Karfin karar albarusai da suka fito daga bututun bingigan nan da ake kira AK47 ne suka fiddamu daga nisan barci da muke yi. “My dear, meka faruwa?” matata Muhibbat ta tambaya cikin ruɗani.
Kafin na buɗe baki nace wani abu, tuni wasu albarusai sun tarwasa gilashin windo dake dab da gadon da muke kwance. Nan take na damko hanunta na jawo ta ya zuwa bajewa a kasa. Zuciyata na duka uku-uku leɓɓan bakina na furta kalmar 'Innalillahi wa inna ilaihirraji'un'.
Shiru ya biyo baya ba motsin komi idan aka ɗauke sautin kukan karnuka dake tashi. . .
Masha Allah, muna jiran next chapter.
Lbr yayi dadi ubangiji ya kara kaifin Alkalami