Skip to content
Part 12 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Saura kadan ya ci karo da ita, ta ja da baya. Kallonta ya yi, sai kuma yaji babu dadi. Tayi bala’in bashi tausayi. Haka ta rabasu ta wuce sashenta. Hannu biyu ta zauna tayi tagumi da su, ta rasa ma wani irin tunani zatayi. Dan haka zuciyarta ta dinga gaya mata ita ya shareta ne, saboda ba ta da gata. Ita kanta ba tasan kuka take yi ba, sai da ta ji tattausan hannunsa a fuskarta yana cewa,

“Kuka kuma? Why Samha? Me zai sakaki kuka kuma yanzu?”

Shiru ta yi masa tana sake jin haushinsa cikin zuciyarta.

Ya jawota gaba daya ya rungumeta.

“Uncle yayi maki laifi ko? Ko kishina kika fara yi ne ban sani ba? Come on. Zo ki gaya min me kika ji a zuciyarki dazu?”

Ta razana! Tabbas idan wannan ne kishi da gaske tana kishinsa kenan? Idan tana kishinsa dole tana sonsa. Da sauri ta girgiza kai ta rushe da kuka tana cewa,

“Ni dai ka kaini wurin Mamana. Kada ka bari inmutu banganta ba.”

Ya jawota suka shige cikin uwardaka. Sakina da ke labe ta yi tsalle ta dire tana murnar makircinta ya ci, ko babu komai yau Samha bazata iya barci ba. Sai dai kuma jinsu shiru ya sakata sake tura kunnuwanta, amma ba ta jin komai. Dan haka ta zagaya ta can baya, ta sake cusa kunnuwanta jikin window dinta na uwardaka.

“Zauna ki gaya min me yake damunki. Zauna mana! Kinsan banason gardama ko?”

Ahankali ta nemi wuri ta zauna a bakin gadon nata. Shima zaman yayi.

“Nuna mini ina yake yi maki ciwo.”

Ta saka hannunta a kirjinta tana jin hawayen suna karuwa. Ya kai hannu ya taba kirjin.

“Kwanta indubaki sai inbaki magani.”

Babu musu ta kwanta. Rigar da ta saka doguwar riga ce mai zip. Ya sauke zip din har kusan cikinta, duk ba ta ankara ba. Haka da iya gaskiyarta kwanciya tayi ya duba mata kirjin, tunda shi babban likita ne.

Kafe kirjinta yayi da idanunsa da suka soma rinewa. Yarinyar ta mori komai. Jinsa shiru yasa ta dan dago,

“Ka gama dubawanne?”

Girgiza kansa yayi ba tare da ya iya magana ba, domin yana furta wani abu zata gane yanayinsa ya sauya. Ya saka hannu a kirjin yana dannawa. Ta dan lumshe idanu ta ce,

“Ka danna ahankali yana min zafi.”

Ya gyada kansa,

“Sai kin cire bra dinnan sannan zan iya yi maki magani.”

Da sauri ta tashi zaune. Sai yanzu ta kula da yadda kirjinta ya fito sosai daga cikin rigar maman. Tayi saurin rufesu da tafukan hannayenta tana girgiza kai.

“A’a gaskiya bazan iya ba. Ka barshi ma kawai ya daina yi min zafin.”

Ya jawota gaba daya ta koma jikinsa suna sakin numfashi. A wannan lokacin da kyar ya iya saita kansa ya tashi kawai ya fice.

Sakina ba ta ji maganar sosai ba, amma dai ta ji Samha tana cewa zafi. Ta yi iya dogon tunaninta ba ta fahimci komai ba, hakannan ta koma bangarenta cike da takaici.

Yau dai ya saki jiki ya ci abinci sosai. Sai dai Sakina ba taga lokacin da ya ci ba, domin kamar yadda ya saba ne, a dakin Samha ya zauna ya ci sosai.

Haka ya sake hada su a falo ya ja masu kunne akan rigima. Sannan ya mike yana cewa,

“Kije ki kwanta Sakina. Ke kuma Samha mu je.”

Samha ta mike suna hada idanu ta sakar mata murmushi. Aikuwa kamar Sakina zatayi hauka a wannan daren. Wajen karfe dayan dare ta je saitin kofar ta cusa kunnuwanta domin ta ji me suke yi. A irin lokacin kuma dukkansu suna bisa darduma suna kai kukansu wurin Allah. Bayan sun idar suka yi karatun Qur’ani, sannan ya ce ta zo su kwanta.

Rungumeta kawai yayi ya jawo masu abin rufa. A haka barci yayi awon gaba da su. Sakina kuwa durkusawa tayi qasa ta kwanta sosai tana lekensu. Hakan bai yi mata ba, ta sake ficewa ta zagaya ta baya. Labulen ya dan daga. Dan haka ta samu ta leka. Ganinsu a cikin abun rufa daya yana manne da ita kamar za a saceta ya sakata cikin tashin hankali. Tasan dai da zarar ya gama abinda zai yi da ita, ko kusa da ita baya sake matsowa. Amma ga Samha nan ya gama kwanciyar da ita, ya kuma jawota jikinsa. Dole ta koma dakinta. A ranar ko da barci yake barowa, bai ci nasar dauketa ba. Haka ta kwana mugun tunani da koke-koken banza.

Washegari da sassafe ta tashi ta dawo falo ta zauna. Jin motsin Samha a kitchen yasa tayi saurin biyota.

“Samha aiki kike yi ne?”

Ta dago tana kallonta. Shiru tayi ba ta ce mata komai ba.

“Ke ki saki jikinki yanzu babu fada a tsakaninmu. Gwara mu hada kanmu mu samawa mijinmu kwanciyar hankali.”

Samha ta ja tsaki kawai, ta cigaba da abinda take yi. Sakina har zata fara kunduma ashar, sai ta hango dokto Zayyad yana tsaye yana saurarensu. Dan haka ta marairaice,

“Haba Samha. Ko dai domin abinda ya faru rannan ne? Kiyi hakuri komai ya wuce. Dan Allah ki bari mu hada kai mu yi zaman lafiya a tsakaninmu.”

Wannan karon ma Samha ba ta yi ko tari ba. A zuciyarta har yanzu mamakin mutuwar karen nan take yi. Babu yadda za ayi ta iya yarda da Sakina.

Zayyad ya karaso ya ce,

“Ke wai Samha wacce irin kafaffiya ce ke? Iyye? Don meyasa tana lallabaki ku zauna lafiya kike irin wannan wulakancin? Ba jiya na gama yi maku magana akan irin hakan ba? Look! Ni banason ciwon kai. Idan kin shirya zaman lafiya da iya fine! Idan kuma baki shirya ba..”

Ta yi saurin dagowa tana kallonsa da fararen idanunta. Maganar da ya gagareshi karasawa kenan. Shikansa yasan ya zaqe da yawa. Yarinyar da ya auro na shekaru biyu kacal! Me zai daga masa hankali da son dole sai an hada kai? Idan banda ma namiji wai yau Sakina ce abin yarda? Kallon da take yi masa yana dauke da ma’anoni da yawa, dan haka ya kasa cigaba da yi mata magana. Muryar Sakina ya ji tana cewa,

“A’a ka kyaleta kila fushi take yi, zata hakura insha Allahu. Ka dawo?”

Ya gyada kai kawai. Samha kuwa kamar kurma haka ta koma. Abinda Zayyad yayi mata yayi bala’in kona mata rai. Sai dai tayi alkawarin ba zata ce masa komai ba. Har ta gama hada masa abin karyawan ba ta fita daga kitchen din ba, kamar yadda taga Sakina tana leke. A zuciyarta tana cewa,

‘Na kusa ma indaina girki a kitchen dinnan. Matar nan makircinta ya wuce yadda ake tunani.’

Da sallama ta shigo masa da kayan karyawan. Yayi kokarin su hada idanu ta hana hakan faruwa. Ya zauna ya ci sosai, ya kora da shayin na’a na’a. Sannan ya fara shiri.

“Zan je wurin aiki. Ko akwai abinda babu a gidan?”

Kamar bazata yi magana ba, sai ta daure ta amsa da

“Akwai komai.”

Ya jinjina kai. Har suka rabu babu wata magana da ta hada su. Ta koma bangarenta ta saka key tayi barcinta sosai, sannan ta tashi ta dora girkin rana.

Tana fitowa kenan ta ji tana waya,

“Kawata zanzo ki kaini wurin malamin nan. Da farko shi nake son inyi maganinsa, amma yanzu sai na fara takan shegiyar yarinyar nan tukun. Wallahi sai na mayar da ita tamkar baiwa sannan zai sallameta shima kuma insallame shi. Eh har yau bai tuna komai ba, bai tuna mun taba zama a baya a matsayin miji da mata ba.”

Ta saki shewa. Samha ta dinga maimaita kalman sun taba zama a matsayin miji da mata.

Dan haka yana dawowa ta same shi a daki. Ta zauna sosai ta dan saki fuska.

“Ko zaka iya tunawa a can baya ka taba auren Sakina kuka yi zaman miji da mata?”

Zayyad ya dinga ganin wani irin dodanni a kwanyansa ya rike kansa da karfi. Nan da nan ya fara gumi. Da sauri ya girgiza kai yana cewa,

“Samha ban taba zama da Sakina a baya ba. Tayaya hakan zai yiwu? Nasan lokacin da na nemi aurenta aka bani. Ni da kaina na ganta nace ina so.”

Samha tayi tagumi kawai. Tasan akwai mugun kulli a tsakanin Dokto Zayyad da Sakina.

“Baka da wani aboki ne da kuka taso tun kuna yara?”

Ya dan yi shiru, daga bisani ya ce

“Abokina daya ne wanda ya sanni ciki da waje. Bayan abubuwan nan da suka sameni, naji labarin an kasheshi. Har yanzu mutuwarsa ta qi bace min. Dama kuma iyayensa ‘yan nijar ne. Shi kuma makaranta ya hadamu muka karanci abu daya, sai ya kasance kamar ‘yan biyu haka muke.”

Ya ciro hotonsa yana nuna mata. Ta kalle shi sosai.

“An kasheshi? Mutuwarsa tana da alaka da kai kenan.”

Zayyad ya dubeta kamar mai son gano wani abun.

“Mutuwar Sani tana da alaka da ni?”

Ya yi tambayar yana mikewa tsaye.

“Meyasa shi baka mance da shi ba?”

Zayyad ya dubeta sosai.

“Abbana ya kawo mini shi a matsayin babban abokina. Shi ya bani labarin alakata da shi. Daga baya kuma aka tabba tar mini an kasheshi. Dan ina yawaita yi masa wasu tambayoyi. Tabbas nasan ina da cutar mantuwa a kwakwalwata, amma wani lokacin ina mance hakan. Ina ganin kamar karya ne ban mance komai ba.”

Samha ta sake tsananta tunaninta sannan ta ce,

“Anya kuwa babban abokin naka aka nuna maka? Ko dai wani aka kawo a matsayin shi ne?”

Ya dubi kwayan idanunta kafin ya ce,

“Kina tsammanin Abba zai yi min karya ne?”

Da sauri ta girgiza kai. Sai duk suka shiru aka rasa mai karfin halin cigaba da magana. Zayyad dai dogon tunani ya shiga ya kasa samun kwakkwarar amsa daga irin tambayoyin da kwanyarsa take yi masa.

“Gobe ka kaini gidanku inaso in gaida su Umma.”

Ya jinjina kai,

“Insha Allahu.”

Washegari suka shirya tsaf! Zasu fita. Sakina ta fito fuskar nan kamar anyi gobara.

“Zaku fita ne?”

Ta kakalo murmushi. Ya daga mata kai,

“Eh. Zan kaita wurinsu Umma daga can zan wuce wurin aiki.”

Ta dan yi yaqe sannan ta ce,

“Allah ya tsareku ya kiyaye hanya. Samha ki gaida su Umma.”

Da kyar Samha ta cira kai ta dubeta, sannan ta ce,

“Za su ji.”

Suka fice abinsu. Sun iso gidan Abbansa baya nan. Shima ya tafi wurin aiki. Gidan daga Umma sai Sharifat da ke kwance tana fama da ciwon ciki.

A tsattsaye ya gaisa da Umma kasancewar yayi latti, ya wuce wurin aiki.

Samha tana nan akan gadon da Sharifat take, tana ta tunane-tunane.

“Sharifat babu wani dakin karatu ne a gidan nan? Akwai littafin da nake nema ne Walh.”

Sharifat ta danyi shiru sannan ta ce,

“Akwai dakin karatu. Amma na Abbane ya kuma hana kowa shiga, gudun kada a canza masa wurin zaman takardunsa.”

Samha ta dan jinjina kai. Ba ta sake magana ba, tunanin yadda zatayiwa Sharifat wayo kawai take yi,

“Amma idan ba zaki dade ba muje innemo maki key din, sai ki yi sauri ki duba abinda kikeson dauka kafin Abban ya dawo.”

Da sauri ta bude idanu, sai kuma ta boye zumudinta,

“Da kuwa na gode maki.”

Tana nan tsaye tana kai komo har Sharifat ta dawo tana dubanta,

“Wallahi key dinne ban gani ba. Da yake wurin yayi qura sosai andade ba a shiga ba. Amma bari insake duba dakinsa.”

Anan ma Samha ba ta daina addu’a ba.

“Yauwa Anti Samha ga shi na gani.”

Samha ta bude idanu ta karbi key din tana jin kamar lokacin warwarewar matsalar Zayyad ne ya zo.

Sharifat ta kaita har bakin kofar dakin karatun sannan ta ce mata ta shiga ita zata koma.

“Ok. Bari inyi sauri. Na gode Sharifat.”

Da sauri ta afka ciki. Takardu ne masu tarin yawa, sai kuma wasu manya-manyan files. Dakin yayi bala’in kura saboda ba a shigarsa. A hankali take dube-dube. Sai dai tarin takardun ba zasu barta har ta gane abinda ta zo nema ba.

Jin alamun motsin mutum yasa ta boye a bayan kofar. A lokacin wani file ya fado abubuwa da yawa suka zube.

Da ta daina jin motsin ta durkusa da sauri tana tarkatasu. Hotuna ta gani, sai wasu takardu. Hoto daya yafi jan hankalinta. Ta kafe hoton da idanu, daga bisani ta kwashe komai ta cusa a cikin rigarta.

Da sauri ta fito ta rufe wurin.

Sharifat har tayi barci dan haka ta kwanta kawai tana jin gabanta yana faduwa.

“Sharifat! Sharifat!!”

Ta ji ana kwala mata kira. A gigice ta farka ta fito inda take jin kiran mahaifinta.

“Waye ya shigar min dakin karatu? Nasan babu wanda zai yi min wannan karambanin idan ba ke ba. Ban hanaku shigar min wurin nan ba?”

Sharifat ta kama zare idanu, ita har ta mance ma da abinda tayi. Da sauri ta ce,

“Wallahi bani bace Abba.”

Ya zaro idanu,

“To waye idan ba ke ba?”

Ta sake girgiza kai,

“Bansan wanene bane.”

Ya wuce kawai yana cigaba da mita. Da gudu ta dawo ta ce,

“Anti kawo key dinnan in mayar da sauri.”

Samha ta mika mata cike da mamakin irin fadan da kunnuwanta suka jiyo mata Abba yana yi.

Da yamma likis Zayyad ya dawo. Suka ci abinci tukun, kafin suka tafi.

“Me kika yi a gidanmu?”

Ta dan yi shiru. Daga bisani ta lumshe idanu,

“Dan Allah ka taimakeni ka kaini ko sau daya ne inga mahaifiyata mana.”

Ya kama hannunta daya yana murzawa. Ta dago cikin kasala, sannan ta mayar da kanta qasa.

“Mahaifiyarki ba ta qasar nan. Tana can Indiya ana kulawa da ita. Nayi maki alkawarin idan komai ya lafa zan kaiki gareta da kaina.”

Ta ware idanu cikin mamaki,

“Waye ya kaita Indiya?”

Ya dan dubeta sannan ya yi ajiyar zuciya,

“Ni ne na kaita da kaina. Inaso ta sami cikakkiyar lafiya. Inason sanin alakarku da Alhaji Bako, da har yake so ya kasheta.”

Ta sunkuyar da kanta cike da farin cikin mahaifiyarta tana ganin kwararrun likitoci,

“Nagode. Allah ya saka maka da alkhairi.”

Bai amsa ba, ya cigaba da tukinsa cike da tunani.

Suna isa gida, ya wuce Masallaci domin ya sami daman yin Sallar isha’i. Ita kuma ta shige bangarenta. Suka bar Sakina da kaiwa da komowa.

Bayan ya dawo ne ya wuce dakin Sakinan.

“Sannu da zuwa.”

Ta ce da shi tana faman yaqe.

“Yauwa. Ya gidan?”

Ta yi shiru kawai. Shima ya juya yana cewa,

“Yau nayi aiki sosai, zan kwanta da wuri.”

Ta kasa hakuri ta ce,

“Haba Doktona. Idan Samha ta karbi girki ko kadan bana gane kanka. Ka yi hakuri mana ka dan zauna anan inganka mu dan yi hira sai ka tafi.”

Kamar ba zai ba ta amsa ba, sai kuma ya ce,

“Kada ki damu gobe ne zaki karbi girki. Sai yadda kika yi da ni.”

Ya fice abinsa. Aransa yana cewa,

“Shugabar masu korafi.”

Baki a sake take kallonsa har ya bacewa ganinta. Ya sami Samha ta saka kayan barcinta ta dora hijabi. Ya ce ta zo su wuce.

A dakinne Samha ta fito da hotunan da ta debo.

“Zo ka ga asalin Sani abokinka, ba wanda aka nuna maka ba.”

Da sauri ya karaso yana kallo. Jikinsa yayi wani iri. Ga hotunansu nan da Sani, tun suna ‘yan shekaru hudu a duniya. Kowanne da suna a jiki, da kuma kwanan wata. Har izuwa girmansu. Da gani aminta ce ta gaske a tsakaninsu. Ya mike tsaye da sauri yana kara kallon hoton da suka yi kowanne da lapcoat a jikinsu.

“What! To ai nasan wannan Sanin. Yana aiki a wani babban asibiti a garin nan. Munsha haduwa a wurin meeting bai taba yi min wata magana da zata nuna yasanni ba. Sau biyu na taba kama shi yana kallona, kallo mai kama da yana tausaya mini. Me yake faruwa ne? Samha na fara shiga rudu.”

Yayi maganar yana jin kamar kwanyar kansa zata fito waje. Yadda taga yana gumi ya kuma fita hayyacinsa, yana kokarin tuna wani abu, ya sanyata ta rungumeshi tsam a jikinta tana shafa bayansa,

“Uncle! Ka tsaya da tunanin da kake yi haka. Ahankali zamu samo komai.”

<< Miskilin Namiji 11Miskilin Namiji 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×