Rannan cikin dare ruwan sama mai karfi ne yake sauka kamar da bakin kwarya, ina kwance can cikin daki akan katifata bayan na shafe jikina da mayuka masu kamshi da kara laushin jiki sai da na feshe jikina sosai da turare mai sansanyar kanshi, sannan na shige cikin bargona na ruhu.
Ina jin yanda ruwa ke sauka da kuma sauraron tsawar da aka yi ina mai karanto addu’o’in da ake yi lokacin saukan ruwa, ko kuma tsawa. Ni kin kawar min da kofin da kanwar nan ke ciki ne? a hankali na ce mishi eh, ai ban san. . .