Skip to content
Part 14 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Sai yamma likis suka koma gida. Ko kadan Sakina ba tasan tare suka fita ba, ta zaci tana bangarenta. Ganinsu tare ya sosa mata zuciya sosai. Zuciyarta ta sosu. Amma sai ta dan danne,

“Kun fita ne?”

Zayyad ne kadai ya amsa, amma Samha ko kallonta ba ta yi ba. Da sauri ta dauko wani jug tana cewa,

“Bari inbaka abu mai sanyi ka jika makoshinka.”

Ya karba da nufin ya sha din. Samha ta rasa yadda za ayi ta hana shi sha, dan ganin yadda Sakina ta kafe ta tsare. Sai kawai dabara ta fado mata.

“Wayyo na shiga uku cikina.”

Cikin sauri ya ajiye cup din ba tare da yasha ba, yana jiyewa ya zube.

“Menene Samha? Cikinne?”

Ta gyada kai. Ya kamota yana mata sannu. Samha ta fakaici idanun Sakina ta sakar mata murmushi. Sakina ta juyo tana kallonta cike da mamakin yadda take yi mata murmushi har suka shige. Suna shiga suka mayar da kofa. Ta dan kwanta a kafadarsa ta ce,

“Meyasa zaka sha wannan abun? Idan ta kasheka fa? Kasan babu wanda zai hadani da Mamana sai kai.”

Murmushi kawai ya sakar mata yana jinjina karfin wayo irin na Samha.

Muje zuwa ‘yar mutan Bornonku ce.

Ya saka hannu yana shafa gefen fuskarta, har izuwa bakinta. Idanunta a lumshe tana jin wani abu yana yawo a dukkan sassan jikinta. Dan haka ta dinga lumshe idanun tana buda bakinta. Har Allah ya ba ta sa’a ta kamo yatsansa ta saka a baki tana tsotso. Ita kanta ba tasan yadda akayi ta aikata hakan ba.

Kafafunsu yana hade da na juna. Bugun kofar ya sakasu dukkansu dawowa cikin hayyacinsu. Ya dagota idanunsu duk sun yi jazir.

A hankali ya raba ta da jikinsa bayan ya sakar mata sumba akan bakinta, sannan ya bude kofar yana kallon Sakina.

“Me ya faru?”

Ya yi maganar da kyar yana aika mata mugun kallo. Ranta a tsananin bace ta ce,

“Au! Me ya faru zaka ce? Lallai Dokto. Ina ilimin addinin naka yake? Ni sakina kake yiwa haka? Akan wata banza? Yau ranar girkina ne fa don meyasa zaku shigar mini girki? Akan me? Wallahi bazan taba yarda da cin fuska irin wannan ba.”

Samha da jikinta yake a mace, ta juya da nufin fitowa ta ba ta amsa, sai dai tuni Zayyad ya kare kofar ta yadda babu yadda za ayi ta fita. Dan haka kawai ta kwantar da kanta a bayansa tana lumshe idanu. Ita kuma Sakina sai lekawa take yi tana kokarin ta hango Samhar, ba tasan tana kwance a bayan Zayyad din ba.

“Ni kike gayawa wadannan maganganun? Sau nawa ina shiga dakinki ba ranar girkinki ba? Meyasa ba ta taba yi mini korafi ba? Wallahi zan zan saba maki Sakina. Kin hanani zaman lafiya da ke da mahaifinki, kun rantse sai kun sakani a cikin masifa.”

Sakina tayi rau! rau! da idanu. A lokacin wayarsa ya dauki tsuwwa. Dokto Zayyad ya ciro wayar yana kallon mai kiran. Bai yi magana ba, haka kuma bai dauka ba, har kiran ta tsinke. Sakina kuma ba ta bar kofar dakin ba, da alama ta shiryawa duk abinda zai faru. Kiran ya sake shigowa, a natse ya dauka ba tare da ya ce komai ba.

“Wallahi ko ka kashe shugaban qasa, a wurin aikin zuciyarsa, ko kayi masa allura, ko kuma in mayar da kai zararre. Domin zan biyo maka ta hanyar da baka taba zato ba. Tunda na kula kai dai baka da rabo. Maganar kudin fansa kuma da ake so inbayar. Bazan bada ba, idan kai ka nemo mini kudaden, ka karbe kayanka. Ina sake ja maka kunne ka fita hanyar iyalina. Mahaifiyata ba taka bace, rayuwata ce ni nake da izinin zabawa kaina abinda na gadama, ba kai ba.”

A hankali ya zame wayar yana cewa,

“Allah na tuba. Allah na tuba da kuskuren bijirewa iyayena da nayi. Yau da nayi masu biyayya da ban hada wurin zama da diyar marasa tarbiyya ba. Ya Allah idan asiri akayi min Allah ka warware komai da ke kaina.”

Baki bude Sakina take kallonsa. Ranta a matukar bace

“Auren nawa kake kira da kaddara?”

Zayyad ya yi mata wani irin mugun kallo, sannan y ace

“Ba aurenki bane kadai kaddara, da ke mahaifinki ne kuka zame mani bakar kaddara. Kuna daya daga cikin bakar kaddarar da ta lalata duk wani kudirina. Amma Wallahi ba zan taba bari ku zama silar wargaza farin cikina ba, zan yi maganinku.”

“Zayyad mahaifina kake cewa zaka yi maganinsa? Mahaifina fa! Uban da ya Haifa maka matar da ka aura shi kake gayawa irin wadannan maganganun?

“Rufe min baki tun kafin in sauke bacin raina akanki. Shi mahaifin naki sarki ne? Ko ubanki ubana ne?”

Hadiye maganar da take Shirin furtawa ta yi, tana ci gaba da kukanta.

A fusace ya fice daga gidan kamar zai kifa.

Samha ta fito tana murmushi. Sakina ta dubeta sosai sannan ta ce,

“Uban wa kike yiwa dariya?”

“Uban da ya tsargu da shi nake yi. Kina ji ko? Kada ki kuskura ki ce zaki rama zagin da mijinki ya yi maki akaina. Ni ina mamakin yadda zaka dage kana makalewa namiji yana gwasaleka.”

Samha ta wuce ciki tana murmushi. Sakina ta saki baki tana kallonta, kafin ta kwafa ta dauko wayarta ta kira mahaifinta.

Shi kuwa Dokto Zayyad kai tsaye gidansu ya nufa, yana kwalawa Abbansa kira.

“Abba! Abba!!”

Gaba daya suka fito suna kallonsa cike da mamaki.

“Abba yau ina so ka gaya mini menene a tsakaninka da Alhaji Bako? Me na yi masa yake son ganin bayana? Idan akwai wani abu a boye ku sanar da ni mana, ku daina wahalar da zuciyata.”

Umma ta zaro idanu tana duban Zayyad.

“Kai Zayyad kana da hankali kuwa? Mahaifin naka kake gayawa irin wannan maganar?”

Ya dan yi shiru, sannan ya sake mayar da idanunsa kan Abba,

“Abba kai nake saurare ka gaya mini mene ne..”

Dau! Umma ta dauke shi da mari. Ya dafe kuncinsa yana dubanta.

“Ina Magana kana yi? Mahaifinka duk lalacewarsa mahaifinka ne.” Da sauri ya fice a gidan yana jin zuciyarsa tamkar zata fito waje. A ranar gaba daya haukacewa ya yi, ya kasa tsaye ya kasa zaune. A lokacin kiran waya ya shigo cikin wayarsa. Sunan shugaban kasa ya bayyana. Gabansa ya fadi da karfi. Sai da ta kusan tsinkewa ya dauka.

“Assalamu alaikum.” Sassanyar muryarsa ta kwararo sallama. Duk wata damuwa a take ta shafe daga zuciyarsa. Wani irin tarin natsuwa da tun dazu yake nemanta ya rasa, ya kawo masa ziyara.

“Daddy barka da warhaka.” Shugaban kasa ya ji wani abu yana yawo a kowane sass ana jikinsa. “Zayyad ka sanar mini da zaka zo, amma har yanzu ban ji daga gareka ba. Ya kamata ka zo ka dubani sannan a saka rana da lokacin wannan aikin. Idan Allah ya yi zan rayu to, idan kuma ba zan rayu ba, sai mu yi fatan cikawa da kyau da Imani.”

“insha Allahu zamu yi aikin nan cikin nasara.” Ya jinjina kai yana goge hawayensa. “Sau tari idan na Magana da kai, kana cire mini kewar abubuwa da yawa da na rasa su.” Zayyad ya dan juya kansa cike da damuwar yadda yake jin muryar mai girma shugaban kasa cike da rauni. Ya ce, “Daddy ka taimakeni ka kwantar da hankalinka, ta wannan hanyar ce kadai zamu iya cin nasara. Insha Allahu idan kana tare da ni, ka dauka tamkar kana tare da duk wani farin cikinka ne, na yi alkawarin zan yi iya bakin kokarina domin in baka kariya.”

Zayyad ya dage har sai da ya tabbatar da ya kwantar masa da hankali, sannan ya nufi gida. Hankalinsa ya koma kan Samha.

Yana shigowa ya sameta zaune a falo tana latsa wayarta. Gaba daya ta turara gidan da turaren kamshi mai sanyin kamshi. Gefenta ya zauna, ya dan kwantar da kansa kasan wuyarta yana shinshina. Kamshin humrar ya ratsa shi, ta yadda har ya lumshe idanu.  Ya kasa daidaita natsuwarsa sai sake shige mata yake yi, wanda hakan yasa hannunta ya fara rawa. Ta saki wayar babu shiri. Bai kyaleta ba, har sai da ya lalubo bakinsa ya hade bakinsu wuri guda. Wani abu mai kama da daukewar hankali daga gangar jiki, ya ziyarci zuciyoyinsu, wanda hakan ya taimaka wurin canza bugun numfashinsu. Hannu ya zura acikin lallausar gashin kanta yana yamutsa gashin. Ita kanta samha, Batasan lokacin da hannunta ya kai bisa habarsa ba, ta dago shi yadda ya sake samun damar kamo harshenta.

Sakina tana cikin daki, ta ji dawowarsa, ganin shiru bai shigo ba, yasa zuciyarta ta sanar da ita har yanzu fushin yake yi. Tana fitowa ta gansu a cikin yanayin da kiris! Numfashinta ya dauke. Batasan lokacin da ta yi kukan kura, ta fizgo Samha ba, sai kuwa gata a kasa. Tsananin radadi yasa Samha cewa “Wash kaina.” Zayyad ya kasa ko da daga dan yatsansa, kallon tsana kawai yake yi wa Sakina. Yaso a ce zai iya yin wani abu, da babu abin da zai hana shi tattakata. Bai an kara ba, sai gani ya yi ta dauko kwalba, ko kafin yasan abin yi, har ta bugawa Samha a kai. Gaba daya ta haukace masu. Tuni jini ya wanke mata fuska. Karar da ta saki ne, yasa ya ji wani irin karfi ya zo masa, yana tashi yad inga dauketa da mari. A gigice ya dauki Samha kamar takarda ya fice da ita.

Kai tsaye asibitinsu ya wuce da ita. Ko sauraren kowa bai yi ba, musamman nasis din da suke kokari su karbeta. Dakin tiyata ya shiga da ita, anan ya wanke ciwon, ya yi mata dressing din wurin. Allurar da yayi mata shi ya taimakata barci ya kwasheta. Tana manne a jikinsa, hakan yasa ya kara gyara mata kwanciya, sannan ya yi ajiyar zuciya. 

Ofishinsa ya dauketa ya kaita ciki, sannan ya sakawa kofarsa key. Tana kwance shi kuma yana zaune a gaban computer yana tattaunawa da wanda zai taimaka masa wurin aikin zuciyar mai girma shugaban kasa. Daga karshe ya kirawo shi a waya, suka yi ta dogon turanci, musamman na yadda za su tsara aikin ya tafi yadda ya kamata.

Bayan ya gama ne ya sauke wayar, sannan rufe computer yana duba agogo. Ya nufi masallaci ya barta anan. Bayan fitarsa ne ta farka. Ta dinga kallon ko’ina har ta gane a in da take. Ta daga kanta tana kalle-kalle, har idanunta ya hango mata wata ‘yar karamar camera. Alhaji Bako da suka gama nadar bayanan, suka kuma dauki email din Dokto Aminu, ya rike kansa yana duban yaron da ke gaban computer din.

“Yarinyar nan tana kallon camera kamar ta gane akwai wani abu a wurin.”

Ya dan yi zooming sannan shima ya shafi kansa, “Da alama ta gane, gashi tana matsowa wurin.” Alhaji Bako  furzar da huci mai zafi, “Yarinyar nan tana yawan kawo mani mishkila a ayyukana. Ya zama dole in fara yin maganinta kafin ta lalata mini aikin da na yi shekara da shekaru ina yi.”

Duk suka tsurawa computer din idanu. A lokacin Dokto Zayyad ya dawo daga masallaci rike da carbi. Ganin Samha a tsaye ya saka shi karasowa da sauri yana dubanta. “Meya sa kika tashi? Kina sane da jikinki babu kwari. Ta juyo tana kallonsa da manyan idanunta. “Akwai camera a ofis dinnan da aka dasa maka.” Ware idanunsa ya yi yana bin hannunta da kallo. Ya yi matukar tsorata, kasancewar wayar da ya yi da dokto Samir akan aikin shugaban kasa. Da sauri ya karasa ya taka tebur ya fizgo shi. Alhaji Bako ya sake dukan teburi da karfi yana jin gumi yana tsattsafo masa. Ya daga waya ya kirawo yaransa.

“Ina son gobe ku je gidan Zayyad ku dauko mini matarsa Samha.” Daga nan ya sauke wayar ya sake kiran wani. Shi kuwa Zayyad bayan ya fizge ya shiga tashin hankali. Dole ya rike hannun Samha suka fito. Babu wanda bai kalle su ba, musamman yadda ya saki hannun nata ya rungumota sosai a jikinsa, kamar za’a kwace masa ita.

Bai koma gidan ba, ba shi da bukatar sake kallon fuskar Sakina a yanzu, sannan yana so ya sami farin ciki daga Samha. Hotel ya kama aka bashi babban wuri da zai Sakata ya wala da matarsa. Kai tsaye wanka ya shiga ya yi, sannan itama ya ce ta je ta yi wankan. Ta dube shi kamar zata yi kuka.

“Bani da wasu kayan anan ka kaini gida kawai.” Ya girgiza kai tare da janyota gaba daya jikinsa, ya manna mata sumba a goshi sannan ya ce, “Ki daure ki je ki yi wankan, sai ki daura tawul tunda babu wanda zai shigo nan.”

Ta zame kanta ta shiga bandakin, duk da zuciyarta bata amince mata da shawararsa akan ta zauna da tawul din ba. Gasa jikinta ta yi da ruwan zafi, sannan ta daura tawul din, ta dauki wani tawul din ta rufe jikinta. Duk da santala-santalar kafafunta suna bayyane, hakan bai wani dameta ba, tunda ta rufe samanta. Yana latsa laptop ya dago yana kallonta. Sai ta juye masa, tamkar irin ‘ya’yan indiyawan nan masu tsananin kyau. Kafafun da take tunanin barinsu ba komai bane, ya bi da kallo, har izuwa santala-santalar cinyoyinta wadanda suke ta sheki, saboda samun hutu.

Kunyar irin kallon da yake yi mata yasa ta kasa karasowa. Janye laptop din ya yi gefe guda, sannan ya mike ya kamo hannunta. Da baya take ja, bayan ta kwace hannun, har suka dangana da jikin bango. Ya yi mata rumfa da faffadan kirjinsa, sannan ya dukar da kansa, kasancewar ya fita tsawo, ya sumbaci wuyanta, hakan ba karamin shiga jikinta ya yi ba, tana jin wani abu mai kama da so yana ratsa kowane sassa na jikinta. A hankali ya koma ya sumbaci kumatunta, sannan ya dire labbanta da suka yi pink kamar ta saka jan baki. Yana hade bakinsu ta saki sassanyar ajiyar zuciya. Mika mata harshensa ya yi, ita kuma ta karba tamkar ta sami sweet. Bata san yadda akayi ba, har ya saka hannu ya zame mata tawul din da ke daure a jikinta, dama dayan tun dazu ya zame ya fadi. Nan da nan jikinsa yak ama rawa, jin komai a hannunsa. Ya mance Samha ce fa agabansa, yarinyar da ya raina yake yi mata kallon annoba, wacce  bai taba tunanin ko hannunta zai iya rikewa ba.

Kirjinta ya yi matukar tafiya da hankalinsa.  A lokacin da ya dora bakinsa a kirjinta a lokacin ta fara kuka. Saboda karatun ya fi karfinta ba zata iya jurewa ba. Da sauri ya zame kansa yana kallonta. Idanunta a rufe suke, haka bata daina turo masa kirjin ba. Ya kafesu da kallo, yana mamakin kyawawan halittar kirji da Allah ya yi mata. Ganin har yanzu idanunta suna rufe yasa ya ce, “Bude idanunki ki daura tawul dinki.” Da sauri ta girgiza kai, sai kuma ta saka hannu ta janyo shi jikinta, ta rungume shi tsam. Shima rungumentan ya yi yana jin tattausan jikinta yana sake rikita shi. “Ni ka kaini gado barci nake ji.” Ya yi murmushi, bai dauki tawul din ba, sai daukarta da ya yi ya kaita kan gadon. A lokacin hannunsa ya dan taba mata goshi, ta saki kara tana dafe da wurin. “Ohh…Sorry Dear.” Tana jin ya kwantar da ita, ta yi sauri ta lullube jikinta. Har yanzu ta kasa bude idanun. Ficewa ya yi zuwa falo, ya kirasu a waya ya bayar da order din abincin da za su ci, yana dawowa ya sami ta koma barci. Ya shafi kansa, ya so da ta rama sallolinta tukun. Bai koma gidan ba, ya fice ya koma asibiti, sannan ya kira daya daga cikin nasis din ya aike ta ta siyo masa doguwar riga da hijabi, ya fada mata size din da yake so, sannan ya kwantar da kansa yana tunanin ta hanyar da zai iya yin maganin Alhaji Bako. Wayarsa ya zaro, sai kuma ya kalli ko ina kada ya saki jiki bai sani ba, ko ya sake saka camera din. Ya jinjina kai yana nazarin duk abin da yake faruwa, dole akwai gudumawar ma’aikatansu. Don haka ya mike a fusace ya nufi wani babban daki, wanda suke gudanar da meeting din su.

<< Miskilin Namiji 13Miskilin Namiji 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×