Skip to content
Part 21 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Gabadaya dakin kowa ya dauke wuta. Sai aka hau kallon-kallo. Yadda Abba ya sunkuyar da kai kadai ya isa ya nuna maka maganar Alhaji Bala da gaske ne ba karya ba. Nura ya dubi mahaifinsa sosai, sannan ya matso daf da shi,

“Wai da gaske ne Abba?”

Gani suka yi ya goce da kuka. Lamarin da ya karasa sanyaya guiwowinsu kenan. Umma kuma ta dukar da kai tana jin kamar kasa ta tsage kawai ta shige.

Alhaji Bala ya fice cike da tashin hankali.

Samha ta taimakawa Zayyad ya yi wanka, sannu a hankali yake jin tashin hankalinsa yana raguwa. Bayan ya kimtsa ya koma asibitinsu, saboda aikin gaggawa da aka kira shi.

Sai da ya yi Sallah raka’a biyu kafin ya shiga aikin.

Wani babban mutum ne, za su yi masa dashen hanji, kasancewar typhoid ta lalata masa hanjinsa.

Haka kawai yake jin faduwan gaba, don haka ya dinga kiran sunayen Allah kyawawa a zuciyarsa.

Bayan sun kammala aikinne, daya daga cikin ma’aikacinsu ya fara kici-kicin mayarwa mara lafiyan ruwa.

Tun shigarsa yake kula da motsin likitan, ya kasa yarda da shi.

“Dakata!”

Ya dakatar da shi da wata murya mai tsananin kaifi. Jikin Dakta Sa’id ya nemi ya fara rawa.

Zayyad ya karaso ya cire ruwan, sannan ya mikawa wata nurse ya ce maza aje akai dakin gwaji a gwada ruwan nan ko baya dauke da guba.

Jin hakan yasa Dokto Sa’id ya fara kumfar baki.

“Akan me zai sa ka ce a je a gwada ruwan? Ko dai baka yarda da ni bane? Na taba cutar da wani ne?”

Zayyad ya yi masa murmushi sannan ya dafa kafadarsa,

“Bincikena ne kadai zai iya baka amsoshin tambayoyinka.”

Ya dubi sauran ya ce masu,

“Ku kai shi dakin hutu gani nan zuwa.”

Yana nan tsaye har aka fita da shi. Da kansa ya dauko wani ruwan ya saka masa. Da key ya rufe kofar bayan ya bar matarsa akansa.

Ita din ma sai da ya tabbatar mata muddin wani abu ya sami mijinta ita zai kama.

Har ya fita matar ba ta daina kallonsa da mamaki ba.

“Sir! Akwai guba a cikin ruwan.”

Dokto Sa’id yana kokarin ficewa ya ji an rike masa kwankwaso. Ya juyo da sauri. Abin mamaki sikuiritis din wurin suke rike da shi kamar barawo.

Zayyad ya aika masa da murmushi.

Bayan an tafi da Dokto Sa’id shima ya wuce gida.

Sai dai ya duba ko ina babu Samha, ya nufi dakin Sakina itama kofarta a rufe. Ya koma ya zauna yana sake-sake.

Gabansa yana tsananta faduwa.

“Assalamu alaikum.”

Da sauri ya waiwayo yana kallonta. Tana sanye da katon hijabi da nikabi.

“Daga ina kuke?”

Ya tambayeta cike da damuwa. Ta kwance fuskarta sannan ta zauna tana fadin,

“Wash!”

Kafin ta yi magana kiran waya ya shigo. Daga asibiti ake nemansa. Ya dubeta,

“Bari in je asibiti in dawo.”

Ta mike tare da mayar da hijabinta,

“Mu tafi tare bana son zaman gidan nan, kullum a tsorace nake.”

Ya kama hannunta yana murzawa a hankali, sannan ya rada mata a kunne,

“Ashe jaruma kamarki tana da tsoro.”

Ta yi murmushi tana sauraren sakonnin da yake aika mata. Ta langwabe a jikinsa domin jikinta ya mutu.

“Ragguwa.”

Ya sake yi mata magana cikin wani irin sanyin murya. Ta sake shigewa jikinsa tana sakin numfashi. Dole ya fizgi kansa, sannan ya jawo hannunta suka fice.

Tana nan makale da file din da ta je makwancinsu ita da Mama, anan ta ta ga file din a in da ta boye.

Tare suka shiga wurin mara lafiyar.  Duk suka zuba masa idanu.

“Waye yake son kasheka?”

Zayyad ya tsinci kansa da rashin hakuri ya yi wa mara lafiyar tambayar nan. Duk da har yanzu bai sami karfi a jikinsa ba, amma sai da ya iya furta,

“Alhaji Bako ya aiko a kasheni.”

Zayyad da Samha suka kalli juna a firgice.

“Me kayi masa?”

Samha ce ta yi saurin yin tambayar cike da mamaki.

“Ya bani tsaron wani gida, gidan akwai ma’aikata da wata mata. Tsawon lokacin nan allura yake yi mata na fita hayyaci. Da zarar ta dawo cikin hankalinta zai sake yi mata allura. Da ni da Debora muke kulawa da ita, muna daukarta mu zagaya gari da ita, muna fito da ita wurin shakatawa na cikin gidan. Yanzu yana farautar rayuwata ne saboda na gaya masa ni bazan iya ci gaba da rashin imanin nan ba, shi ne yake tunanin zan tona masa asiri ne ya dinga aikawa a kasheni, Allah baya bashi sa’a. Ban san yadda akayi yasan za ayi mini aiki ba, ya turo a kasheni.”

Zayyad ya yi sauri ya karaso kusa da shi.

“Don Allah ka gaya mini ina ya ajiyeta? Ina zan sameta?”

Duk da yadda mara lafiyar ke jin jiki yana magana da kyar, wannan karon Zayyad ya gaza tausaya masa, bare har ya hana shi ci gaba da magana, kokarinsa ma ya daga muryarsa sosai ta yadda zai iya ji.

“Gidan yana wani daji ne, wanda babu gida a gaba bare baya. Anan ya gina katon gida.”

Wannan karon maganarsa ta daina fita. Zayyad kamar zai yi hauka. Dole Samha ta rike hannunsa da karfi tana girgiza kai,

“Please ka da ka daga hankalinka don Allah. Mu bi komai a sannu.”

Bai da zabi da ya wuce bin bayan Samha kamar yadda ta bukata. Zuciyarsa tana tafarfasa, soyayyar mahaifiyarsa tana kara ratsa sassan jikinsa. Yana so ya ji duminta da aka raba shi da ita tun yana yaro karami.

A ofis dinsa suka zauna kowa da irin tunanin da yake yi. Da sauri ta ciro file din ta mika masa.

“Ka duba wannan ko zai taimakawa tunaninka ya dawo.”

Ya karba kamar ba zai duba ba, domin a yanzu baya bukatar dawowar tunaninsa, babbar bukatarsa kawai ya ga mahaifiyarsa, ya dawowa da mahaifinsa farin cikinsa.

Yadda ta tsare shi da idanu ya sanya shi maido da idanunsa bisa file din.

Sannu a hankali ya fara karantawa.

 Tarihin rayuwarsa ce, da yadda akayi har ya auri Sakina, da dalilin sakinta, har zuwa ranar da ya saurari maganganun Alhaji Salisu da Alhaji Bako, akan yadda za a kashe shi, da kuma ranar da ya saurare su suna kulla yadda za su kashe shi, a wannan ranar ce suka buga masa iccen da ya yi sanadin rasa tunaninsa.

A hankali ya ji duniyar tana juya masa. Ya fara ganin wasu dodonni, ya rike kansa da karfi yana ganin dodon Sakina. Zufa ya dinga karyo masa.

Samha tana zaune tana kallonsa, ko kadan ba ta yi yunkurin dakatar da shi ba, domin itama a wannan lokacin tana bukatar ya dawo hayyacinsa. Ta gaji da zama da mutunin da bai san kansa ba.

Tun tana daukar abun wasa har ta ga ya zube a wurin baya motsi. Anan kuma sai ta rude ta tashi a guje ta yi kansa tana girgiza shi. Da gudu ta kwasa tana kiran

“Dokto! Please help!”

A guje suka yo kanta suna tambayarta. Ta kasa magana sai nuna ofis din Zayyad take yi da hannu. Wasu suka nufi ofis din, wasu kuma suka riketa ganin tana neman ta sume masu.

Taimakon gaggawa suka bashi, sannan suka daura masa karin ruwa.

Da kyar suka samu har Samha ta daina kuka, sannan ta ki barin kowa ya zauna kusa da shi, ita ke jinyarsa.

Wayarsa kuwa kiran shugaban kasa babu kakkautawa, amma ta kasa dauka. Tana tsoron yasan dansa yana kwance a asibiti babu lafiya.

Duk da tana tunanin ko bai san dansa bane, ba za ta iya gaya masa ba.

Cikin dare ya farka, a lokacin Samha tana zaune akan darduma tana ta kwararo masa addu’a.

  Ya dinga kallon ko ina, yana mamakin abin da ya kawo shi nan wurin.

A hankali komai ya dinga dawo masa cikin kai tiryan-tiryan. Rayuwarsa ta baya ta dawo cikin kwakwalwarsa. Ya kafe Samha da idanu. Shi kansa a yanzu yana jin tamkar an sauke masa wani irin tulin kaya ne a tsakiyar kansa.

Tana waiwayowa ta ganshi ya kura mata idanu, gabanta ya fadi da karfi. Yadda ya ganta tana zazzare idanu, abin ya so ya bashi dariya.

“Sannu ka tashi?”

Ya dubeta da rashin fahimta,

“Kema likita ce? Wace ce ke?”

Ta yi matukar firgita. Nan da nan jikinta ya kama rawa, bakinta yana karkarwa ta ce,

“Ka yi wa Allah da Annabi, idan ka mance ni kada ka mance mahaifiyata tana wurinka, idan ka mance in da ka kai mini ita zan iya mutuwa.”

Tana maganar bakinta yana kyarma.

Murmushi ya yi, sannan ya jawota gaba daya ta fada jikinsa.

“Da ruwa a hannunka fa.”

Bai ce komai ba, ya saka dayan hannun ya cire karin ruwan yana ci gaba da kallonta.

Ya jawota ta hau kan gadon ya jawo masu bargo, gaba daya suna fuskantar juna.

Bai yi magana ba, ya saka hannu ya kewayeta, sannan ya cusa hannunsa a cikin rigarta yana laluban bra dinta. Tana so ta yi magana, bai bari ta furta komai ba, ya hade bakinsu wuri guda. Tun tana mutsu-mutsu har ta yi lakwas! A lokacin da ta ji hannunsa akan dukiyar fulaninta. Tsigan jikinta ya dinga tashi saboda irin sakonnin da take karba. Kafafunsu da suka hade wuri daya suke ta motsi da su. Ya cusa kansa cikin bargon, a lokacin da ya ci nasarar zuge rigar komai suka bayyana, ya cusa kansa yana tsotson ‘yan biyunta. Ba ta san lokacin da ta saka hannu tana taba sassan jikinsa ba.

Sun yi nisa sosai, suka ji bugun kofa. Babu shiri ta kwace kanta tana mayar da numfashi. Gaba daya jikinta ya yi sanyi, sakonnin yau sun shigeta sosai.

Dokto Sani ya gani a cikin dakin. Zayyad ya kalle shi sosai, sannan ya ce,

“Sani..”

Duk suka kalle shi. Ya gyada kansa,

“Babu abin da ban tuna ba, akan rayuwata. Yanzu abin da ya fi damuna ina Ummana take?”

Sani ya jinjina kai, sannan ya karaso. Ya dubi yadda kwalar rigarsa take bude, ya dan yi masa siginal sannan ya nuna masa kirjinsa. Zayyad ya yi murmushi mai sauti sannan ya tashi zaune yana gyara kwalar rigarsa.

Samha dai sunkuyar da kanta kawai ta yi.

Anan suka tattauna yadda ya kamata su biyowa lamarin. Zayyad ya kirawo ‘yan sanda. Samha ta saka rigima akan dole sai ta biyo su. Mutum daya daga ‘yan sandan ya zauna kusa da mara lafiyar, aka saka masa waya a kusa da shi. Yana bayanin wurin da Hajiya Farida take.

 Cikin ikon Allah suka iso tanfatsetsen gidan, da ke dauke da gardawa majiya karfi.

‘Yan sanda za su fara harbi Zayyad ya dakatar da su.

“Ku dakata. Idan aka bude masu wuta, wani abu zai iya samun mahaifiyata. Ku bari mu yi amfani da dabara. Dole akwai tsaro mai tarin yawa a gidan nan.”

Duk suka amince da hakan. Samha ta yi yunkurin fitowa ya dakatar ita. Dole ta zauna tana nazarin abin da ya kamata ta yi.

Kafin su ankara har ta fice ta tunkari gidan. Zayyad bai san ta fice ba, sai hangota ya yi, tana gudu saura kiris ta karasa wajen gate din. Kansa ya sara da karfi, baya kaunar dalilin da zai sa Samha ta sami matsala. Da sauri ya yi yunkurin bin bayanta. Daya daga cikin ‘yan sandan ya dakatar da shi,

“Kyaleta…”

“Kamar yaya in kyaleta? Matata ce fa.”

Ya gyada kai,

“Ita din mace ce. Idan ba hakan akayi ba, ba zamu sami abin da muke so, ta kwanciyar hankali ba. Ina tabbatar maka babu abin da za su yi mata. Mu zagaya ta baya.”

Kafin su zagaya, suna hangota yadda take bubbuga gate din tana ihu.

Cikin mintuna kalilan dukkaninsu suka yo kanta, suka saita bindiga a goshinta.

Zayyad ya sake yunkurin bin bayanta. Dan sandan ya sake hana shi.

Da lallabawa Zayyad ya dan sakawa kansa natsuwa, musamman da ya hango yadda suka sauke bindigun suna ci gaba da kallonta.

“Ku taimakeni masu garkuwa da mutane ne suka daukoni yau, guduwa na yi, ku taimakeni don Allah.

Babu wani tunani, daya daga cikinsu ya bude mata kofar gate din a gurguje sannan ya bi bayanta. Wani daki ya nuna mata yana cewa,

“Ki boye anan, zuwa gobe sai ki wuce gidanku.”

Godiya ta dinga yi masu. Shi kuwa Zayyad hankalinsa ya gaza kwanciya, tsoro yake ji kada su cutar da ita.

“Kasan akwai matsala ko? Dole muna bukatar map din gidan nan, idan ba haka ba, babu yadda za ayi mu san wata hanya da za ta bulle da mu.”

Kiran wayar Samha ya dawo da shi duniyar tunani. Ya yi ajiyar zuciya sannan ya katse kiran.

“Ka dauka mana kila ta samo mana mafita ne.”

Ya girgiza kai,

“Akwai cctv a gidan, muddin suka ganta tana waya kashe mini ita za su yi.”

Text ta yi masa,

“Ka dauka ina cikin bandaki ne, kuma babu cctv a wurin.”

Ya yi ajiyar zuciya sannan ya kirawota.

“Na ga map din gidan a dakin da suka saukeni, sai dai har yanzu ban san in da Umma take ba.”

Ya jinjina kai,

“Ki ajiye wayarki kada ki sake kirana, ki natsu ki dinga aika mini da text. Ki ajiye map din ki dauki hotonsa ki aiko mini.”

Babu musu ta aikata hakan sannan ta boye wayar ta fito. Wani murdade ta gani a gabanta wanda ya kusa sakata ihu. Duk a zatonta ya kamata ne, don haka saboda tsananin firgici ta ji dumi yana bin kafafunta.

  Ya dubeta kawai sannan ya mika mata abinci.

“Ga shi ki ci in ji oga.”

Da sauri ta karba tana hadiye wani abu. Tunda Allah ya halicceta yau ne rana ta farko da ta taba jin mugun tsoron abokin halitta.

Ta karba kawai ta koma kan gado ta manne a lungu tana kyarma.

Duk abubuwan da take yi suna kallonta a cctv. Zuwa yanzu sun tabbatar da gaskiyar Samha, musamman yadda take a firgice tana zazzare idanu, wani lokacin kuma su ganta tana kuka.

Har yanzu babu wanda ya gayawa Alhaji Bala akwai wata bakuwa a gidan.

Bayan ya shigo ne, ya umarcesu da su canzawa Hajiya Farida daki, su kaita dayan dakin. Ba tare da wani tunani ba, suka kawota dakin da Samha take, sannan suka mayar da kofar.

Har Alhaji Bako ya taka zai shiga dakin da Samha take, sai kuma aka kira shi a waya. A yau ya ci burin ya biya bukatunsa da Hajiya Farida ta karfin tsiya, sannan ya kasheta. Ta hakane kawai zai dandanawa Zayyad da mahaifinsa madaci.

Domin yana da tabbacin a yanzu haka Zayyad ya haukace da neman in da mahaifiyarsa take.

Ficewa ya yi daga gidan gaba daya, jin mummunan labari akan har yanzu Alhaji Shamsu yana nan da rai bai mutu ba.

Har daren nan su Zayyad suna nan a wurin da ‘yan sanda. Haka zalika rashin jin Samha ba karamin daga hankalinsa ya yi ba.

Samha ta kafe Hajiya Farida da idanu, itama ta kafeta da idanu.

Babu wanda ya yi wa dan uwansa magana.

A lokacin wani ya shigo da wani try ya ce,

“Ki ci abinci ki sha maganinki.”

Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Samha ta karbi try din,

“Bari in ba ta.”

Bai kawo komai ba ya mika mata. Ta dubeta hawaye cike da idanunta ta ce,

“Umma ki ci abincin.”

Ta girgiza kai, tana ci gaba da kallonta cike da mamakin sunan da ta kirata,

“Maganin nan ne bana so, idan nasha yana wahalar da ni.”

<< Miskilin Namiji 20Miskilin Namiji 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×