Skip to content
Part 11 of 19 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Kaduna.

Karfe goma sha daya na safe agogon hannunsa ya buga. Yayi daidai da bude gate din da securities din suka yi.

Hankada hancin motarsa ciki. Bayan yayi parking ya sakko hannunsa dauke da bakin jakar hannu. Yayi kyau sosai. Cikin shigarsa ta manyan kaya yau ya sami isowa wurin shugaban qasa. Wannan karon ba can Abuja ya biyo shi ba, wanda wataran har kasar yana bari ya je wurinsa a qasar waje.

“Bismillah mu je ko?”

Suka kama hanya. Tafiya suka yi mikakkiya kafin suka iso wani katon falo. Dokto Zayyad bai zauna ba, yana nan tsaye yana kallon katon hoton shugaban qasan da wani yaro da ba zai wuce shekaru uku a duniya ba. Duk suna dariya. Sai kuma gefe daya ga wata mata a gefensa itama dariyar take yi.

Bai taba ganin hoton ba, tunda yake zuwa wurinsa. Ko da yake wannan falon ma shine karo na farko da ya shige shi.

“Rankashidade ya ce ka shigo cikin daki.”

Dokto Zayyad ya jinjina irin girman da Alhaji Mamman sadau yake bashi. Duk da kasancewarsa shugaban qasa hakan bai saka shi daukar kansa a wani abu na daban ba.

Sai da yayi sallama, ya amsa tare da bashi izinin shigowa. Sannan ya shigo. Yana kokarin tashi zaune daga kan hadadden gadonsa. Dokto Zayyad yayi saurin karasowa ya taimaka masa. Mai girma shugaban qasa ya dubi Security dinsa ya ce,

“Kana iya tafiya.”

Dokto Ya rankwafa sosai ya ce,

“Barka da wannan lokaci mai girma shugaban kasa.”

Ya jinjina kai,

“Barkanmu da juna.”

Sosai ya rike hannunsa kamar ba zai saki ba. Suka dan yi shiru, daga bisani ya kore shirun da cewa,

“Ya jikinka rankashidade.”

Ya gyara zama ya ce,

“Jiki Alhamdulillah. Na ji sauki sosai.”

Dokto ya ciro abin gwajin bp. Ya gama auna shi, sannan ya dago yana dubansa.

“Sir! Har yanzu jininka bai sauka ba. Dan Allah kayi hakuri ka cire tunanin komai, domin mu samu jinin ya sauka. Idan jininka bai sauka ba, babu yadda za ayi mu ci nasarar yi maka aikin zuciyar nan. Mun saka rana har sau uku muna dagawa saboda matsalar jinin.”

Saitin inda yake kallo shima ya kalla. Hotonsa yake kallo da yaron nan da kuma matar. Sai kuma yayi ajiyar zuciya,

“Zayyad zanyi kokari insha Allahu. Kasan duk wanda nauyin jama’a ke kansa babu yadda za ayi ya sami kwanciyar hankali. Amma insha Allahu zanyi kokari.”

Dokto ya kalleshi cike da tausayi. Wai irin wannan mutumin akeso ya kashe da hannayensa. Mutumin da ya sadaukar da komai nasa akana talakawansa. Lallai da ya aikata hakan gwara Alhaji Bako ya karar da dukkan zuri’arsu. Duka duka shekarunsa biyu akan mulki, amma komai ya sauya a qasa. Sai yanzu ya ji yana son ya ji meyasa suke son kashe shi? Me yayi masu?

“Rankashidade zan dibi jininka. Don Allah ka daure ka cire damuwar. Ka tuna cewa komai yayi farko zai yi karshe. Duk abinda ya faru da sanin Allah. Yasan zaka iya ne shiyasa ya wakilta mana kai a matsayin wakilinmu. Don Allah kada ka sare.”

Hawaye suka cika masa idanu,

“Ina jin kamar na kusa barin duniyar nan Zayyad.”

Da sauri Dokto ya dago yana dubansa. A karo na farko da ya kura masa idanu a duk shekarun da suka kwashe suna alaka. Kyakkyawan bafullatanin Yola. Wani iri ya ji a jikinsa. Zuciyarsa tana neman karyewa. Bai saba ganin babba ya karaya kamar haka ba. Bai san lokacin da ya kai hannu ya goge masa hawayen da ke sauka a fuskarsa ba.

“Rankashidade ko dai akwai wani abu da yake damunka ne banda ta al’umma.”

Yayi tambayar yana jin kamar yana shirin wuce gona da iri, na kokarin sanin sirrin shugaban qasar.

Alhaji Mamman ya yi ajiyar zuciya, yana jin wani irin sanyi, a kokacin da hannun Zayyad yakai bisa fuskarsa.

“Zayyad ina fama da damuwa da yawa. Labarin akwai tsawo. Na rasa abubuwa da yawa masu mahimmanci a cikin rayuwata. Na hadu da sharrin aminai, na hadu da sharrin matar aure. Na hadu da kaddarar haifan ‘ya’ya har biyu dukkaninsu babu mai jin magana. Abubuwa da yawa suna tabani, shiyasa jinina ya qi sauka tun bayan mutuwar matata da gudan dana da nakeso kamar in mutu. Na kasa jurewa na kasa.”

Wannan karon hawaye sosai ke sauka daga idanunsa. Hankalin Zayyad idan yayi dubu ya tashi. Ya rikice. Da sauri ya kama hannunsa yana jin kamar nasa idanun ma za su zubar da ruwa.

“Ka daina kuka. Idan ka rasa ‘ya’ya na gari nima danka ne. Kuma duniya tana alfahari da ni a matsayin yaro na gari. Dan haka ka daukeni ka sakani a cikin zuciyarka a matsayin babban danka kuma na gari.”

Cak! Ya dakata da kukan da yake yi yana duban Zayyad. Ya daga masa kai alamun tabbas haka yake nufi. Baisan lokacin da ya rungume Zayyad ba, duk suka yi shiru bugun zuciyoyinsu yana sauyawa.

“Allah yayi maka albarka Zayyad. Insha Allahu indai zaka maye mini wannan gurbin dawowar da zaka yi zaka sameni mai cikakkiyar lafiyar da za a iya yi mini aiki.”

Zayyad ya lumshe idanu, yana jin wani irin kaunarsa yana mamaye dukkan ilahirin jikinsa. Yana jin wani abu mai kama da wani babban jigo a tattare da dattijon.

Haka suka Zayyad ya dibi jininsa, sannan yayi masa allura yana son ya dan sami barci dan zuciyarsa ta huta.

Barcin kuwa ya kwashe shi, ya zauna yana duba agogo. A kalla sai da ya kwashi awa biyu yana barci. Zayyad yana nan zaune kamar mai gudun wani abu ya taba lafiyarsa.

“Zayyad kana zaune baka je ka kwanta ka huta ba?”

Yayi murmushi,

“Barka da tashi. Na je masallaci yanzu na dawo.”

Yana kokarin tashi, Zayyad ya taimaka masa.

“Nima ya kamata inyi Sallar ko?”

Ya gyada kai. Har bandakin ya raka shi, sannan ya dawo ya zauna. Haka kawai yake jin bayason rabuwa da shi. Bayan ya yi Sallar aka gaba tar masu da abinci kala-kala. Tare suka ci. Zayyad ya saki jiki da shi sosai, a sabanin baya da yake kasa sakin jiki da shi. Sosai yaga walwalar Alhaji Mamman ya karu. Ya saki jikinsa har da dariya.

Zayyad yaso tafiya, sai dai ya rokeshi yana so ya kwana, domin ya taya shi hira da wasu ‘yan shawarwari.

Shi kuma Zayyad hankalinsa yana kan Samha. Yana tsoron kada Sakina ta cutar masa da ita.

“Rankashidade yadda kace haka za ayi.”

Ya sake kafe shi da idanu,

“Zayyad daga yau ka dinga kirana da sunan da ‘ya’yana suke kirana, wato Daddy. Har Muhseen ya bar duniya Daddy yake kirana. Haka ma sauran ‘ya’yana. Mufida da Walid. Duk sun kammala karatun degree dinsu zuwa masters a London.

Zayyad ya gyada kai.

“Insha Allahu daga yau mahaifi kake a gareni.”

Suka dan cigaba da tattaunawa. Har ya ciro wayarsa yana nuna masa ‘ya’yansa. Duk da yasansu a duniyar media, amma hakan bai sa ya qi kallonsu ba.

“Muna shirin aurar da kanwarka Mufida. Zata auri yaron ministan gida.”

Anan ma jinjina kai yayi. Yanaso ya kira Samha sai dai bazai iya koda duba wayarsa ne a gaban Shugaban kasa ba.

Sai da ya tashi ya ce zai shiga bandaki ya watsa ruwa, sannan Zayyad ya saki ajiyar zuciya. Ya daga wayarsa ya kira Samha.

“Hello Samha.”

Tana kwance ta kudundune. Ba tasan ta shaku da shi ba, sai a jiya da ta kasa barci, ba tasan rashinsa a kusa da ita illa ba ce, sai da yar yanzu ba ta ganshi a gabanta ba.

“Na’um Uncle.”

Ya dan yi kasa da murya kamar mai rada,

“Na tafi na barki ko?”

Ta yi shiru idanunta suna fitar da hawaye.

“Sorry zan dawo amma sai gobe.”

Wannan karon tayi karfin halin cewa,

“Ina tsoron kwana babu kai a gidan.”

Abin ya bashi mamaki. Ya danne mamakinsa yana aikin lallashinta.

“Kiyi addu’a ki kwanta babu abinda zai sameki.”

Daga cikin wayar ya ji kara. Hakan yasa ya sake makale wayar a kunnensa yana faman kiran sunanta.

“Samha! Menene?”

Ba ta kai ga magana ba, ta tashi zaune tana kallon yadda Sakina ta hankado mata kofa tana huci. Samha ta kalleta sosai ta ce,

“Lafiya zaki shigo min babu sallama?”

Sakina ta kalleta sosai ta ce,

“Nan gidan ubanki ne? Nace gidan ubanki ne da zaki saka mini dokar shigowa?”

Samha ta ce,

“Ba gidan ubana bane, kamar yadda kema ba gidan naki uban bane. Kuma Wallahi idan baki fita ba sai nayi maki illa.”

Sakina ta saki shewa ta ce,

“To ‘yar gidan matsiyata. Yau na binciko rufaffen sirrinki. Ashe almajira ce ke ya tsinceki ya aureki. Baki da asali, sai yawon bara a titi. To Wallahi bazan zauna da mabaraciya a gidan nan ba.”

Samha ta nade hannunta tana rike da wayarta ta ce,

“To yanzu ya za ayi kenan? Tunda ba zaki iya zama da almajira ba, sai ki sakeni kawai ki huta ganina.”

Ta dubeta shekeke,

“Ko ban sakeki ba, zan saka a sakekin. Ki zuba idanu ki ga yadda wasan zai kare. Na fi ki iya makirci. Babu boka babu malam zan hada maki tuggun da sai kin bar gidan nan. Banza munafuka.”

Ta juya ta fice tana zage-zage. Ko alama Samha ba tasan Uncle Zayyad yana saurarensu ba. Ta mance ma da waya take yi. Ta karasa bakin kofarta ta datse da key. Ta koma ta jingine bayanta da kofar ta fara kuka.

“Ya Allah ka dawo mini da mahaifiyata gareni. Ya Allah ka sassauta mini kasa bawan Allahn nan ya tausaya mini ya mayar da ni wurin mahaifiyata. Rashinki babbar matsala ce Mama.”

Ta cigaba da kukanta. Hatta yadda take rera kukan Zayyad yana saurare. Kukanta yake ji tamkar wanda ake watsawa wuta. Bai ce komai ba, ya katse wayar kawai.

Haka yayi ta hira da shugaban qasa, wanda yayi mamakin yadda ya saki jiki da shi fiye da zatonsa. Bai taba zama yayi hira da wani dan adam haka ba, kamar yadda yake hira da Alhaji Mamman. Yayi mamakin har sha biyun dare suna tare. Haka zalika babu wanda ya amincewa ya shigo ya ganshi.

Bayan sun rabu ne, ya watsa ruwa, sannan ya daga waya ya kira Samha. Ga mamakinsa bugu daya ta dauka jikinta yana rawa.

“Hello uncle.”

Yadda take kiran sunansa tana qara kashe masa jiki.

“Na’am Samha. Me kike yi baki yi barci ba?”

Ta goge hawayenta ta ce,

“Babu komai.”

Ya jinjina kai,

“Kiyi hakuri gobe da safe insha Allahu, zan dawo. Ki tashi ki je kiyi alwala kiyi Sallah. Idan kina da damuwa ki sanarwa Allah shi zai yi maki maganin damuwarki.”

Ta jinjina kai.

“Insha Allahu.”

Duk suka yi shiru. Kowannensu da irin tunanin da yake yi.

“Sai da safe.”

Ba ta iya amsawa ba har ya kashe wayar. Ta numfasa sannan ta tashi ta nufi bandakin.

Washegari da misalin sha biyu, Shugaban kasa ya bar garin. Shi kuma Dokto Zayyad ya nufi hanyar Kano.

Misalin karfe uku ya shigo gidan. Sakina tana jin alamunsa ta zauna tana rusa kuka. A lokacin Samha ta fito da nufin zagayawa baya ta kunna famfo, domin tun jiya da daddare ruwa ya daina shigo mata. Tana jin tsoro yasa ba ta fito ba. Wanda Sakina ce ta kashe ta boye ta baya hannunta rike da wata katuwar muciya tana jiran ta fito ta kwada mata, ta gudu. Har ta gaji da jira ta dawo ta kwanta a falo ba ta ganta ba.

Samha tana ganinsa ta dan ja da baya cike da murnar ganinsa. Sai dai yadda fuskarsa babu fara’a yasa ta dan rabe a jikin bango tana kallon yadda Sakina take kuka.

Da sauri Sakinar ta nufo shi tana cewa,

“Alhamdulillahi.. Gwara da Allah ya kawo min kai yanzu. Jiya Samha babu irin zagin da ba ta yi mini ba. Karshe yarinyar nan ta mari fuskata, saboda tsabar ta rainani ta ganni ban kaita tsawo ba. Tunda ka hanani kai kara Walh sai ka dauki mataki akanta.”

Yadda ta takarkare tana yi, idan da bai ji komai ba, zai iya gazgatata domin ta iya acting.

Bai ce komai ba, ya nemi ya wuce su zuwa dakinsa, dan yana da bukatar hutawa. Ta sake tunkaro shi tana kuka. Waigowar da zai yi, ya wawwanketa da mari. Tsabar azaba da gigicewa yasa ta fadi kasa tana wani irin kururuwa. Ya saka hannu ya fizgota. Ya ware idanunsa akanta,

“Idan kika cigaba da matsa min zaki bar gidan nan. Kin isheni Sakina. Ban isa inyi tafiya ki bar gidan nan ya zauna lafiya ba? Duk irin cin mutuncin da kika shigo jiya kika yi mata akan kunnena. Na kirata a waya naji komai! Da kike cewa almajira ce ita, ke mecece? Almajirar ba ta fi ki komai ba? Kinsan illar zama da wanda bai mori tarbiyya ba kuwa? Munafuka kawai.”

Ya watsar da ita kamar kayan wanki, sannan ya shige dakinsa. Kunyar duniyar nan ta rufeta. Samha ta saki baki tana kallonta cike da mamaki.

“Lafiya kike kallona? Sai kinsan kin hadani fada da mijina Wallahi. Kuma kada kiyi tunanin kin ci nasara zan nuna maki kin yi kadan ki rabani da shi.”

Samha ta tabe baki ta yi ficewarta. Har ta kunna famfon ta dawo ba ta daina al’ajabin Sakina ba. Lallai matar nan ta wuce tunaninta indai a fagen makirci ne.

Sakina ta murda kofarsa da nufin shiga amma sai ta ji ta a rufe. Dole ta koma dakinta tana cizon yatsa.

Uncle Zayyad

Haka ranar ya kwana ya tashi, bai yiwa kowa magana ba, bai kuma shiga sabgarsu ba. Duk da zuciyarsa tana gaya masa bai kyauta ba, tunda babu abinda Samha ta yi masa.

Da misalin karfe tara na safiyar talata ne, ya shigo falon Sakina fuskar nan babu rahama. Wannan rana ta kasance ranar da Samha zata karbi girki.

Tana ganinshi ta yi saurin tashi zaune tana zare idanu,

“Ke zauna magana zanyi da ke.”

Bakinta yana rawa ta sake gyara zama tana yayyanka idanu.

“Waye ya gaya maki Samha almajira ce?”

Gabanta ya fadi da karfi. Bakinta na rawa ta ce,

“Wata ce ta gaya mini kawata ce.”

Ya gyara zama sosai yana sake tamke fuskarsa,

“Ina fatan wannan zai zama na karshe da maganar nan zata sake fitowa daga bakinki. Wallahi Sakina kika sake jifan Samha da irin wannan maganar zan yi matukar baki mamaki.”

Ya mike zai fice tayi saurin tashi ta rungume shi ta baya, tana shesshekan kuka,

“Kayi hakuri nima nayi nadama. Kuma insha Allahu zanje in ba ta hakuri. Fatana ka yafe min mu koma zamanmu kamar da. Wallahi inashan wahalar rashinka.”

Har cikin zuciyarsa ya yarda da kalamanta. Har ma ya juyo ya rungumeta yana shafa bayanta.

“Idan kika yi hakan zaki siyawa kanki girma a idanuna.”

Ta sake kankame shi tana cewa,

“Insha Allahu zaka sameni fiye da yadda kake zato. Zan gyara maka gidanka, zan rike girmana a matsayina na uwargidanka, kuma uwar ‘ya’yanka insha Allahu.”

Ya jinjina kai, ya kamo hannunta suka fito. Sakina har da langwabewa a jikinsa tsabar makirci. Ta kuwa ci sa’a Samha ta fito daga bangaren maigidan ga dukkan alamu gyara masa tayi. Duk da Sakina tayi mamakin yadda baya ba ta makullin dakin, amma kuma yake baiwa Samha, sai ta danne komai tana sake shige masa. Shi sam! Bai ga Samha ba, dan haka ya sake rungume Sakina da dayan hannunsa dayan kuma yana latsa waya. Samha ta ji wani abu ya dirar mata a kirji, wanda zata iya rantsuwa ba ta taba jin irinsa ba.

<< Miskilin Namiji 10Miskilin Namiji 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×