Na daga ido na kalle shi cikin natsuwa, na tambaye shi wani abu ya faru ne? ya ce me kika gani? Na ce uh'uh nayi shiru naci gaba da abinda nake yi, shima ya kashe wayoyin nashi ya kara gyarawa Baba Yahya jinginon da yayi a jikinshi yana bacci wai don ya kara jin dadi.
Jimawa can sai naji ya ce min ke a rayuwari ai ke 'yar gata ce Humairah nayi maza na ce mishi da aka yi me? ya ce to kin rayu tare da uwa da uba da Kakanni na bangaren uwa da uba.
Ki duba. . .