Skip to content
Part 15 of 21 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Ya bada umarnin a kira kowane ma’aikaci da yake on duty. Bayan duk sun taru ya furzar da huci sannan ya ce, 

“Gobe idan Allah ya kaimu ina bukatar ganin kowane ma’aikaci da yake aiki a wannan asibitin. Da misalign karfe goma sha daya na safe.”

Ya fice ya na saka waya a kunne. “Hello Dr. Samir. Sorry ko akwai wanda ya kiraka akan aikin nan da muke Shirin yi?” Dr Samir ya ce masa babu wanda ya kira shi, dole ya yi sallama da shi ya ajiye wayar ba tare da zuciyarsa ta amince ba. Bayan an kawo kayan Samha ya karba ya koma. Sai dai har yanzu barcin take yi, don haka ya dawo falo yana kallo yana cin abinci. Tunani yake yi irin hukunci da zai yiwa Sakina.

Ita kuwa Samha tana farkawa ta ga kayan da ya ajiye mata, ta dauka ta saka, sannan ta yi alwala ta zo ta gabatar da sallolinta ta zauna tana lazimi.

A falo ta same shi, duk suka dubi juna, ta yi saurin kawar da kai.

“Uncle Zayyad..” 

Ya dago yana dubanta. “Uhm ya aka yi?” 

“Ba zamu je gida bane?”

Ya girgiza kai, “Anan zamu kwana. Ina so ne ki huta sosai.”

Bata sake cewa komai ba. Sai can ta ce “Ina zargin wani abu?” Ya dago yana sake dubanta, har yanzu bata son hada idanu da shi.

“Anya kuwa su Abba suka haifeka?”

Jikinsa yana rawa ya mike ya zuba mata jajayen idanunsa. Wanda a take suka rine saboda bacin rai. “Me kika dogara da shi a wurin kawo wadannan kalaman naki? Kin kuwa san girman abin da kika fada? Maya sa kike kokarin tsallake huruminki? Ko don kin ga ina kulawa da ke shiyasa har kika sami damar warware harshenki kika bashi daman furta duk abin da kika gadama?”

Bai tsaya saurarenta ba, ya shige ciki ya yi rigingine yana jin maganarta tana yi masa yawo. Samha ta yi ajiyar zuciya, ta kuma yi masa uzuri. Domin ba kowane jarumi bane zai jure jin wadannan kalaman masu fasu fasa kwakwalwa. Tana so ta kai ziyara asibitin da Hajiya Hannatu take haihuwa. Tana so a fitar mata da file din family din. Sai dai kuma dole sai ta nemo card din su ta nan ne kadai za ta iya samun lambar file din. Idan kuwa hakanne tana da bukatar zuwa gidansu Zayyad ta yi kwanaki biyu. ‘Tayaya hakan zai kaance?’ Ta tambayi kanta tare da mikewa tana kai kawo a tsakanin katon falon. ‘Idan nace zan je gidansu Zayyad in yi kwanaki biyu, babu ko tantama zai gane akwai wani abu da nake shiryawa. Ni kuma bana so ya fahimci shirina, har sai na je na tabbatar da hujjata. To wai ma idan har ba su bane iyayensa su waye? Mene ne amfanin dakko dan da ba nasu ba, su mayar da shi dansu? Ko domin rikicewar kwakwalwata da kullum take kwana take tashi a cikin waswasi ya kamata in binciko komai.

Daga ciki kuwa Zayyad ya kasa sukuni, a zuciyarsa yana jin bai yi mata daidai ba, bai kyauta ba, ba haaka ya kamata ya yi mata ba, yana sane da irin kokarin da take yi akansa. Har karfe biyun dare Samha bata biyo shi ba, shima kuma bai biyota ba, duk dasun kasa barci. Zayyad ya mike ya nufi falon. Tana jin motsinsa ta rufe idanu alamun tana barci. Yana zuwa ya dauketa ya yi cikin daki da ita. Ya yi kokarin ya rabata da kayan jikinta, amma sai ta kudundune. A lokacin kiran wayar Sakina ya shigo. Ya dauke wayar yana kallo har ya tsinke. Ya duba wayar yaga ta yi masa kira na kusan hudu kenan. Ya so ya basar, sai ta sake kira. Yad aga ba tare da yayi Magana ba, ya saka handsfree.

Ku ci gaba da bin mu a cikin wannan kataccen labarin.

“Hello Dokto wallahi ga barayi sun shigo na shiga uku.” 

Da sauri Samha ta tashi zaune tana zazzare idanu. A lokacin kuma Zayyad ya nemi wuri ya zauna zuciyarsa tana gaya masa wani abu. Muryarsu ya ji suna cewa, 

“Ga shegiyar nan ku damkota. Wato ke kin iya liken asiri ko? Ba Samha ba, ko Samiha ce yau sai mun karairaya ki.” Tana kuka jikinta yana rawa tana cewa, 

“Ku taimakeni Wallahi bani ba ce Samha.” 

Suka kwashe da dariya, tare da tasa keyarta suka fice da ita. Zayyad ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ajiye wayar yana duban yadda Samha ta dawo kusa da shi ta makale shi jikinta yana rawa. 

“Me nayi masu suke nemana? Yau na shiga uku ka kira ‘yan sanda kada su tafi da ita.” 

Zayyad ya yi ajiyar zuciya, ya koma ya kwanta kawai yana lumshe idanu. Ta girgiza shi da karfi tana kuka, “Su waye suke nemana? Don Allah ka ceci Sakina da bata ji ba, bata gani ba.” Wannan karon hannu ya saka ya janyota ta kwanta a gefen hannunsa yana shafa bayanta.

”Dazu kin gano camera din da Alhaji Bako ya saka a ofis dina, shi  ne shi kuma ya aika a daukoki, a rashinta aka sami diyarsa, don haka babu wani dan sanda da zan dauko in tsaya batawa kaina lokaci. Na ji a jikina zai iya daukar mataki akan ki shiyasa ni kuma na kawo ki nan.” 

Jikin Samha ya yi mugun sanyi, ta dinga zazzare idanu gabanta yana dukan tara-tara. Ya sake janyota jikinsa yana shafawa. 

“Ki kwantar da hankalinki komai zai wuce kamar ba’ayi ba. Ki daina damun kanki. Ta jinjina kai. A haka barci ya kwasheta, shima kuma yana waswasi barcin ya yi awon gaba da shi. 

Karfe hudu ta tashe shi, akan su je su yi nafilfili har a kira asubahi. Bai yi mata musu ba, domin shi din ma yana da bukatar ganawa da Ubangijinsa. 

Ita kuwa Sakina idanunta a rufe da bakinta suka fice da ita. Kai tsaye wani daki suka ajiyeta a cikin gidajen Alhaji Bako, gidan da ita kanta Sakina bata taba saninsa da shi ba.

Anan ta kwana cikin wahala. Sai misalin daya na rana sannan Alhaji Bako ya zo gidan. Mamaki sosai ya yi, da har yanzu bai ji wata sanarwa akan bacewar Samha ba, uwa uba ya kira Alhaji Salisu a waya, har suka gama maganganunsu bai ji ko alama ya yi masa wata Magana ba. Don haka ya wuce gidan domin tabbatar da ko sun sameta. Yana zaune aka fito da Sakina idanunta a rufe ya yi murmushi ya ce,

“Zan kawo karshen barazanata yau. Kina ‘yar yarinyarki da ke sai kafirin wayo? Su waye iyayenki? Wallahi kafin in kasha ki sai na sauke kwadayina akanki, domin yadda kikasan matata haka zan mayar da ke, idan ya so shi Zayyad din ya zo ya kwaceki mu gani. Daya bayan daya zan yi maganinku. Ku dauketa ku kai mini ita bedroom dina yanzu in sauke gajiyata akanta.”

Suka dauketa ba tare da ya ce a kwanceta ba. Ya mike ya shiga wani wuri ya sha magungunan karfin mazansa, sai da ya tabbatar ya dauki caji, sannan ya yi kokarin shiga dakinsa wanda babu haske sosai duk an kasha fitilun. Daya daga cikin amintattun yaransa ya tsayar da shi daga bakin kofar ya ce “Yallabai mun kwance mata ido amma bamu bude mata baki ba, gudun ta yi mana ihu, kasan akwai mutane da ke kai kawo, kuma makocin gidan nan da ya tare soja ne, gidansa kewaye yake da sojoji. Alhaji Bako ya dafa shi yana jinjina kafadarsa, 

“Ka kyauta sosai.” Alhaji Bako ya shige abinsa. Tana girgiza kai tana taba shi alamun ita ce, tana kokarin yin Magana, amma hakan ya faskara. Alhaji Bako ya yayyaga mata kaya, suka yi ta kokawa akan gadon, har  Allah ya bashi ikon kwantar da ita ya haye ruwan cikinta. Sai da ya murje kirjinta yadda ransa ke so, sannan ya fara saduwa da ita, tana jinsa duk abin da yake yi, sai dai tuni jikinta y agama mutuwa tun lokacin da ta tabbatar da mahaifinta ne yake saduwa da ita. Hawaye kawai ke zuba daga idanunta. Yi yake yana zaginta yana cewa, 

‘Ashe ma ba wani dadi gareki ba. Wallahi da a ce haka kawai ne da tuni na dagaki, amma ko domin in kuntata maki a rashin dadin naki zan dinga saduwa da ke sau biyar a rana. Ko yanzu din ma sai mun share awa uku a haka. Tana jinsa yadda yake saduwa da ita, ko motsi da hannunta ta kasa yi. Tun tana fahimtarsa har bakin ciki ya sa ta suma. Sai da ya tabbatar da yayi mata mumumunan rauni, sannan ya tashi yana ajiyar zuciya. Duk ya yi zufa. Sakina kuwa yana tashi a jikinta idanunta suka bude, sun yi mata nauyi girgiza kai kawai take yi. 

Alhaji Bako yana tashi ya kunna wutan dakin, tuni dakin ya gauraya da haske, sannan ya nufi bandaki ba tare da ya kalleta ba. Ruwa ya watsa sannan ya fito hakannan tsirara. A lokacin idanunsa ya hango masa Sakina cikin bargo tana kuka. Da sauri ya karyata kansa, ya yi sauri ya karasa ya cire mata tsumman da aka rufe mata baki da shi. Da sauri ya gwale idanu. A lokacin ta rushe da kuka tana cewa, 

“Abba ka cuceni ka cuci rayuwata. Kai da kanka ka haike mini? Kai mahaifina…” Ta ci gaba da kukanta. Alhaji Bako yana zaune kamar ruwa ya ci shi, ya girgiza da wannan abun. Tun a wannan lokacin ya kamata ya koma ga Allah ya gane wannan ma wata izna ce, sai dai kuma shaidan ya ci gaba da yi masa fiitsari a tsakiyar kai. Huci kawai yake yi  yana ganin kamar Zayyad ne ya shirya masa wannan tuggun. Ya kasa Magana, sai ma yadda abubuwan da suka faru a tsakaninsa da Sakina suka dinga dawo masa. Idan ba ishara ba, ya kamata ya gane bambanci Samha da Sakina, domin Sakina gajera ce Samha kuma doguwa. Sakina bata da jiki, Samha kuma tana da kugu. Duk suka yi shiru, idan banda sautin kukan Sakina babu abin da yake tashi a dakin. A fusace ya mike zai fita, muryarta cikin kuka ta dakatar da shi.

“Kasa su mayar da ni gidana.” 

Sosai yake jin kunyar ‘yar tasa, yana fita ya rufe su da fada, 

“Wannan ce Samhar da nace ku dauko? Ku wasu irin mahaukata ne? Kawai kuna shiga daga kun ga mace sai ku daukota? Ya tabbata duk yawanku na banza ne.”

Ya basu umarnin  su mayar da ita ya fice yana huci. Kiran wayar da abokinsa ya yi masa ne ya dan saka shi jin sanyi a zuciyarsa. Ya tabbatar masa da sun sami Dokto Salim, ya kuma gaya masu ya amince dari bisa dari, zai kasha shugaban kasa ayayin gabatar da aikin zuciyarsa. Shi kuma Zayyad ya shiga damuwa, musamman yadda Samha ta ce masa ita bazata koma gidansa ba, in dai zai yi tafiya zuwa Kadunan nan kawai ya kaita gidansu ta zauna a can. Bai san meyasa ba, baya son barinta a gidan iyayensa, yasan hatsabibanci irin na Alhaji Bako zai iya aikawa a saceta. 

   Da ita ya taho ofis, ya barta a ciki tana ta kalle-kallenta, shi kuma ya wuce meeting. Kowa ya hallara, shi kadai ake jira. Bai zauna ba, sai kaiwa yake yana komowa,

“Abin da yasa nace ku zo nan, saboda yadda wani a cikinku yake bayar da hadin kai, ake bude mini kofa da master key har a ci nasarar nadar wasu mihimman sirrikana. To Wallahi! Muddin na kama ko waye zan dauki mummunan mataki, bayan n araba ko waye da aikinsa. Kuma daga yau zan saka kwakkwaran tsaro, irin wanda a kwana daya zan iya kama ko waye. Wannan kiran da na yi maku tamkar gargadi ne da kuma jan kunne, sake aikatashi kuma ganganci ne. Na sallame ku.” 

Duk suka tashi kowannensu da irin abin da yake cewa. Da yawa suna fatan Allah ya tona asirin ko waye, wasu kuma mamakin karfin halin wanda yake aikata hakan suke yi.

Ya dawo ofis din ya sameta rike da jarida, tana zaune a kujerarsa. Yadda ta dago ta yi bala’in yi masa kyau.

“yau ke ce likitan kenan?” Ta gyada masa kai. Ya miko mata hannu ta kama, gaba daya ya janyota ta fada jikinsa ya rungumeta yana Magana a hankali.

“Meya sa zaki ce gidanmu zaki je? Ki yi hakuri ki zauna agidana mana, ba zan wuce kwanaki biyu zuwa uku ba insha Allahu. Daga kaduna zan wuce  Abuja,a can zamu yi masa aikin, tunda yana da tsattsauran ra’ayi, ya ce shi ba zai fita kasan waje ba. Ki daure ki zauna a gida kin ji?”

Ta makale  kafada alamun a’a

Dole suka wuce gidansa domin ta kwaso kayanta. Suna shiga suka sami Sakina ta yi kuka har ta ji babu dadi. Idanunta sun kumbura saboda azaban kuka. Samha ta zabga mata harara, a zuciyarta kuma tana mamakin yadda akayi har Zayyad ya gano Shirin Alhaji Bako. Kayanta ta hada akwati guda, sannan ta zauna tana jiransa.

Bai ko kalli in da Sakina take ba, yana kokarin shiga dakinsa ta yi saurin shan gabansa. 

“Wani irin kiyayya ce kake yi mini haka? In gaya maka ga barayi sun shigo amma ko cigiyata baka yi ba? Hasalima ko dawowa gidan ka zo ka ga me ke faruwa duk baka yi ba Dokto? Wani irin abu ne wannan don Allah? Idan Samha ce…”

   Da sauri ya dakatar da ita. “Dakata don Allah. Waye zai saceki idan ba mahaifinki ba? Nasan kina cikin koshin lafiya neman me zan yi maki? Kisan Allah? Muddin kika ce zaki dinga damuna ni zan yi maganinki.”

Ya shige tare da mayar da kofarsa ya rufe. Samha ta fito tana janye da akwati. Suka yiwa juna kallon banza. Sannan ta kalli goshin Samha ta yi dariyar mugunta. Samha ta shafi kanta itama tana murmushi. 

“Kin za ci kin fasawa banza kai ko? Babu wanda ya taba nuna mini yatsa ban karya ba, ki zauna ki jira dawowana insha Allahu sai na fitar maki da jini.”

Sakina ta mike kamar tana jiranta.

“Idan kinsan mahaukaciyar uwarki ce ta haifeki don Allah zo ki rama, na dakeki na daki banza..”

Samha ta yi kukan kura, ta dauko wata kalba wanda aka saka fulawa, ta maka mata a kai. Bata kyaleta ba, ta sake maka mata. Wani irin jiri ya kwasheta ta zube a kasa. Zayyad ya fito yana Salati.

“Meyasa zaki kwala mata wannan abun? Wato kema baki da hakuri ko? Akan me zaki kwala mata? Idan ta mutu ya zaki yi?”

Ta dago tana dubansa. 

“Ni da ta kwala min kana nufin ni ba mutum ba ce? Ko kuwa sunan uwata da ta ambata a matsayin mahaukaciya zan kyaleta ne? Wallahi..”

Ya mike kamar zai daketa. 

“Shut Up! Ki yi min shiru tun kafin in sauke fushina akanki. Haka zaku zauna kamar karnuka? Kullum kuna yi mini masifa a cikin gida? Ke da kika zo yi min aiki ina ruwanki da wata kishiya? Kishin me kike yi akanta?” Jikinsa yayi sanyi saboda irin kallon da take yi masa. Shi kansa bai san bakinsa ya subuce ba. Da gudu ta koma daki, ta dauko masa takardar yarjejeniyarsu ta yayyaga ta watsar a wurin,

“Yanzu yarjejeniya ta kare ko? Ka dawo mini da mahaifiyata ka fita hanyata. Ni na taba gaya maka ina kishi akanka ne? Ko na taba jawoka da karfi nace dole sai mun yi auren yarjejeniya? Na tsani yarjejeniyar nan, yau gashi banda cin mutuncin iyayena har gori kake yi mini. Idan bata tabani ba, me zai sa in tabata? Ta kira mahaifiyata ta mahaukaciya in zuba mata idanu saboda wata takardar yarjejeniya? Idan baka dawo mini da mahaifiyata ba, Wallahi sai kotu ta rabani da ni da kai. Igiyar aure kuma, ko ka sakeni ko baka sakeni ba, aure tsakaninmu ya rabu. Ta juya da gudu zata fice, ya kasa ko motsi har ta fice. Runtse idanunsa ya yi yana jin gabansa yana faduwa. Ga Sakina a kwance babu numfashi, ga jini yana zuba, ga kuma yarinyar da ta gama mamaye cikin zuciyarsa ta gudu ta barshi a daidai lokacin da yake da bukatarta. Dole ya tsaya ya ba Sakina taimakon gaggawa. Wurin ta sami mummunan raunin da sai da ya yi mata dinki. Ya bata magunguna ta kwanta tana jin azaba, domin ko zafin bai kashe mata ba. 

“Idan kika ji sauki ki wuce gidanku ki rufe  mini kofa ki ba mai gadi key. Idan kuma kika bari na dawo na sameki Wallahi kiyi kuka da kanki.” Ya fice yana jin damuwa tana sake lullube shi. Duk inda yasan zai iya samun Samha ya duba bai ganta ba, hatta gidan Dokto Rahama ya je babu ita. Ya yi ta kiran wayarta a kashe. 

Bai yi tunanin zuwa gidansu ba, ya wuce kawai. Bayan ya isa Kaduna ya sake kiran lambarta a kunne amma ta ki ta dauka.

<< Miskilin Namiji 14Miskilin Namiji 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×