Yau dai Zayyad ya dauki Hajiya Farida da Samha suka nufi wurin shugaban kasa.
Tun shigowar Zayyad asibitin ake bashi girma, har ya isa kofar da za ta sada shi, da dakin shugaban kasa, babu wanda ya hana shi, ko kuma yi masa tambayoyi.
Suna bude kofar suka sami matarsa tana hamshake a wata kujerar alfarma tana latsa waya. Walid da Mufida suma suna zaune a wata kujerar suna latsa laptop.
"Assalamu alaikum."
Gaba daya suka dago kai. Idanun shugaban kasa fes! Akan Hajiya Farida.
Ita kanta matarsa sai da gabanta ya fadi, duk da babban hoton da ke dakin. . .