Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Mijina Wukar Fidar Cikina by Ahmad Sale Muri

Karfin karar albarusai da suka fito daga bututun bingigan nan da ake kira AK47 ne suka fiddamu daga nisan barci da muke yi. “My dear, meka faruwa?” matata Muhibbat ta tambaya cikin ruɗani.

Kafin na buɗe baki nace wani abu, tuni wasu albarusai sun tarwasa gilashin windo dake dab da gadon da muke kwance. Nan take na damko hanunta na jawo ta ya zuwa bajewa a kasa. Zuciyata na duka uku-uku leɓɓan bakina na furta kalmar ‘Innalillahi wa inna ilaihirraji’un’.

Shiru ya biyo baya ba motsin komi idan aka ɗauke sautin kukan karnuka dake tashi daga nesa.

‘Meke faruwa da mu ya Allah?’  Na furta lokacinda Muhibbat ke kaɗawa tamkar leda a cikin guguwa.

‘My dear waɗannan ba ɓarayi ba kuwa?’ Ta tambaya cikin ɓoyeyyiyar murya mai ɗauke da fargaba.

An sake samun wadatar shiru tamkar akasi aka samu wajen kawo mana harin. Hakan ya bani damar yin-ja-da cikin ya zuwa ɗaukar wayan salulata dake kan duruwan madubi.Nan take na mika hanu na sake kamo hannun Muhibbat na janyota muka rarrafa zuwa bayan ɗaki dake cikin ɗaki.

Cikin fargaba na danna lambar ofishin ‘yan sanda.’Hello who is on the line?’ Wata kakkaurar murya ta tambaya.

‘Ofisa, ina kira ne daga unguwar barade gida mai lamba 73 layin Ibrahim Abacha. Ranka ya dade ɓarayi ne suka shigo mana unguwa, yanzu haka sun rikita ko ina da karar bindiga. Don Allah a kawo mana ɗauki cikin gaggawa!” Na furta masa yayin da gumi ke bin duk wani sassa dake jikina. ‘Im sorry yallaɓoi, bamu da isasshen mai a mota, ku yi hakuri’. Ɗan sandan ya faɗa tare da datse waya.

Yin hakan ya zo daidai da lokacin da ake dukan kofar falona tamkar za a balla. ‘Salauddeen…muna umurtarka da ka buɗe kofan nan cikin tsanaki da kwanciyar hankali. Sabanin hakan, zaku iya haɗuwa da fucin bakin dalma dake hannun mu.’

Da jin wannan umurnin na kalli matata Muhibbat, itama ta mai da kallonta gare ni, sabon firgita da ruɗani suka daɗa bayyana a garemu. Muhibbat ta fashe da kuka lokacin da muka ji an sake harba albarusai a sararin samaniya. Ko shakka babu bamu da wata dabara illa mu mika kai.

‘Salauddeen muna sake gargaɗanka a karo na karshe, ka buɗe kofa ko mu buɗe da karfin bindiga mu same ku. Salauddeen……! Mun san kana jin mu. Muna matukar tausaya wa halin da zaku tsinci kanku a ciki matukar ka butulce wa umurnin mu.

‘Na ɗaga hannuna sama wanda ke nuni da cewa na mika wuya. Na doshi kofar fita bayan ɗaki da muke ɓoye. Muhibbat ta yi sauri ta rike rigata ta baya, na waigo na kalleta. Ta kaɗa kai cikin tsoro da fargaban abin da zai biyo bayan yunkurin da nake kokarin yi.

‘My dear ba mu da zaɓi, don idan suka ɓalla kofa suka shigo zasu iya halakamu’. Na faɗa mata lokacin da ita ma ta fihimci cewa zan buɗe ne don ya zama dole.

‘Kana da minti uku Salauddeen matukar baka buɗe ba ka kira ku da sunan matattatu’.

A hankali na sa hannu cikin sadaukarwa na juya mabuɗi kofa, kafin na seseta nunfashina, an bankaɗo kofar ya zuwa ciki. Nan take na ji an dalla mini mari wanda karfinsa ya ba walkiya damar ratsa idanuna. Lamarin bai tsaya nan kawai ba, kai tsaye na ji an kwashe kafafuna na zube  kasa.

“Ka ɗauke mu ‘yan iska marasa aikinyi ko? Zaka tsaya kana ɓata mana lokaci. Ina iyalanka?”

“Tana…tana ciki”. Na faɗa  lokacin da karfin zafin mari ke raɗaɗi tamkar an shafa min borkono. Ba a jima ba na ji an cillo Muhibbat ya zuwa gefena.

“Bani wayarka” Ɗaya daga cikin muryoyin ya umurce ni. Na sa hannu cikin aljihuna na ciro karamar wayata na mika masa. Nan take aka sake dalla mini mari. “An ce maka mu matsiyata ne da zaka bamu wannan waya. Ka bani wayarka ta iPhone wacce ka saya a MSDK Communication Ventures dake titin Maitama.

“Wayar tana ɗaki a cikin durowar madubi, amma don Allah me kuke so na baku ku rabu da mu?” Na tambaya cikin fargaba.

 “Ko kasan mu su waye? Kinnapers ne. Don haka bamu bukatar sisinku, zamu tafi da kai ko matarka”.

Nan take na ji tamkar hanjin cikina sun harɗe, zuciyata ta karfafa addu’a da fatan mafarki nake yi.

“Dont waste our time, take him!” Wata murya mai matukar kauri ta furta wanda ke nuni da cewa mamallakin muryar shine jagoransu.

Ba ɓata lokaci aka jajumi wuyar rigata, kafin a ɗagoni zuwa kan kafafuna, Muhibbat ta taso ta rungume ni.

“Don Allah don Annabi….Don darajan Manzo Allah ku faɗi abin da kuke so mu baku ko kuma wallahi saidai ku tafi dani nima, don bazan rayu babu shi ba,” Ta furta lokacin da nake jin taushin fatar jikinta na shuɗanya da tawa fatar jikin. Nima na yi sauri na kankameta don na bata kwarin gwaiwa bisa shahadarta.

“Ranku shi daɗe muna iya baku duk abin da kuke bukata matukar mun mallake shi. Don Allah ku yi hakuri ku faɗi me kuke so?”.

Duk tasu ba wanda yace mana uffan. Kawai da karfin tsiya da kuma duka da gindin bindiga aka ɓanɓare Muhibbat daga jikina. Abin da ya biyo baya shine naji an buga min gindin bindiga a baya. A wannan lokacin ne na fara ji duk wani sauti, motsi da ɓuruntu na kokarin komawa sararin samaniya. Haka a cikin ‘yan dakikan lokaci na daina jin motsin komai, duk wani gaɓa dake jikina ya daina aiki.Daga bisani numfashina ya ɗauke tamkar ɗaukewar wutar lantarki, labari dake fita daga harshen bakina shima ya datse.

Awowi  casa’in da bakwai 97, kwanaki huɗu kenen daidai Muhibbat ke kwance a gadon asibiti batare da sanin inda take ba. Kaɗawar babban yatsarta ta kafar dama ne ya janyo hankali ‘yan uwanta dake cike a kanta; tun ranar farko da aka kawota asibitin. Ko shakka babu, suna zaune ne cikin zulumi da addu’ar Allah ya tashi kafadunta.

Hajiya Adda Manga ta yi sauri ta mike daga zaune, hakan ya ba da damar ganin sandar bugun halittarta. Asalin launin fatarta baki ne, amma ya koma cakulet kolo sakamakon tsawon lokaci da ta ɗiba tana rayuwa a cikin daula. Haka doguwa ce wacce aukin jikinta ya saje da kyauwun shimfiɗar fuskarta.

Ta kurawa fuskar Muhibbat ido, kamar da dai yanda sauran dangin suka yi. Har yanzu Muhibbat bata buɗe ido ba, saidai annurin fuskarta ya canja ya zuwa kama da waɗanda ke da sauran numfashi a duniya. Don haka kamannin kyawun surar halittar fuskarta bai ɓace ba. Ance kyau ɗa ya gaji ubansa, awannan gefe Muhibbat ta yi kama da mahaifiyanta ne wato Hajiya Adda Manga. Domin kuwa idan ka ɗauke kirar bugun halittarta tamkar kwalban kokakola, da kuma hasken launin fatarta, ba abinda ya saura da bai yi kama da na Hajiya Adda Manga ba.

Dakta Sanusi Babagana, dogo baki mai alamun zanen cika-baki a bakinsa, ya buɗe kofa ya shigo cikin gaggawa. Kai tseye ya kura wa Muhibbat ido.

“Don Allah ku ɗan ragu domin kun yi yawa a kanta”. Ya furta lokacin da ya maida kallosa ga sauran ‘yan uwanta dake kallonsa. Nan take ya sa wa Muhibbat na’uran gwadin bugun zuciya don neman sanin tsakanin duniya da lahira a ina tafi karfi. Bayan ɗan mintuna ya kalli Hajiya Adda Manga.

“Insha Allahu zata farfaɗo nan da wasu ‘yan lokaci kuma yana da kyau abata wuri don bai kamata ta farfaɗo ta ga mutane da yawa a kanta ba”

 Kafin Dakta ya rufe baki Muhibbat ta fara kaɗa kai alama dai tana dab da buɗe idanu.

“Muhibbat…” Hajiya Adda Manga ta kira sunanta cikin tsanaki. Ahankali Muhibbat ta buɗe idanu, hakan ya zo daidai da lokacin da wayan salulan Hajiya Adda Manga ya fara kaɗawa. Dagawarta keda wuya taga lambar Sala’uddeen. ” Salamu alaikum, Salahuddeen kana ina?” Hajiyata ta tambaya cikin kishin ruwan neman amsa

“Ki tara hankalinki wuri guda, bashi ke magana ba. Ina magana da Hajiya Adda Manga ce?”

“Itace, dawa nake magana?”

 “Suna ba shi da muhimmanci, ki natsu da kyau ki saurare ni kan abinda zan faɗa maki”. An samu shiru na wani lokaci, kafin muryar ta cigaba.

“Sala’uddeen yana hannun mu. Kin fi kowa sanin cewar ‘yarki na matukar kaunar surikinki. Ko shakka babu zata iya samun ciwon bugun zuciya duk lokacin da ta samu labarin mutuwarsa. Ba ina nufin mun kasheshi ba.The deal is simple. Surkinki zai samu ‘yarki araye idan kin aiko mana da dola dubu ɗari biyu da saba’in da ɗari huɗu da talatin da huɗu da ƙwabo biyu (276,434.002). In nufin miliyon ɗari kachal!. Kuɗin basu da yawa hajiya, musamman idan kika dubi darajar rayuka. Nace rayuka don idan kika yi sake muka ɗauki ran Salahuddeen, Muhibbat na iya bin ran mijinta a lahira. Don haka, kina da awowi ashirin da hudu idan kudin sun zama ready, zan fada miki inda za a kai domin mu sako muku Salahuddeen”.

Hajiya Adda Manga ta ɗauki wata waya kirar Techno dake gefen laptop ɗin ta ta ɗauki hoton adireshin da manhajar ta bayyana. Nan take ta tura a wani layin WhatsApp. Mai maganan ya cigaba.

“Kuma ina son ki sani, a yanzu haka kina Ahmaddeedan Memorial Hospital ne dake babban titi Ardo Buba. Kina ɗaki mai lamba 62F a hawa na uku. Kuma, kina sanye da kaya da indiyawa ke kira sarin. Kalan launin kayan sun fito da kyaun halintarki. Ba kirar halittarki nake yabawa ba. Ina kokarin fahimtar dake cewa duk wani motsi da za ki yi ko kike yi muna sane.

A yanzu ku hudu ne cikin ɗakin da Muhibbat ke kwance wacce har yanzu Dokta Sanusi Babagana ke tsaye akan ta. Haladu shine mutun na hudu dake tare da ku cikin wannan daki. Yana sanye da farin tabarau a fuskarsa, badon yana da matsalar ido ba, sai don yanda ya kasance mai son yin gaye a kodayaushe. Doguwar koriyar jamfa ke jikinsa.

 A karshe Hajiya, na yaba matuka da karfi basirarki. Zan so a ce na aure mace mai irin ƙwanyar da mahalicci ya mallaka miki. Da ace ‘yarki Muhibbat ta yi gadon wannan ƙwaƙwalwa irin taki, duk duniya ba mahalukin da ya isa ya aureta in ba ni ba.

Ba ki yi yawo a kasashen Turai a banza ba. Don haka ina jinjina miki don kumfutarki ta laptop kirar ‘SAMSUNG new modern’, ta baki  adireshin daidai da inda nake magana dake a yanzu. Na taya ki murna bisa nasara da kika samu wajen gwada basirarki a karon farkon mu’amalarmu da ke. Haka zan taya ki jaje idan nan gaba karamin basirarki ya ruɗeki kika sake aikata wannan kuskure. Saboda haka, ki kiyaye shigar da hukuma cikin kasuwancimu dake. Ki kuma sani, sake aiki da iliminki shi zai bani damar yin aiki da nawa jahilci. Basai na fada miki ba, ke kanki kin sani da ilimi da jahilci kishiyoyin juna ne. Nan da ‘yan dakikan lokaci zan turo miki da sakon adireshi da kika ɗauka a laptop naki kika tura wa hukumar DSS.

Hajiya ina baki shawara da cewa ki bi doka ki zauna lafiya. Kar ki manta 24 hours kachal kuke da shi”.

Shiru ya biyo baya sakamakon kashe waya da mai maganan yayi. ‘Tashin hankali wai gobarar gemu’ Hajiya ta furta a cikin zuciyarta.

Hankali ya sake komawa kan Muhibbat wacce a yanzu idanunta ke buɗe numfashinta na kokarin fin karfin asalin yanda ya dace ta numfasa.

Dakta Sanusi Babagana ya yi saurin mai da hankalinsa gareta.

Alat ya shiga cikin wayar Hajiya Adda Manga. A yanzu hankalinta ya kasu kashi biyu. Ɗaya na kan Muhibbat, yayin da ɗaya kuma ke nazari kan wasikar da ta shiga wayarta. Lailai idan abin da ta tura wa hukumar DSS ne kidnaper nan ya turo mata, a kwai alamomin tambaya kan jami’an tsaron ƙasar nan.

Wani a abin tambaya yaya yayi yasan halin da suke ciki a cikin asibitin? Ta yaya ya iya ganinsu har ya iya kwatanta duk abin da ta aikata? Wane ne bare daga cikin waɗan da a yau suka zo kan Muhibbat musamman idan aka ɗauke Dokta? To ko da haɗin bakinsa ne? Anya kuwa Dokta Sanusi Babagana zai sa kansa cikin cin amana mafi muni irin wannan? Idan har babu hanunsa, to akwai hannu ma’aikatansa ba tare da saninsa ba.

A yanzu zuciyarta na raya mata cewa, akwai abin da turawa ke kira ‘danger’ ga duk wani yunkuri da zata yi saɓanin umurni da kidnaper ya bata.       

*****

Awowina ɗari da goma sha ɗaya, kwanaki huɗu kenan da awowi goma sha ɗaya daidai ina garkame cikin wani gandun daji. Iya abin da zan iya sani shine, sama na sama, ƙasa na nan a ƙasa don akanta nake zaune a yanzu. Amma ban san ina kudu, ina ne arewa ba, ballantana gabas. Hakan na nufin tunda masu garkuwa da mutanen suka yi garkuwa dani ban samu damar yin sallah ba.

Karon farko kenan a zahirin rayuwata na ɗibi kwanaki har huɗu ban gana da Ubangijina ba. Kamar da shine karo na farko da aka min luguden duka da gindin bindiga. Nan take tunanin Muhibbat ya faɗo min a rai.

Allah sarki Muhibbat, matata abar sona, tauraruwa mai haskaka rayuwata. Macce ɗaya data soni, so na hakika da bana zaton a duniyar zamanina za a yi wata macce da zata soni kamar yadda ta soni. Yanzu, ko a wani hali take ciki ne ohooo…? Wata kila mun rabu kenen rabuwa na har abada.

“Malam Salahuddeen…  .” muryar wani  gabjeje ne dake tsaye a gefena ya datsemin tunanina, ya kuma cigaba.

 “Mun ba surkuwarka sekon dubu tamanin da shida da ɗari hudu daidai (86400) don ta kimtsa mana miliyan dari. A yanzu ta lashe sekon dubu talatin da tara da ɗari shida (39600) daidai, awowi goma sha ɗaya kenan suka salwanta.

Kawai saura sekon dubu arba’in da shida da dari taƙwas (46800). Kenan saura awanni goma sha uku cif-cif. Suna karewa idan ba wani labari, zan maka taimako ɗaya, zan baka takarda da biru ka rubuta wasiya zuwa ga masoyiyarka Muhibbat. Daga nan sai nayi ‘posting’ naka zuwa barza’u. Muhibbat kuma, ta maye gurbin inda kake zaune a yanzu.  Yin hakan zai sa mu gane ko surkuwar taka na da wariyar launin dangi ko a’a.  Ta yiwu , don ita uwar matarka ba lallai ne na ta aminta da kai a matsayin uwarka  ba.

Ku biyo ni a babi na biyu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Mijina Wukar Fidar Cikina 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×