Sannu a hankali natsuwarsa ke dawowa. Ya sami natsuwar da take neman ya samu. Ya dinga sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya ci gudu. Barci ya dinga fizgarsa. Dan haka da taimakonta ya kwanta ta ja masa bargo, tare da tofe shi da addu'a.
Ita kuwa Sakina tana can a labe, jin yadda yake numfarfashi yasakata tunanin tabbas wani abu yake yi da ita. Ta zabura tana cewa,
"Ni ranar girkina sau daya yake yi min, amma ita da yake shafaffiya ce da mai da yaji, gashi can yana sake saduwa da ita. Duk inda munafunci yake mazan nan. . .