tasan zata sha wajen Dimples shisa ko da wasa bata taba bata labarin Hamzan da yanda take bibiyar shi ba, yanzun ma kawai ca tayi mata

‘A Instagram nake ganin shi, yana burgeni sosai, kuma Architect ne.’

Tsaki Dimples din ta turo mata

‘Allah yasa ya watsa maki zagi tunda ke baki da tunani, halan Jalil bai koya maki hankali ba? Kinsan ni bana wani yin Instagram, saboda nasan makaryata sunyi yawa a wajen. Kilan ma duk abinda yakeyi yana burgeki din Fake ne, Hindu ki rufama kanki asiri da mazan social media, kiyi addu’a Allah ya kawo miki wanda zaki natsu da shi’

Kai take girgizawa tana karanta sakon

‘Ke shi ba karya yake ba.’

Emoji din harara Dimples din ta aiko mata

‘Kici gaba dai, tunda baki da hankali har yanzun. Ni dai na fada miki, Wallahi ki kiyayi mazan Social Media.’

Sauka kawai Hindu tayi daga whatsapp din, daman abinne taji ba zata iya barma cikinta ba shisa ta fadama Dimples din, duk da tasan halinta da kuma yanda sam bata da yadda, mutanen da take gani ma bata yarda dasu ba, ballantana na Social Media, bama mutane Dimples take so ba, lokutta da dama zakaga ta daga girarta in tana danna waya, duk idan ka tambaya zata ce

‘Mutane ne suke mun magana, me yasa mutane suke mun magana ne wai? Halan basu san ni ba son su nake ba.’

Har dariya take ba Hindun, sai dai duk baudadden halinta tana da dadin zama, saboda tana da wani irin kirki da ba ko yaushe ake samun mutane masu irin shi ba yanzun, sai dai tana cikin mutanen da ake kira ‘kai fi daya’ kuma cikin wanda ake cewa su ‘tsaye’ suke, shisa sai kayi tunanin magana Dimples ta fada maka wasu lokuttan, amman har ranta hakikanin gaskiyarta ta fadi, bata damu da ya zaka dauki hakan ba. Shisa suke fada da Hindu wasu lokuttan, saboda tana mata fadan gaskiya.

Wayar Hindu ta saka a key zata ajiye sai taji ‘dit’ alamar sako ya shigo, da sauri ta danna ta cire key din ganin notification din na Instagram ne, shiga tayi tana budewa, zuciyarta na wani irin tsalle ta dawo wuyanta, kafin ta koma kirjinta tana cigaba da dokawa kamar zata fito, ganin da tayi Hamza ne ya amsa sallamarta, ya dan dauki mintina kafin taga ya turo hoton da tayi saurin budewa tana ganin ‘Rough sketch’ daya warware matsalar da ta kasa na zanen nata, sai dogon sharhi cikin gamsashen bayani daga kasa.

Wani irin murmushine ya subuce mata, tayi wani tsalle tana dawowa kan gadon, hadi da mirginawa tana jin kamar an mata albishir da kujerar hajji da duk wani cikar burinta saboda farin cikin daya lullubeta, tuntuni inda tasan maganar Architecture itace zata saka Hamza ya kulata a DM da tafi shekara da tura mishi, yanda in tayi mishi a comment section yake yin biris da ita yasa bata taba tunanin zai amsa mata magana ta private ba. Hamza fa, Hamza Abu Abbas ne ya zauna yayi mata bayani harda zane yanda zata fahimta sosai. Rubutu ta soma yi tana tura mishi

‘O. M. G,  wallahi ban taba tunanin zaka amsani ba, banma san me zance ba, na rasa ta ina zan fara, har yanzun ina ganin kamar mafarki nakeyi ka amsani, Nagode, Nagode, Nagode’

Baifi minti daya ba ya turo mata gajeriyar amsa

‘Uw’

Daya nuna alamar da wahalar gaske ya sake cewa komai, amman a hakan ma ita ce da dubban godiya, dan yau ya gama mata komai, ya wanke mata bakin cikin da ta kwasa a watannin nan, ranta kal take jin shi, dan tashi tayi ma ta koma kan zanen da takeyi. So takeyi ta gama ta dauki hoton ta tura mishi, tana jin alamar ko da zata kwana tana zane yau babu gajiyar da zata saukar mata, sakon Hamza ya zame mata kamar ‘Energy drink’.

***** *****

Zaune yake kan doguwar kujera ya jona cajar system din shi a jikin extension din dake falon ya janyo wayar yana kokarin hadawa. Fodio ya fito daga daya daga cikin dakunan baccin, kugun shi daure da towel, sai wani karami yana goge kan shi da shi, ya zo tsallakewa yayi ciki da cajar Hamza din da ya buga wani tsaki yana dorawa da.

“Wawa ne kai Allah… Wanne iskancine ma zaka fito tiqi-tiqi da towel kana goge mana kai a falo?”

Arafat da yake zaune yayi dariya mai sauti, Fodio kuwa towel din ya sauke daga kan shi

“Ni da gida na? Sai a hanani yin abinda nake so? Kaji mun wani karfin hali dan Allah.”

Tsakin Hamza ya sake ja yana rankwafawa ya dauko cajar tashi ya jona hade da system din. Da gaskiyar Fodio, gidan shine da yake nan Malali, shi dan asalin garin Kano ne, Mahaifin shi dan kasuwane da zai shiga cikin jerin manyan yan kasuwa da ake sarin kayan masarufi a wajen su a garin Kano, matan shi hudu, mahaifiyar Fodio itace ta biyu, kuma shi kadai ta haifa kafin Allah yai mata rasuwa tun yana da karancin shekaru, ya sha gwagwarmayar rayuwa, shisa yaci burin karatu dan ya zama wani abu ya daga ma gidan nasu ko zai huta da yan ubancin da ake nuna mishi kiri-kiri.

Da yake mahaifin shi ba wani damuwa yayi dasu ba, sun kai su arba’in a wajen shi, kudine duk idan ka tambaya zai dauka ya baka tunda ba matsalar shi bane ba, ko karatu Bauchi Fodio ya zaba, can kuma yaje ya karancin bangaren gini, ya fita da sakamakon da makarantar suka so rike shi, sai dai tuntuni yake burin zama garin Kaduna, hakan yasa shi yayi cuku-cukun da bautar kasa ta kai shi Kaduna, ya kuma yi zaman shi da yake yayi sa’a kamfanin sun yaba da kwazon shi suka kuma rike shi. Tsarin baban sune duk yaran shi Maza yakan siya musu gidaje, Fodio ya zabi a siya mishi na shi anan garin Kaduna, bai kuma sami matsala ba, ba zaice ga ranar shi ta karshe da yaje garin Kano ba.

Arafat dan nan Kaduna ne, duk da asalin su dan garin Kaduna ne, Structural Engineer ne, su ukkun sun hadu wajen IT, shi da Hamza da kuma Fodio din, a wani construction company a garin Abuja, jinin su ya hadu suka kuma zama aminnai kafin wani lokaci, duk da karatu ya watsa su wajaje daban-daban, sun ma kan su alkawarin duk zasu zauna a Kaduna suyi nasu kamfanin na qashin kan su komin shekarun da hakan zai dauke su. Abdallah ne kawai a cikin su abinda ya karanta ya banbanta da nasu, tunda shi aikin Banki yakeyi kafin daga baya ya dawo karkashin su Hamzan da aiki,  kuma shi kadai ne talaka a cikin su, ya hadu da Arafat da Fodio ta sanadin Hamza, sun taso unguwa daya tun suna yara, da ya zama wani kuma ko kadan bai yarda zumuncin da yake tsakanin su ba.

Sosai Abdallah yake samun rufin asiri ta fannin Hamzan dan shi mutum ne da hannun shi yake a bude, kuma irin mutanen da zasuyi komai dan abokan su. AbdulHafiz da Civil Engineer ne, kuma jinin Sarauta gaba da baya, daga garin Gombe, Sarautar garin da wahala taje hannun mahaifin AbdulHafiz din, dan anfi saka ran idan Allah ya dauki ran Sarki maici na yanzun babban yaron shi za’a ba, kuma shine Wan mahaifin AbdulHafiz din, a takaice dai jikane shi wajen Sarkin Gombe. Wajen taron da akeyi na manyan Architects da Hamza ya ziyarta yana shekarar shi ta ukku a makaranta suka hadu da AbdulHafiz ya rako Yayan shi da yake cikin manyan baki a wajen taron.

Da yake Hamza mutum ne mai shiga rai lokaci daya, jinin su sai yayi wata irin hadu Hamza din, a haka su biyar suka zama abokan da suke jin junan su tamkar yan uwa. AbdulHafiz shiya dinga samo musu ayyuka daga manyan mutane har sukai kudin da suke da shi yanzun, aka kuma san su a wajaje da dama cikin fadin Nigeria, kamfanin su yana nan garin Kaduna na HAF constructions. Kalmomin farko na sunan su sukayi amfani dashi, sannan abokantakar su bai hanasu kafa kamfanin akan duk wasu ka’idoji da ya kamata ba, har da lawyoyi da kowa yake da shi, saboda halin rayuwa, ko ba da babu mutuwa. Duk da a tafiyar tasu ko kadan basa hango rabuwa ta sanadin samin matsala.

Basu zo inda suke yanzun ba sai da fahimta sosai, duk a cikin su ma AbdulHafiz ne halin shi ya fita daban, ko magana sai kayi da gaske zaka ji tashi, suna iya tashin dakin da surutu sai dai ya bisu da idanuwa, ko zage-zagen da akeyi tsakanin abokai, sai dai su din su zage shi, amman shi ba zaka taba jin zagi a bakin shi ba, idan Sarautar ta motsa mishi ma, ko hayaniyar zakaga baya so, sai dai ya tashi yabar musu dakin, in sun ishe shi yabar gidan gabaki daya. Su dukkan su babu wanda bashi da gida da komai na bukata a ciki, sunfi zama gidan Fodio ne kawai. Abdallah kuwa da yake yana da matar shi, sai dai yazo su danyi hirar da zasuyi ya wuce, idan aiki bai sha musu kai ba kenan.

Yanzun ma duk maganar da suke ya lafe cikin kujera da wayar Hamza a hannun shi, su duka suna daukar wayoyin juna, amman sun san iyakarsu a kai, duk kusancin su ba zaka tsinci daya daga cikin su na bude sakon wani ba sai da izini. Kome zasuyi da wayar kuwa, zasu iya shiga banki tunda duk sun san lambobin sirrikan juna su tura kudi, ko su siyi kati, amman ba zasu duba sakon da bai shafe su ba, suna girmama junan su, dan waya sirri ce, duk yanda kake ganin kusancin ka da mutum kuwa, akwai wani sirri a ciki da ba lallai yaso kagani ba.

Ko AbdulHafiz din daya shiga Instagram, Hamzan yace ya dora mishi wani zane daya gama. Sai ya tsaya kallon hotunana, yana ganin yanda sakonni ke ta shigowa

“Kai baka duba sakonnin ka ne.”

Ya bukata, Hamzan na girgiza mishi kai.

“Instagram ne fa!”

Fodio daya zauna gefen Hamzan ya amsa da

“Instagram din fa, kasan aiki nawa na samar mana ta Instagram din?”

Dan daga kafadu Hamza yayi dan shi kam bashi da lokacin tarkacen Instagram, ya dauke shi wajen ajiye hotunan shi, in yanajin kwiyar mayar dasu kan system. Ga shi da yarda waya kamar me, idan bai yardar ba za’a sace tunda duk inda zaije haka yake barin gilasan mota a bude. AbdulHafiz kance.

‘Rashin adani na cikin almubazzaranci Hamza, saboda kana da kudin siyan wata wayar baya nufin ka dinga sakaci da wadda kake da.’

Amman haka zai sake bari a sace, kusan indai da AbdulHafiz za’ayi fitar shi yake rufema Hamzan gilasan mota, tun yana fada harya gaji ya saka ma Hamzan ido

“Da gaskiyar Fodio, ana samun clients a Instagram fa.”

Arafat ya fadi, kafadun Hamza ya sake daga musu wannan karin hadi da fadin

“Hafiz ka shiga kagani, tarkace ne fa.”

Shigar kuwa Hafiz yayi, yanata duba sakonnin, da gaskiyar Hamzan, tarkacen su suka fi yawa, yawanci sakon gaisuwa, yan mata ma sunfi yawa, suna saka AbdulHafiz jinjina ma kokarin su, bawai yaga rashin ajin su ba, dan sun yiwa Hamzan magana, kawai dai yana ganin kokarin su wajen sake yi mishi magana bayan bai amsa waccen ta baya ba

“Hindun Baban ta.”

AbdulHafiz ya karanta a fili, yana saka su ukkun kallon shi, kafin kowa yaci gaba da abinda yakeyi, sunan ne yayi mishi wani iri, sakon ya bude, yanayin murmushi, yanayin shiriritarta tayi mishi kama da ta Nabilar shi, yarinyar da ya dinga dakon soyayyarta tun kafin tayi hankalin da zata san yanayin ta, har Allah ya taimake shi ta fahimta, ta kuma amsa tayin shi, yanzun gashi har manya sunsan da maganar, da yake abu na cikin gidane, abokiyar wasan shice, basu kuma sami wata matsala ba.

Hakan kawai yasaka shi amsa ma Hindu sallamarta, yana karanta sakonta, duk da ba fannin shi bane, matsalar tata ba wata babba bace ba, mikewa yayi yana zuwa dakin da indai zai kwana a gidan nan yake kwana, dan shi baya son jin hayaniyar komai in har yayi shirin kwanciya, ko da ba baccin zaiyi ba, ya dauko littafin da yakan yi zane-zane a ciki, sannan ya dawo inda yake ya zaina yana zana mata yanda taswirar matsalar take, ya dauka hoto ya tura mata, tukunna ya hada dayi mata bayani dalla-dalla, sai yaji ta burgeshi, dan karatun da takeyi din bakowacce mace bace zata iya.

Lokacin da yan makaranta da yawa, harda masu nacin karatu zasu kai sha biyun dare su kwanta, Hindu zata kai asuba kan abin zanenta tana aiki, washegari kuma ta tafi makaranta, asalima zata iya sati daya a kowanne dare da wahala ta sami baccin awa biyu cikakke, lokacin da sauran dalibai suke tafiya gida duk idan an gama jarabawa, lokacin Hindu zata fara zuwa makaranta dan yin presentations na project dinta na wannan zangon. Dalibai kanyi project daya tal bayan shekaru hudu ko biyar, Hindu kanyi guda biyu kwarara a shekara daya, banda kananun da ba zasu kirgu ba.

Duk da Hamza kance mishi ko a mafarki yaga zai karanci Civil Engineering idan ya tashi zaiyi sadaka, dariya kawai AbdulHafiz din yakan yi, dan yana da tabbacin babu wani abu da zai gagari Hamza in dai ya sa kan shi, domin yana da kwakwalwa da AbdulHafiz kan gani a fina-finai na kasashen ketare, yakan kuma ji labarin mutanen da ake ma laqabi da ‘gifted’. Bai taba cin karo da su ba sai da ya hadu da Hamza.

“Me kakeyi haka?”

Fodio ya tambayi AbdulHafiz din

“Wata yarinya na amsa.”

Ya fadi a takaici yana saka Hamza dagowa daga zanen da yake a laptop din shi ya kalli AbdulHafiz din

“Me yasa zaka amsa ta? Da nace ka duba nace ka amsa ne?”

Idanuwa AbdulHafiz ya kafe Hamzan dasu da ya saka shi kauda kai da cewa

“Ni dai da baka amsa mun ba.”

Hankalin shi AbdulHafiz ya mayar kan wayar da yake dannawa, su dukan su yana musu wani irin kwarjini, ba ko yaushe maganganun su ke da amsa a wajen shi ba, kallon su kawai yakeyi sai kowa a cikin su ya kama kan shi, sun san AbdulHafiz, ba ko yaushe yake wasa dasu ba, yana karasawa ya ajiye wayar yana mikewa, dan lokacin wayar shi da Nabila yayi, yana barin wajen Hamza yace ma Fodio

“Dan miko mun wayata dan Allah…”

Wayar Fodio ya mika mishi, shima yana tashi yabar wajen, dan ya fita zaiyi ya siyo musu abinda zasuci, shi kam yunwa ta fara naniqar shi, har tara da wani abu. Sakon da AbdulHafiz ya amsa Hamzan ya duba yana shiga profile din Hindu, hotunanta ya shiga yana tsayawa kan wani da take sanye da farin Hijab

“Woow”

Ya tsinci kan shi da furtawa, ta mishi kyau badan bai tana ganin yan matan da suka fita din ba, kawai ya manta ranar karshe da mace tayi mishi kyawu a idanuwan shi har haka.

<< Mijin Novel 7Mijin Novel 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×