Skip to content
Part 22 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Samha ta dukar da kai tana jin tausayinta, tana diban kamanni da Zayyad sosai.

“To ci abincin.”

Ta karba tana ci. Bayan ta gama ne, ta mike za ta shiga bandaki. Da sauri Samha ta rike hannunta suka shiga tare. Suna shiga ta riketa sosai.

“Umma na zo ne in taimakeki. Insha Allahu lokacin barinki gidan nan ya zo.”

Hajiya Farida da jikinta yake rawa ta ce,

“Wace ce ke?”

Samha ta girgiza kai,

“Idan kika fito zaki gane ko wace ce ni Umma. Kawai ki saka a ranki ni diyarki ce. Jininki yana tare da ni.”

Ta numfasa. Samha ta fito ta kyaleta a bandakin.

Hajiya Farida ta sami sassaucin abin da ke damunta. Ko babu komai yau ta ga wacce ta hada kanta da jininta.

Suna nan zaune babu mai yi wa dan uwansa magana. Sai gani suka yi an dauke wuta.

Gaba daya gidan duhu ya garwaye. Hajiya Farida ta ce,

“Ban taba ganin an dauke wuta a gidan nan ba.”

Samha da take jin tabbas Zayyad ya bayyana a cikin gidan ta dan yi shiru tare da kasa kunnenta.

Tana jin yadda ake ta surutai. Zayyad ya gano in da su Farida suke don haka kai tsaye dakin suka dosa kamar yadda ta gaya masa. Da hasken wayarsa ya shigo, ya ce

“Ku yi sauri ku zo mu tafi.”

Yana kama hannun mahaifiyarsa ta ji gabanta ya fadi da karfi. Binsa kawai take yi Samha tana biye da su.

Dogon ladan da Zayyad ya gani a gidan ya dauka ya manna da katangar sannan Samha ta fara hawa. Ta riko hannun Hajiya Farida. Wajen dirowa ‘yan sandan suka taimaka masu. Zayyad shima ya hau sannan ya ture ladan. Kafin ya dira, wutan gidan ya dawo.

A lokacin wani ya biyo shi yana cewa,

“Waye anan?”

Zayyad ya diro, yana kallon yadda Samha ke wahala da mahaifiyarsa kasancewar ba ta iya gudun sosai.

Cikin hukuncin Allah suka shiga motar suka bar wurin.

Masu gadin gidan kuwa a wannan lokacin sun sha giyarsu sun koshi, sai hauka suke yi. Ko kadan basu kawowa kansu daukewar wutan nan yana da alaka da Hajiya Farida ba.

Kai tsaye Zayyad ya wuce da ita asibitinsu.

Cikin gaggawa ya fara ba ta taimako. Har ya kama hannunta yana neman jijiya ba ta daina kallonsa ba. Samha kuma tana rike da ita, lokaci zuwa lokaci taba yi mata sannu.

A cikin allurar da ya yi mata har da na barci. Bakinta yana motsi, amma ta gaza furta komai. Barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. Dukkansu suka kalli juna sannan suka numfasa.

Samha ta zauna a gefenta tana kallonta cike da tausayawa.

 Shi kuma ya fice zuwa wurin ma’aikatan asibitin.

A ofis dinsa ya yi wanka, ya kimtsa sannan ya aika aka siyo masu ‘yan abubuwan da ba za a rasa ba. Duk da dare ya yi hakan bai hana masu kasuwanci barin shagunansu a bude ba. Ya shigo yana duban Samha, tana nan rike da hannunta, tana gudun kada ta cika motsawa hannun ya kumbura.

Dayan gadon ya hau sannan ya yafitota da hannu.

Ta juya ta kalli Umma, sannan ta ajiye hannun a hankali ta karaso wurinsa.

A kunne ya rada mata,

“Ki kwanta hakannan ki huta kina bukatar hutu.”

Tana so ta yi masa magana, sai dai yadda ya cusa hannunsa a cikin rigarta yasa gaba daya ta daburce.

Ya dan yi magana kasa-kasa,

“In sha?”

Ba ta san lokacin da ta daga kanta ba, alamar “eh” Ya kuwa daga rigar ya manna bakinsa a kirjinta. Ta dinga turo masa kirjin, tare da danna kansa.

Sai da ya luguiguita ta yadda yake so, sannan ya rabu da ita idanunta a lumshe.

Dukkansu sun kasa barci sai juye-juye suke yi.

Da asubahin fari ma’aikatan nan suka dawo hayyacinsu. Mai kai mata magani ne ya fara an karewa da babu Hajiya Farida babu Samha.

Da gudu ya fito yana sanar masu. Duk suka haukace da nemansu amma ko sama ko kasa basu gansu su ba.

Suka bude cctv babu abin da suka gani, sai wani mutum da ya je wurin wuta ya katse wutar.

Anan idanu suka raina fata. Dukkaninsu suka yanke shawarar su yi kamar basu san abin da ya faru ba, idan ba haka ba, Alhaji Bala duk sai ya harbe su.

Haka suka ci gaba da sabgoginsu kamar babu komai, a can kasan zuciyoyinsu kuwa tsoro ne da fargaba.

“Wato wannan yarinyar da muka taimakawa ita ce shaidaniyar kenan. Wallahi sai da na zargi wani abu akanta, musamman yadda na ganta tsaf! tsaf!! babu wata alama da zai nuna maka tabbas an sace ta ne.”

Daya daga cikinsu ya furta yana cizon yatsa.

Hajiya Farida tana farkawa, Zayyad ya cire mata ruwan, Samha kuma ta hada mata ruwan wanka. Bayan ta fito ne, ta hau kan darduma ta yi sallah.

Kafin ta idar har Samha ta hada mata tea mai kauri da Bread. Abin mamaki tasha sosai, sannan ta yi hamdala.

Ta dube su daya bayan daya, yadda suka durkusa har kasa suna gaidata. Idanunta suka kawo kwalla. Jikinta yana ba ta wannan Muhseen dinta ne. Ta kafe shi da ido sosai, idanunta cike da hawaye.

“Muhseen.”

Da sauri Zayyad ya dago shima yana kallonta. Wani abu yana ratsa zuciyarsa. Ji yake tamkar an sauke masa wani katon dutse ne a kirjinsa.

Da sauri ya karaso ya rike hannayenta.

“Na’am Umma.”

Nan da nan ta fashe da kuka da sauri ya karaso sosai ya zauna kusa da ita. Da sauri ta rungume shi tana kuka sosai.

Bai hanata ba, domin shi kansa da zai samu hawayen ya fito da ya yi kukan.

Da kanta ta tsahirta, ta dubi Samha ta ce masa,

“Wannan wace ce?”

Dukkaninsu suka sunkuyar da kai.

“Matarka ce?@

Ya daga kai. Ta dubeta, ta ce

“Zo kusa da ni diyata. Allah ya yi maku albarka.”

Samha ta karaso da sauri duk ta hadesu ta rungume. Tanason tambayarsa mahaifinsa sai dai ta gaza tambayar, don haka ta hadiye kawai zuwa wani lokaci.

Zayyad yana ofis dinsa kiran wayar Alhaji Bako ya shigo masa. Cike da kwarin guiwa ya daga wayar.

“Ina so da ga yau ka fara kuka, domin kuwa na kashe mahaifiyarka. Ta mutu har lahira sai dai ka nemo wata uwar ba ita ba. Domin a yanzu haka ina hanya zanje wurinta, don na fara jiyo kamshin gawa.”

Zayyad ya yi murmushi mai sauti,

“Kai za ka rigata mutuwa. Idan ka isa in da za ka kasheta, ina so kayi gunduwa-gunduwa da namarta, muddin ka iya aikata hakan, ka tabbata ba mahaifiyata ba ce, idan mahaifiyata ce da gaske, bana jin daga rana irin ta yau za ka iya sake ganinta a kusa da kai.”

Alhaji Bako ya dinga dariya har da buga sitiyari.

“Sai na saka an yi video din yadda zan keta haddinta, saboda ka ga yadda ake kwanciya da uwarka.”

“Kai! Bako! Ya isa haka! Ya isa! Sai na tabbatar da kayi danasanin munanan furucinka.”

Ya katse wayar yana mayar da numfashi.

Alhaji Bako kuwa cike da farin ciki ya isa gidan.

Bayan duk sun gaida shi, ya nufi dakin Hajiya Farida a fusace. Sai dai har bandaki ya duba bai ganta ba, da sauri ya koma dayan dakin, duk a zatonsa sun sake mayar da ita dakin ne. Ya gigice ya shiga kwala masu kira.

Jikinsu yana rawa suka ce masa basu san yadda aka yi ta fice ba, sun dai san jiya wuta ya dauke.

Da sauri ya shako wanda yake bayanin, ya dinga wanka masa mari jikinsa yana rawa.

Gaba daya ya haukace, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba.

A lokacin wayarsa take neman agaji. Ya dauka ba tare da yasan waye ba. Muryar Zayyad ya ji yana magana,

“Na gaya maka na fi ka hatsabibanci. Tunda kuka yi sake na kai shekarun nan a raye, da ga nan kuskurenku ya fara. Kada kayi yunkurin yin wani abu, domin kuwa karyarka ta kare. Gidan da ka ajiye mahaifiyata tsawon shekaru a yanzu haka kewaye yake da ‘yan sanda. Sai ka fito da duk abin da ka taka, domin ni da kai zamu bayyana a gaban kotu.”

Kit! Ya kashe wayar yana murmushi.

A yanzu mahaifinsa yake son gani, domin ya gama da fannin Alhaji Bako. Haka zalika ya cire sunan Alhaji Salisu, ko babu komai, ya rike shi riko na tsakani da Allah, bai taba nuna masa bambanci ba.

‘Yan sanda suka tattare duk wata halitta da ke cikin gidan. Sai ga Alhaji Bako yana zazzare idanu. Gaba daya ya muzanta.

Zayyad da Sani suka je har police station din suka same shi a cikin Cell yana huci kamar zai daki mutane.

Zayyad yana murmushi ya ce masa,

“Na gode maka da ka taimaka mini tunanina ya dawo. A marasa imani babu na biyunka. Kana sane babu aure a tsakanina da diyarka, amma saboda son zuciya ka sake aura mini ita. Na tuna komai, na tuna yadda kayi yunkurin kasheni Allah bai nufa ba. Mahaifina ya yi maku rana, sai kuka zabi ku yi masa dare. Kune silar da ya kamau da mummmunan cuta, duk da hakan bai isheku ba, har sai kun sake nesantani da shi. Zan tabbatar da an yi maka hukuncin da zai zama izna ga ‘yan baya. Domin babu amfanin zamanka a duniyar. Kayi yunkurin kashe mahaifina, ka yi yunkurin kashe mahaifiyata, ina tabbatar maka zan kawo karshen zaluncinka har ma da ire-irenka masu tunani irin naka.”

Alhaji Bako ya dube shi yana dariya,

“kai Muhseen! Na riga na yi maka mummunan illa! Ka je kayi gwajin kanjamau domin kana dauke da shi. Ka ga ko da wannan na barka na yi maka illa.”

Zayyad ya yi murmushi.

“Shiyasa na gaya maka ni nafi karfinka. Har alfahari kake yi ka kwanta da diyarka, ka saka mata cutar kanjamau ko? Allah ya yi ta nuna maka ishara tuntuni akaina amma sai idanunka suka rufe, zuciyarka ta

ka sa  baka shawara. Tun lokacin da ka kwnata da ‘yarka nasan komai, tun daga nan na kiyaye diyarka. Don haka ni baka gama da ni ba, ka dai gama da ‘yarka. Hatta guban da kake ba ta domin ta zuba mini a cikin abinci ina sane. Na zuba maku idanu ne domin in ga iya gudun ruwanku.”

Ya juya yana huci. Alhaji Bako kuwa shiru ya yi yana jin takaicin duk yadda ya kai ga kassara iyalan Alhaji Mamman hakan yake gagara, sai ma tarin nasarori da suke samu.

Bayan Zayyad ya bar police station din kai tsaye asibiti ya nufa,  ya tattara mahaifiyarsa da Samha, suka wuce  gida.

Tun daga falo suke jin shewa. Har suka shigo Sakina ba ta san sun shigo ba.

Tana tare da kawayenta wayayyu. Umma ta tsaya turus! Tana kallon ikon Allah.

“Wace ce kuma wannan?”

Ya numfasa sannan ya ce,

“Sakina ce diyar Alhaji Bako.”

Sakina ta kalleta, a lokacin da ta kashe sautin. Samha ta dubi hannun Sakina da kafafunta duk an yi mata dauri, amma saboda tsinancewa ta kasa dawowa hayyacinta, sai ma gayyato kawayenta da ta yi, suna sharholiyarsu.

Umma ta kalli Sakina sosai sannan ta ce,

“Me take yi anan gidan kuma?”

Ya dan yi shiru. Caraf! Sakina ta amsa

“Kamar yaya me nake yi anan? Nan fa gidan mijina ne, bai kamata ana tambayar abin da nake yi ba.”

Shi kansa bai san lokacin da ya karaso wurinta ba, sai jin saukan mari ta yi a kuncinta, ya dinga wanka mata mari, har sai da Umma ta yi magana cikin bacin rai,

“Kyaleta Muhseen. Da baka aurota ba, ba za ta zo tana maganar nan ba.”

Ya girgiza kai,

“Wallahi ba matata ba ce.”

Sakina da kawayenta suka zaro idanu. Sannu a hankali ya gayawa mahaifiyarsa duk abin da ya faru. Wanda tuni gumi ya wankewa Sakina fuska. Ba ta taba sanin ya dawo hayyacinsa ba. Ya dubeta cike da bacin rai ya ce,

“Ki zo ki fice mini a gida. Ina sane da kina dauke da cutar kanjamau wanda ubanki ya saka maki.”

Wata daga cikin kawayen ta yi tsalle ta ja da baya tana kallon Sakina. Samha kuma ta kama hannun Umma ta nufi da ita falonta ta ajiyeta a dogon kujera.

Zayyad kuma ya wuce dakinsa. Samha ta lallaba ta fito wurinsu Sakina, sannan ta yi dariya.

“Kin yarda yanzu da likafanina na shigo gidanki ko? Likafanin nan ya yi maki amfani, tunda ga shi za ki koma rayuwar kabari. Kin za ci duk abubuwan da kike aikatawa ina kallonki ko? Kin gane bambancin mutum da dabba ko? Kin gane bambancin mai ilimi da dakiki ko? Kin zuba guba a cikin abinci domin Uncle Zayyad ya mutu, abin mamaki ina zubawa kare ya mutu. Na dade ban ga azzaluma kamarki ba Sakina. Na tsaneki. Bushewar zuciyarki iri daya da na ubanki, domin kuwa babu in da kika baro halayyarsa.”

Sakina ta yi yunkurin kaiwa Samha duka da dayan hannun mai lafiya. Samha ta rike hannun, sannan ta nunata da yatsa,

“Kul! Kada ki kuskura ki yi wannan gangancin, domin zan iya karasa dayan hannun ki tafi a nakashe. Ki kwashe kayanki da ke gidan nan, kada ki bar ko da tsinke ne. Idan ban da rayuwar dabbobi ta ina aka taba yin aure aka yi saki uku, don lalura ta kama mijin a sake mayar masa? Daga karshe saboda ku din mugaye ne wai kuka ci gaba da neman rayuwarsa.”

Zayyad yana bayansu yana jin komai. Mamaki ya kara kama shi. Sai yau yasan dalilin mutuwar karen nan.

“Ba zan fita ba, idan kin isa ki zo ki fitar da ni.”

Kafin Samha ta ba ta amsa Zayyad ya amshe maganar,

“Idan ba ki fita ta dadi ba, babu ko shakka zaki fita ta hanyar wahala. Na baki mintuna ashirin, kada in dawo in sameki a cikin gidan nan.”

Ya jawo hannun Samha, domin yasan muddin ya barta anan sai sun ci gaba da hayaniya.

Haka Sakina ta tattara kayanta ta koma gidan Hajiyarta a karo na farko. Har ta gama shigar da kayanta hajiya Zaituna mahaifiyarta  ba ta ce mata uffan ba. Sai ma ci gaba da kallon labarai da take yi.

Ita kanta Sakinar ba ta yi mata magana ba ta ci gaba da sabgoginta.  A cikin zuciyar Hajiya Zaituna tana jin dama Sakina ba ta kasance daga cikin jininta ba.

***

Samha kuwa tun bayan tafiyar Sakina, take aiki a cikin gidan. Gaba daya ta tsaftace ko ina, ta gyarawa Umma dakin da Zayyad ya ce akaita, daga nan ta fada kitchen domin samar masu abin da za su ci.

Lokaci zuwa lokaci takan leka Umma ta tambayeta ko tana son wani abu. Farat daya Samha ta shiga zuciyar Hajiya Farida.

Kafin Zayyad ya dawo, har Umma ta yi wanka ta kwanta, Samha ta dinga yi mata tausa. Nan da nan barci mai dadi ya kwasheta.

Samha ta koma ta sake watsa ruwa. Tana zaune tana shafa mai a santala-santalar cinyarta. Ji ta yi ana shafa bayanta, da sauri ta kalli madubi, duk suka yi murmushi.

“Tunanin me kike yi?”

Ta dan sunkuyar da kanta ba tare da ta ce komai ba.

“Ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe.”

Shiru ta yi, don haka ya saka hannu ya warware tawul din. Ta madubi ya kallesu sun gama burge shi.

Cak! Ya dauketa ya kaita kan gado. Ba ta hana shi duk abubuwan da yake yi ba, sai da ta ji yana kokarin zakewa sannan ta rike hannunsa tana girgiza kai.

Bai ce komai ba, ya zame kansa ya kwanta.

<< Miskilin Namiji 21Miskilin Namiji 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.