Gambo ta kalle ni so yake ki koma gobe? Na bata rai saboda ran nawa ya baci, na ce ban sani ba tunda ya kashe, to kira shi mana kiji, ya baro ki kin zo lafiya cikin farin ciki da alhairori iri-iri ai ba za ayi sanadin bacin ranshi ba.
Na sake kiranshi, nayi zaton ba zai dauka ba, sai naga ya dauka. A hankali na ce mishi kayi hakuri in ranka ne ya baci, ko da bana kusa dashi nasan murmushi yayi.
Gambo tana nan kenan? Na ce mishi eh, ya ce nasan ita ce zata ce ki. . .