Ina zaune a falona ina karatun littafin (Riyadus-salihin) babin godiya kan ni'imomi nake karantawa, Baba Yahya ya shigo da gudu, can bayana ya tsallaka ya wuce ya buya.
Sai ga Umamatu ta biyo shi a fusace, ga dukkan alamu tsokanarta yayi, ta bude baki da nufin yin magana fushin nata yayi tsanani, na daga ido na kalle ta cikin natsuwa na ce mata.
"Umamatu sau nawa zan gaya miki cewar Ubangiji yana son masu hadiye fushinsu, nan da nan ta 'sauka, ta kalle ni cikin ladabi ta ce na hadiye Goggo, na ce to ai kin san kuma. . .