Skip to content
Part 17 of 21 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Akan kantan ta tsaya gabanta yana faduwa. Dama kuma ta dibo kudade irin wanda Dokto ke ajiye mata. Mai bayar da katin ya kalleta ya kuma kallon katin, yana mamaki. “Hajiya ai wannan katin ba lallai a iya gano file din cikn sauki ba, domin an kwashe su an kai wani dakin ajiye tsofaffin files.”

“Ka kai shekaru nawa kana aiki anan?”

Ya dan yi shiru, daga bisani ya ce, “Ba zan wuce shekaru goma ba.”

Ta jinjiina kai, 

“Ko kasan Dokto Rose Abraham da ta dade tana aiki anan?”

Fuskarsa ta nuna kosawa da tambayoyinta.

“Hajiya nima labarinta na ji, saboda kwarewarta a aiki, amma ban yi zamani da ita ba gaskiya.

Samha ta bude Jakarta ta ciro rafan ‘yan dubu daidai ta mika masa.

“Karbi wannan kayi mini wani aiki.”

Jikinsa yana rawa ya waiwaiga sannan ya an she kudin yana washe baki.

‘Hajiya me kike so?”

“So nake yi ka kawo mini files din da ke dauke da wannan lambar, sannan ka nemo mini lambar Dr Rose da kuma adireshinta.”

“An gama Hajiya. Bari innemo wacce zata tsaya anan yanzu zan cika maki aikinki.”

Samha ta koma ta zauna gabanta yana faduwa, addu’a kawai take yi Allah ya taimaketa ya rufa mata asiri. Ta kasa zaman, sai kaiwa take tana komowa.

Sakina ta gani ta shigo asibitin ita kadai, hakan ya bata mamaki. Da sauri ta koma ta boye tare da rufe fuskarta. Yadda take sauri-sauri tana hardewa yasa ta bi bayanta. Wani ofishi ta shiga, sai da ta waiga sosai sannan ta shige. Samha ta zagaya ta bayan window din iskan labulen ya daga, ta ga Sakina cikin kuka tana Magana. Hakan yasa ta saka kunnenta sosai, sai kuma tunani ya zo mata, ta ciro wayarta ta danna video tana nadar komai.

“dokto ka taimakeni ina cikin tashin hankali.”

“Hajiya Sakina ki kwantar da hankalinki ki gaya mini, shiyasa na kawoki nan, saboda babu wanda zai shigo wurin nan. Me ya faru?”

Ta sharce hawayenta,

“Mahaifina ya kwanta da ni, duk a zatonsa amaryata ce, ya aika a dauko masa amaryata yana son ya wulakantata sai aka sami akasi ta fita da maigidan, ni kuma ya kwanta da ni a cikin duhu bai san ni ce ba, bakina a rufe. Kuma ina da tabbacin mahaifina yana dauke da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato h.i.v  ina son maganar nan ta zama sirri a tsakaninmu. Ya ji mini ciwo, bana son mijina yasan wannan maganar, shiyasa na zo nan domin ka dubani ka gani ko ina dauke da cutar.”

Dokto ya dan yi shiru daga nan ya mike ya dauko wani dan tsinke yana cewa,

“Abu bai yi dadi ba, zan iya gwadaki ki ga babu, saboda lamarin bai dade da faruwa ba, idan muka ga babu sai ki dawo bayan watanni uku a sake gwadaki. Haba kema kinsan b azan gayawa kowa ba, mun dade muna abubuwan sirri baki taba jinsa a waje ba.”

Samha da wani irin jiri ya kwaheta Batasan lokacin da ta koma ta zauna ba. Kasancewar ta baya ne ba kowa ke zuwa wuraren ba. Da sauri ta koma ta sake labewa. Dokto din ya yi ajiyar zuciya bayan ya gama dubata.

“Kina dauke da cutar. Nayi mamakin yadda ya yi saurin bayyana kansa. Amma duk da haka kada ki damu, akwai magungunan da zaki dinga sha, babu wanda zai san kina da shi. Sai dai kuma ya zaki yi da maigidanki?”

Ta girgiza kai,

“Ai dama na fada, sai mun mutu mu uku. Don haka zan kyaleshi ya kwasa, shi kuma ya sakawa tsinanniyar.”

Sai kuma ta saka kuka mai tsuma zuciya.

“Wallahi Abba ka cuceni ka cuci rayuwata.”

Dokto din dai ya ci gaba da lallabata. Abin mamaki da al’ajabi sai y afara lalubarta yana shafa kirjinta. Samha ta ware idanu. Sakina ta ce,

“yanzu me zaka yi da ni dokto? Ni da nake dauke da cuta a jikina.”

Ya yi murmushi irin nasu na ‘yan duniya.

“Kada ki damu, ina da robar kariya, babu abin da zai sameni.”

Idanun Samha sun gaza karasa kallon kazantarsu, don haka ta yi saving din video din. 

Ciki ta koma jikinta yana rawa. Mai bada katin ta samu yana washe baki. 

“Hajiya gasu an samu, dukka. Amma fa nasha wuya sosai, baki ga duk na yi gumi ba?”

Jikin Samha a sanyaye ta ce, 

“Na gode. Gobe zan dawo maka da files din zan kara maka kudi insha Allahu.”

Ya yi mata godiya ta juya da sauri ta bar wurin. Tana isa gida ta fashe da kuka, tausayin Zayyad ya tsirga mata. Bata san lokacin da ta daga waya ta kirawo shi ba. A lokacin suna tsaka da tattaunawa da likitoci, duk baya fahimtarsu. Yana ganin kiranta ya fice da sauri,

“Kina lafiya?”

Ta yi kokarin shanye kukanta.

“Lafiya lau. An yi aikin?”

“Na kasa yi. Saboda bansan halin da kike ba.”

“Kayi aikinka, ina yi maka fatan nasara. Allah yaba mai girma shugaban kasa lafiya.”

Ya ji dadin addu’arta sosai, ya kuma sami karfin guiwar da ya rasa tun isowarsa Abuja.

“Amma sai na ji kamar muryarki tana rawa.”

“Babu komai barci na tashi.”

Suka yi sallama akan zai kirata anjima.  Da sauri ta bude files din. Hankalinta ya kara tashi, ganin akwai komai na Zayyad a cikin file din. Ta jinjina kai, tabbas akwai wani abu a kasa, ya zama dole a ce wadannan abubuwan kirkirarsu aka yi. Wani abu da ya ja hankalinta yadda aka rubuta shekarun Zayyad, ya zo daidai da na kaninsa Nura. Ta ware idanu tana kallo. 

“Tayaya hakan zai faru? Dama su ‘yan biyu ne? No.. Ko a fuska ka kalli Zayyad kasan ya girmi Nura.”

Da sauri ta dauki lambar Dr Rose ta kirawota.

“Da wa nake Magana?”

“Ni ‘yar jarida ce, mun ci karo da gudumawar da kika ba kasa, a lokacin da kike gudanar da aikinki. Shi ne muke neman izinin zuwa gidanki domin mu tattauna da ke.”

Ta jinjina kai.

“Ina maraba da ku.”

Samha ta ajiye wayar, ba zata iya bari sai gobe ba, haka kuma ba zata kwana a cikin gidan nan ita kadai ba, domin lamarin Alhaji Bako ya wuce tunaninta. Ta firgita da jin abubuwan da suke faruwa da Sakina. 

Taxi ta sake dauka, ta dinga bin kwatance har Allah ya kawota kofar gidan.

Tsohon gini ne, irin ginin da wanda yasha wuya. Gidan akwai bene, shima benen irin na da. Ta sauka tare da sallamar mai taxi din.

Ta dade tsaye a kofar gidan, da take da tabbacin nan ne gidan Dokto Rose. Wani matashin yaro ya bude yana kare mata kallo. 

“Nan ne gidan Dokto Rose?”

Sosai yake kallonta da alamun tambaya a fuskarsa, kasancewar ta sanya face mask. 

“Eh gidanta ne. Waye zan ce mata?”

Ta yi murmushi tare da cire facemask din.

“kace mata ‘yar jaridar da suka yi waya ne.”

Ya juya ya bar Samha tsaye tana tunanin jaki. Can ya dawo ya ce ta shigo. Falon babu laifi a tsaftace yake, sai dai kujerun duk sun ji jiki. Kallon kallo aka shiga yi a tsakanin Samha da Dokto Rose. Ta tsufa sosai.

Har kasa Samha ta durkusa ta gaidata. Matar mai fara’a ta amsa tana ci gaba da kallon Samha.

“Ni ba ‘yar jarida ba ce.”

Nan da nan fuskar Dokto Rose ta sauya. Samha ta yi murmushi. A lokacin da wannan yaron ya sake fitowa yana kallonta.

“Ki bani kudi in siya sabulu zan yi wanki.”

Samha ta kafesu da ido, musamman yadda Dokto Rose take kokarin neman kudin kamar wacce dama ta ajiye. Samha ta gama fahimtar babu kudin da zata ba yaron, don haka ta ciro dubu goma ta mika masa. Da sauri ya karba, dokto Rose ta shiga zuba godiya babu kakkautawa. 

Samha ta gyara zama bayan ta tabbatar da yaron ya fice yana murna.

“Ke ce Dokto din gidan Alhaji Salisu ko?”

Da sauri ta dago tana zazzare idanu.

“Eh ni ce, amma bansan komai akan gidan ba.”

“Dokto ki kwantar da hankalinki, ni taimakonki zan yi. Na gani ke kika karbi haihuwar Mukhtar Zayyad, da Nura, sai dai abin da ya sakani a duhu yadda katin shaidar haihuwar Nura, ta zo daidai da ta Zayyad ko ‘yan biyu ne?”

Dokto Rose ta yunkura da kyar ta mike jikinta yana rawa.

“Ina zuwa bari in kawo maki ruwa.”

Ta damki wayarta ta yi taku daya biyu ana ukunne Samha ta dakatar da ita, sannan ta mike ta biyota in da take tsaye.

“Idan kika ce zaki kira Alhaji Bako ko Alhaji Salisu, Wallahi zuwa anjima za su kashe ki. Duk in da kika je domin  ki buya babu ko shakka sai sun tsamoki. Gwara ki tsaya mu yi maganarmu ba tare da kowa yasan cewa ke ce kika sanar mini da komai ba. Dawo ki gaya mini Zayyad yaron waye? Meyasa kuma su Alhaji Salisu suka raba shi da iyayensa? Kada ki damu, maganar nan da zamu yi ba zan taba bari asan cewa ke ce kika gaya mini ba.”

Dokto Rose ta fara kuka.

“Zan gaya maki iya abin da na sani. Bansan Zayyad ko yaron waye ba, ina aiki watarana, aka ce an sace wani yaro, sanadin da Baban yaron ya sa aka rufe asibitinmu kenan.. A lokacin Alhaji Salisu ya sakani, in yi dabara in shiga asibitinmu in kirkiri katin haihuwar Zayyad, ni kuma sai nayi kuskure na kwafe na Nura. Amma tabbas ba su suka haifi Zayyad ba. Kuma ya dan yi girma a lokacin da suka samo shi.”

Samha ta saki zazzafar ajiyar zuciya. Har yanzu dai bata sami dalilin da yasa suka aikata hakan ba. 

Ta ciro kudaden da ita kanta Batasan ko nawa bane, ta mika mata.

“Idan kika yi shiru kin tsira.”

Dokto rose ta bita da kallo har ta bacewa ganinta. Da sauri Samha ta shiga taxi, kai tsaye gidan Dr. Rahama ta nufa.

Suka rungume juna suna murna, sannan ta cire abayanta ta shiga bandaki. Bayan sun idar da Sallah ne, suka zauna a tsakiyar gado, Samha ta gaya mata komai, ta kunna mata dukka recording din. Dr. Rahama ta cika da mamakin yadda Samha take da kafirin wayo har haka. 

“Samha! Baki tsoro? Kinsan mutanan nan idan suka ganoki zaki sha wahala fa.”

“Anti tsoron me zan ji? Duniyar nan fa abu biyu ne, rayuwa ko mutuwa. Babu abinda za a fasa a cikin abubuwa biyun nan. Wallahi Anti tunda ya ce mini ya kai mahaifiyata india, ni kuma na ji a cikin raina zan iya tsayawa in kare shi daga sharrin su Alhaji Bako.”

“Kin kyauta sosai. Haka ake son mutum.”

Daga nan suka yi ta hira har suka raba dare. Tana kallon kiran Zayyad amma sai ta kashe batason ya gane ta huce gaba daya.

***  ***

Yau litinin, a yau ne kuma za ayiwa shugaban kasa aikin zuciya. Dukkaninsu suna sanye da kayan shiga tiyata, a wani babban asibiti dake Abuja. Kafin ayi masa allura, Shugaban kasa yayi masa alama da yana son Magana da shi. Zayyad ya dubi likitocin ya ce,

“Ku bamu wuri.”

Suna fita ya rike hannun Zayyad sosai sannan ya ce,

“Idan na mutu, ka taimaka mini, ka nemo min dana da kuma matata da na rasa su a tsawon shekaru ashirin da bakwai. Dana yana da shekaru uku a duniya, wasu maciya amana suka sace mini shi.” Ya dan karkace ya dauko masa hotuna ya damka masa.

Zayyad ya girgiza kai, ya saka hotunan a cikin aljihu.

“Insha Allahu zaka hadu da su da ranka da lafiyarka.”

Kiran waya ya shigo, ya manta shaf ya shigo da wayarsa. Ganin Samha yasa ya dauka.

“Ina yi maku fatan nasara a wannan aikin.”

Wani karfin guiwa ne ya zo masa, cikin gaggawa ya amsa da “Ameen.”

Daga nan ya sauke wayar yana yi masa kalaman lallashi, ya juye masa ruwan allurer. Nan da nan barci ya yi awon gaba da shi. Da Sauri ya kirawo likitocin, suka dukufa akansa.

A kalla sun kwashe awa hudu suna aikin, kafin cikin ikon Allah suka kammala. Bayan an kaishi daki na musamman, Zayyad ya ki amincewa kowa ya zauna akansa, shi kadai ke tsaye akansa. Hatta iyalansa babu wanda aka yiwa izinin shiga wurinsa. Zayyad ya mike domin zagayawa ta baya ya amsa waya. A lokacin Dr. Salim ya sami daman shigowa, hannunsa dauke da allurar goba.  Wanda ya karbi makudan kudade a hannun su Alhaji Bako. Duk da Alhaji Bakon bai yi Magana da shi ido da ido ba, ta hannun wani suka bi, haka shima bai yarda ya zauna da Salim ba, Magana suka yi ta waya, aka ajiye masa jakar kudi a wurin bishiya, suka kwatanta masa ya je ya dauka, akan idan ya kammala aiki za a ajiye masa sauran kudin.

Salim ya zuko ruwan guban a gurguje yana sauri zai zuba, har ya kama ledar ruwan, ya ji an rike masa hannu. Kallon kallo suka yi da Zayyad, nan da nan hannunsa ya fara rawa, a lokacin kuma Shugaban kasa ya farfado.

“Ka za ci zaka iya cutar da shi ne? Kayi kuskure. Muddin ina numfashi, ba zan taba barin ko kuda ya keta ta gabansa ba. Tun ranar da na yi waya da kai a ofis dina, hankalina ya gaza kwanciya da kai. Naso in cire sunanka a cikin wadanda za su yi aikin nan, sai kuma naga idan na yi maka hakan ban kyauta ba, tunda bansan zuciyarka ko tana da kyau ba. Kaso ne ka zuba masa guba   ni kuma ka sakani a matsala ko? Ka so ne a daureni a ce na cutar da shugaban kasa ko? Idan da irinku a duniyar nan yaushe kasa zata zauna lafiya? Da ka cutar mini da shi, da sai na rabaka da numfashinka, bas ai na jira an yi shari’a da kai ba. Ofisa ku shigo.”

Nan da nan yaga an kewaye shi da bindigu. Salim ya durkusa yana kuka yana rokarsu, babu wanda ya kalle shi, karshe ma suka rufe shi da duka, suka jawo shi kamar akuya suka fice da shi. Da sauri Zayyad ya karaso kusa da Alhaji Mamman ya kama hannunsa, tare da kai kunnensa daidai bakinsa, domin ya fahimci Magana yake son yi.

“Allah ya yi maka albarka.”

Zayyad ya kasa amsawa sai hannunsa da ya rike sosai, kamar wani zai kwace. Yana kallonsa ya koma barcin, sannan ya yi ajiyar zuciya.

A can kuwa Samha ta kasa tsaye ta kasa zaune. Mutum daya take hari yanzu, wato Sani. Don haka yau ta shirya tsaf! Ta nufi asibitin da aka tabbatar mata anan yake. Ta yi mamakin da yana hangota ya yi sauri zai canza hanya. Da gudu ta sha gabansa tana dubansa.

“Bawan Allah ka taimakeni mu je wurin Zayyad. “ Sosai ya kafeta da idanunsa, daga bisani ya juya ya ci gaba da tafiya.

“Zayyad zai mutu ka taimakeni ka zo ka duba shi.”

Cak ya tsaya, sai kuma ya dawo da sauri yana zare idanu.

“Me ya sami dan’uwana Zayyad?”

“Ka zo mu je yana can kwance bai san in da kansa yake ba.”

Da sauri ya bi bayanta, ba tare da dogon tunani ba. A motarsa suka tafi. Kai tsaye gidan Anti Rahama ta kaishi. Sai da ya shiga, sannan kuma ya dago yana dubanta.

“Kayi hakuri ka zauna.”

Ya girgiza kai,

“Kin kafa mini tarko kuma na afka. Ki gaya min me kike nema da ni?”

Ya tsaya yana dubanta duba na mamaki.

“Ka taimakeni ka gaya mini rayuwar mijina ta baya. Ka taimakeni.”

Ta saka kuka. Zuciyar Sani ta dade da karyewa sai dai bayason Samha ta fahimci hakan har ta ci galaba akansa. Yana sane da bayyana komai tamkar wasa yake da rayuwarsa da kuma ta iyalansa. Ya girgiza kai ya kara takun tafiyarsa.

“Idan baka taimaki abokinka na tun yarinta ba, zaka yi danasani. Domin kuwa rayuwarsa tana cikin hatsari. Idan a baya ka jure ganinsa a cikin matsala, bana jin a yanzu zaka iya jurewa in dai da gaske kai dinne babban amininsa.”

Da sauri ya sake waiwayowa yana kallon Samha.

“Ki taimakeni ki fita a rayuwata. Idan Alhaji Bako yasan da wadannan abubuwan da kike yi, babu ko shakka sai ya yi ajalinki.”

<< Miskilin Namiji 16Miskilin Namiji 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×