Skip to content
Part 5 of 19 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Takun tafiyarsa ya dawo da kowa cikin hayyacinsa. Kai tsaye wurin wanke hannu ya nufa, ba tare da ya daga kai ya kalli kowa ba. Ya wanke hannun, yana jin yadda duk suka mike suna cewa,

“Wellcome sir.”

Bai amsa ba, ya cigaba da abinda yake yi. Sannan ya saka hand gloves Ya yi taku kamar zai fita, sai kuma ya dawo gaban Safiyya yana kallonta. Kiris tayi fitsari a wando tsabar gigicewa,

“Idan kika kori Samha ba fada kawai zan yi ba. Daureki zanyi sai naga wanda ya tsaya maki. Sannan dole ki tura danginki nemanta, idan anganta sai in sakeki ki kama gabanki.”

Har ya wuce ya sake juyowa,

“Idan na daureki kullum da kalar izayar da zanyi maki.”

Ya karasa ficewa bai dubi sauran ba. Duk suka zube suna numfarfashi. A rude Asiya ta ce,

“Kai ku tashi mu je zai zagaya marasa lafiya.”

Suka sake kwasawa a guje. Kowaccensu tana kokarin tuna abinda ta ce.

Ga mamakinsu dakin Samha ya fara dosa. Da sauri suka bi bayansa.

Tana zaune ta idar da Sallah. Ya saka hannu ya yafitota. Ga mamakinsu sai gata ta zo gabansa kanta a kasa. Ya kama tsintsiyar hannunta yana cewa,

“Hannun ya kumbura why?”

Yayi maganar cikin wani irin sanyi. Ta dago fararen idanunta ta dubeshi, sai kuma tayi saurin janye idanun.

“Kina motsa hannun da yawa ne Samha. Kinji sauki gobe zan sallameki. Kin ci abinci?”

Ta daga kai alamun eh. Ya dago yana dubansu,

“Me kuka ba ta da rana?”

Da sauri Sadiya ta ce,

“Tuwon shinkafa tace tana so da miyar ganye da nama.”

Ya jinjina kai. Ya bare maganin da kansa ya mika mata. Idanunta suka raina fata dan ta tsani magani. Ya ware idanu yana dubanta. Dole ta karba ya bude ruwan roba ya ba ta. Tasha tana runtse idanu. Ya dan matse hannunta, hakan yasa ta dago ta dubeshi, ya daga mata gira sannan ya ce,

“Sorry.”

Dukka ‘yan dakin mutuwar tsaye suka yi. Dan har ya mike basu sani ba, tsabar mamaki.

Bai kallesu ba yayi hanyar waje. Karar bude kofarsa ya ankarar da su, da sauri suka bi bayansa. Samha ta lumshe idanu tana jin sanyi da irin kulawar Dr akanta. Ada ta dauke shi mugu, a yanzu kuma ta fahimci yana da tausayi. Sai dai kuma tunanin mahaifiyarta ya qi barinta ta ji dadin tarin ni’imomin nan. Sosai ta saka kuka tana kiran sunan Mamanta. Har da birgima tana shure-shure. Gani tayi anbude kofar. Ba ta dago ba ta cigaba da kukanta.

Yana karasowa ya dagota, bai iya dogon lallashi ba, dan haka ya hadeta da jikinsa yana shafa bayanta.

“Meya saki kuka? Ki natsu kinji?”

Wani irin shokin ta ji ya ratsata, tunda take ba ta taba sanin akwai wata rayuwa irin wannan ba. Jikinta yayi sanyi kalau.

“Are you ok?”

Gyada kanta ta yi. Ya dagota yana share mata hawayen da dayan hannunsa.

“Fada min menene?”

Ita dai ta nemi kukan ko sama ko kasa ta rasa. Labbanta suka motsa, dan haka ya kawo kunnensa

“Ina jinki tell me.”

“Mamana..”

Ta furta maganar cikin wata marainiyar murya. Iskar bakinta suka daki kunnensa, har sai da ya ji tsigar jikinsa ya tashi.

Kafadunta ya rike ya ce,

“Samha. Ki kwantar da hankalinki kin ji? Mahaifiyarki tana cikin koshin lafiya, bazan bari wani abu ya cutar da ita ba nayi maki alkawari.” Ta kasa magana, amma fuskarta tana nuna yadda ta ji dadin kalamansa.

Sai da ya tabba tar da ta sami natsuwa sannan ya fice yana furzar da huci. Yana son tambayarta inda ta ajiye files dinnan. bayaso kuma ta zargi wani abu. Tunda ya fahimci yarinyar tana da wayo.

Lumshe idanunsa yayi yana hango iyayensa suna meeting babu shi a ciki. Abin ya tsaya masa a rai. Kiran wayar mahaifinsa ya gani, hakan yasa ya janyo wayar ya dauka tare da sallama. Ko a muryarsa bai bari mahaifinsa yasan akwai wata damuwa a zuciyarsa ba.

“Abba ina ofis.”

Ya bashi amsa bayan sun gaisa.

“Ok ka zo ofis dina yanzu yanzu.”

Ajiye wayarsa yayi tare da mikewa. Tafiyar mintuna sha biyar ya sada shi da ofishin mahaifinsa.

“Ina so zan aikeka Gombe ne.”

Zayyad ya cira kai da sauri yana duban mahaifinsa.

“Abba gombe kuma?”

“Eh Gombe.”

Ya bashi amsa a dan fusace. Ya ce

“Ok. Dama inaso ingaya maka Alhaji Bako yazo ya kawo mini wani file ya ajiye a ofishina. A cctv na ganshi.”

Zayyad ya kara shiga duhu saboda ganin yadda Abbansa ke keta wani irin gumi. Jikinsa har kyarma yake yi,

“Ka ce mene?”

Abban ya sake tambayarsa. Zayyad ya sake maimaita masa yana dubansa. Da karfi Zayyad ya rike kansa yana ganin wasu abubuwa masu kama da dodanni. Ya rike kan da karfi kamar yanason tuna wata rayuwa da ya taba yi a baya, amma hakan ya faskara.

“Zayyad menene kake yi haka?”

Maganar Abba ya dawo da shi hayyacinsa. Yayi saurin dubansa shi kansa gumin yake yi.

“Ina files din da ya ajiye maka? Ka karanta ne?”

Da sauri ya girgiza kai yana dafe da kansa,

“Wata yarinya ta sace files din. Amma ina nan ina bibiyar yarinyar.”

Abban ya saki ajiyar zuciya.

“Ina sake gaya maka ka kiyayi Alhaji Bako. Idan ba haka ba, watarana sai ya yi maka muguwar illa. Ka tashi kaje, na fasa aikenka Gomben.”

Zayyad ya jinjina kai, ya tashi ya fice.

*****

A katon wurin shakatawan wanda yake dauke da kujeru masu kyau na alfarma. Dr. Zayyad ne, da Dr. Rahama, da kuma Samha. Ya sake duban Dr Ramaha ya ce,

“Ke ce kadai zaki iya yi mini wannan taimakon. Ina son a watanni biyu Samha ta dawo wayayyar mace, ta kuma iya kalolin girke-girke. Zan kara wata daya akai, tasan dabarun gudanar da bincike. Banason insaka jami’an tsaro a cikin wannan abunne. Samha tana da wayo ina ji a jikina ita ce zata binciko duk abubuwan da ni na kasa bincikowa. Dokto rayuwata tana cikin hatsari. Mutane da yawa suna farautata, suna farautar rayuwata. Yanzu zargin kowa nake yi. Sai dai na kasa gane komai. Da ke da Samha kune kadai wadanda zaku iya taimakona. Ina so duk wani abu na kauyanci ki cire shi a jikin Samha.”

Ya karashe maganar cikin wata murya. Sosai tausayinsa ya tsirgawa Samha. Duk da haka sai da ta kwantar da kanta ta ce,

“Mamana kuma fa? Inaso inganta.”

Dr. Zayyad ya dubeta sosai sannan ya ce,

“Idan kin yarda da ni, mahaifiyarki tana cikin kulawarmu. Kina gama yi mini aikina kafin nan mahaifiyarki ta mike ras! Sai ki koma gareta.”

Sai yanzu Dr. Rahama ta numfasa,

“Insha Allahu Allah zai tona asirin duk masu binka da bita da kulli. Sannan zan yi iya yina akan Samha. Nayiwa Baba magana nayi masa bayani. Dan haka kana iya turawa a nemi auren Samha a wurinsa. Ai da na kowa ne.”

Dr. Zayyad ya zube miliyan biyar agaban Dr. Rahama ya ce,

“Ki fara amfani da wadannan.”

Ganin yadda take girgiza kai yasan bazata karba ba, dan haka ya mike kawai yana cewa,

“Kada ki damu. Kada ki ce a’a. Sai na waiwayoki.”

Rayuwar Samha da Dr. Rahama abin ya ba ta mamaki. Duk abinda take kokarin koyawa Samha, sai taga ta iya. Bangaren girki ne kawai ta koya mata abubuwan zamani da yawa. Ta dauko mai gyaran jiki aka gyare Samha tas! Yarinya mai kyau da diri. Gashin kanta kuwa ga tsawo ga cika ga sulbi. Babu abinda Dr. Rahama take cewa sai “Masha Allah.”

A yau Zayyad ya nufi gidansu da nufin gaya masu auren da yake nema.

“Aure fa kace Zayyad.”

Umma ta tambaya tana ware idanunta. Ya jinjina kai. Abban ya yi gyaran murya ya ce,

“Allah ya baka ikon rike ko wacece. Sai ka hadani da iyayen yarinyar zan tura bappaninka suje su nema maka auren.”

Har ya mike zai tafi Umma ta dube shi cike da rauni ta ce,

“Zayyad!”

Ya juyo tare da dawowa,

“Na’am Umma.”

“Zayyad me yasa ka canza kwana biyu? Me yake damunka ne?”

Ya girgiza kai,

“Babu komai Umma. Kwana biyun nan ne sai indinga ganin abubuwa kamar wanda ya taba wata rayuwa. Ko kuma inyi ta wasu mafarkai barkatai.”

Umman ta jinjina kai,

“Ka dinga addu’a Zayyad. Kana sakaci da addu’a.”

Ya dan shafa kai,

“Insha Allahu Umma. Na barku lafiya.”

Har ya karya hanyar gidan Dr Rahama, sai kuma ya canza hanya ya koma gida. Sakina ta dubeshi idanunta sun yi jazir saboda kuka. Sosai ya ji zuciyarsa ta karye. Ya fara tunanin ko dai kawai zuciyarsa ce ke zargin Sakina?

Ya yafitota da hannu, da sauri sauri gudu gudu ta karasa jikinsa ta kwanta. Dukkansu suka saki gouron ajiyar zuciya. Har yanzu kukan take yi. Da gaske ta yi kewarsa, da gaske tana jin sonsa yana ratsa zuciyarta. Ta gane cewa duk barazana ce, domin zuciyarta ba zata iya rayuwa idan babu Dr. Zayyad ba. A kalla sun kwashi mintuna biyar a haka. Sannan ya jawota zuwa kujera. Ya zauna sannan ya zaunar da ita a jikinsa. Ya kwantar da ita a kafadarta yana shafar bayanta kamar ‘yar baby. Abin mamaki da al’ajabi sai ji yayi tana sauke numfashi, na irin wacce tayi barci. Da sauri ya cira kai ya dubeta. Tabbas barcin take yi. Ya kwantar da ita tare da raba kansa da ita. Ya kafeta da idanu. Fuskarta tana yi masa kama da irin fuskar da ya taba sani a wani wuri. Kansa ya fara daukar caji. Yanason dole sai ya tuna inda ya taba saninta ba a matsayin matarsa ba. Karar wayarsa ita ta dawo da shi, duniyar tunanin da ya shiga wanda ke barazanar cizge masa kwakwalwa.

Kira ya samu daga asibiti, dan haka ya fice da sauri.

Da isowarsa ya sami wata dattijiwa tasha wuya. Cikin gaggawa ya fara ba ta kulawa. Yasha bakar wahala akanta kafin ya sami kanta.

“Ina danginta?”

Ya yi tambayar cikin takaici. Wata ta karaso tana cewa,

“Rankashidade nima taimakon musulunci nayi. Tsohuwar nan yaronta mai kudi ne, amma haka suka kyaleta tana kwana da yunwa ta tashi da yunwa. Duk garin nan waye baisan Alhaji Bako ba? Ga dukiya har dukiya, amma mahaifiyarsa ko kallo ba ta isheshi ba.”

Zayyad ya dawo da baya bakinsa a bude,

“Kika ce waye danta?”

Matar ta matse hawaye ta ce,

“Alhaji Bako dai da ka sani shine Danta da ta haifa a cikinta. Amma Wallahi baya ba ta abinci sai mu makota mun tausaya mun kawo mata.”

Dr. Zayyad ya wuce kawai yana jujjuya maganar.

“Wanene Alhaji Bako? Tayaya ma akayi har na iya auren Sakina? Me ya faru dani ne? Wanene ni? Dole akwai wani abu a cikin rayuwata.Dole akwai dalilin da Alhaji Bako ya shiga rayuwata. Meyasa iyayena basu iya daukar mataki akansa ba? Meyasa su kansu suke tsoronsa? Mahaifiyarsa? Ni da kaina ne na auri zuri’a irin ta Alhaji Bako? Tayaya? Iyayena basu yi mugun dagewar nan akan bazan aureta ba, sun dai nuna basa so na nuna ina so. Meyasa basu dage kada na aureta ba?”

Shi kadai yake ta sumbatunsa. Da sauri ya koma wurin tsohuwar, ya cira tsadaddiyar iphone dinsa ya dauki hoton tsohuwar. Sannan ya bayar da umarnin a mayar da ita daki na musamman, a ba ta kulawa. Idan ta tashi aba ta abinci mai kyau.

Da sauri ya kama hanyar gida. Ikon Allah kadai ya kawo shi gida. A lokacin ya ci karo da wata dalleliyar mota ta fice daga gidansa. Da idanu ya raka motar, kafin ya dubu maigadin ya ce,

“Waye ya shigo min gida?”

Jikinsa yana rawa ya ce,

“Alhaji ne mahaifin madam.”

Zayyad yayi shiru kamar mai tunani. Har maigadin ya cire rai da zai sake yi masa magana, sai kuma ya kada yatsuntsa ya ce,

“Daga yau, na saka dokar kada ya sake shigo mini gida. Idan ka sake barinsa ya shigo mini gida, ina tabba tar maka zaka koma gidansa da gadi. Bude min gate.”

Maigadi ya dinga bashi mamaki. A zuciyarsa kuma mamaki ne ya lullube shi. Ko a wasan kwaikwayo bai taba jin inda akayi haka ba. Tayaya hakan zai faru? Surukinka kace kada a sake barinsa ya shigo gidan da ‘yarsa take rayuwa? Haka yayi ta jujjuya abun.

Babu sallama ya banko kofar. Tana tsaye hannunta rike da makudan kudade tana murmushi. Matsalarta da Zayyad ko kadan baya sakar mata kudi, haka zalika ta rasa inane maboyarsa. Duk binciken duniyar nan tayi, amma ba ta taba cin sa’an samun ko naira daya ba.

Ta firgita, tana kokarin boye kudin, ta tabba tar da ya riga ya gani. Dan haka ta fito da su tana cewa,

“Sannu da zuwa masoyi. Ka ga yanzu Baba yazo ya bani wannan.”

Bai ba ta amsa ba, sai neman wuri da yayi ya zauna yana dafe da kansa. Ji yake komai yana yamutsewa.

“Kinsan wannan matar?”

Ya bude wayarsa yana nuna mata hoton dattijuwan nan. Da sauri ta karaso tana kallon fuskar wayar. Ta dade tana kallon tsohuwar, daga karshe tayi zooming din hoton.

“Bansanta ba Wallahi.”

Jikin Zayyad ya karasa mutuwa. Zarginsa ya kara karfi. Ya kasa amincewa tsohuwar nan ita ce mahaifiyar Alhaji Bako. Idan da gaske mahaifiyarsa ce meyasa hatta diyarsa ta cikinsa ba tasanta ba? Meyasa zuri’ar Alhaji Bako suka yi masa yawa? Meyasa suka hanashi kwanciyar hankali? Mahaifiyar Samha ma tasan Alhaji Bako. Hasalima nemanta yake ya kasheta. Tabbas da ba dan shi ba, da tuni an mance da tarihin mahaifiyar Samha, da tuni Alhaji Bako ya shafeta. Shi ba dan siyasa ba, ba mai neman mulki ba, amma yana sha’awar bakar zalunci ba tare da kowa yasan me yake son ya cimma ba.

“Wacece ita?”

Ta katse masa tunani. Ya shafi lallausan gashin kansa ya ce,

“A’a ankawota ne babu lafiya ta bani tausayi.”

Ba tare da dogon tunani ba, ta ce,

“Allah sarki. Bari inkawo maka abinci.”

Ya jinjina kai. Shiru-shiru tunda ta shiga kitchen ba ta fito ba. Hakan yasa ya mike ya shige dakinsa ya rufe. Tana fitowa tayi turus! Ta tsaya tana zare idanu.

“Na shiga uku. Allah dai yasa ba ficewa yayi ba.”

Ta duba can waje ta ga motarsa, sannan ta saki ajiyar zuciya. Sai dai bugun duniyar nan tayi amma ya ki budewa. Tayi mamakin yadda bai fito yayi mata tijara ba.

Haka ta koma da abincin da yake dauke da maganin barci, wanda mahaifinta ya ba ta umarnin nan, yana so a sace shi, yasan ba zai sacu ba, har sai an bugar da shi.

Kwanaki biyu Inna tayi a asibitin ta murmure ga kayan dadi kala-kala. Dr. Zayyad ya janyo kujera gabanta yana kallonta,

“Inna yau zamu sallameki.”

Tayi kamar zatayi kuka.

“Ku taimakeni dan Allah. Bana son komawa gidan can wahala nake sha, babu abinci.”

Ya tsura mata idanunsa yana wani tunani.

“Kiyi hakuri dole zamu sallameki. Amma zamu cigaba da kawo maki tallafi.”

Ta dinga yi masa godiya tana saka masa albarka.

Kowane albarka daya idan ta saka masa, sai yaji wani irin sanyi a zuciyarsa.

Haka ya rubuta mata sallama sannan ya saka aka maidata gida.

A ranar wuni yayi cikin dogon tunani. Kaiwa yake yana komowa a ofis dinsa.

“Hello Najib.”

“Na’am Dokto ya aikin?”

“Amm… Lafiya lau. Please ina bukatar jinin Alhaji Bako, for DNA test!”

Ya jinjina kai,

“Ok. Zan saka a diba sai ka gaya mini inda za a kawo maka. Dazu ma mun hadu da shi, yake ce min kana da taurin kai.”

Kit! Ya katse wayar. Bayason jin abinda ya shafe shi.

<< Miskilin Namiji 4Miskilin Namiji 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×