Skip to content
Part 8 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

“Samha ke ce karama. Ina so ki dinga ba ta girmanta. Banason fada a gidana. Idan na sami daya daga cikinku da canza min maganata zan dauki matakin da sai kunyi mamakina.”

Ya danyi shiru kamar mai tunanin abinda zai ce, sannan ya cigaba

“Samha zata fara girkinta har sai tayi kwanaki bakwai kamar yadda yake, idan budurwa ce sati daya. Sannan sati mai zuwa zata tare a wancan bangaren. Ita na saka a gyarawa saboda tafi son qasa. Ba aure zan kara ba, kamar yadda kike tunani.”

Sakina ta danyi ajiyar zuciya. Amma kuma yadda Samha tace a dawo da ita qasa, tana da tabbacin akwai abinda take da burin aikatawa ne. Ya zama dole ta sake yin takatsantsar da yarinyar nan.

“Ku shirya anjima da daddare zan kaiku gidanmu zaku je ku duba mahaifiyata ba ta da lafiya.”

Jin an ambaci mahaifiya yasa idanun Samha ya kawo ruwa. Kallo daya yayi mata tayi saurin hadiye kukan.

“Samha mu je ki tara min ruwan wanka.”

Sakina ta sake sunkuyar da kai tana jin daci a zuciyarta. Addu’a take yi kada ta kashe Samha. Ta tsaneta fiye da yadda ta tsani kowa. Yau agabanta saboda cin fuska mijinta yake cewa wata su je a hada masa ruwan wanka. Ba zata mance wannan cin fuskar ba. Samha ce a baya, sai da suka kusa shigewa sannan ta waiwayo suka hada idanu. Daman tasan su take kallo. Samha ta sakar mata murmushin cin nasara sannan ta shige. Tana shiga ta dinga bin ko ina da kallo kamar wata ‘yar kauye.

Bai jira ta hada masa ruwan ba, kamar yadda ya bukata, da kansa ya shige ya sakarwa kansa ruwa.

Da karambani Samha ta gano inda yake ajiye zannuwan gadonsa, ta cire na kai ta shimfida sabo. Kafin ya fito har ta tattare komai ta gyara. Tana son zuwa sama ta dauko turaren wuta, amma dai ta bari sai anjima. Wannan karatun Dr Rahama ce. Ita ta gaya mata ta dinga tsaftace komai nasa.

Yana fitowa ya dinga kallon kan gadon yana murmushi.

“Na gode Samha.”

Ya yi maganar yana cigaba da goge kansa. Ta kasa kallonsa saboda yadda ya fito. Ba ta taba ganin namiji a hakan ba, shiyasa abin yayi mata wani iri.

Har ya gama kintsawa sannan ya hau gado ya kwanta. Tunani ne kala-kala a cikin zuciyarsa.

“Samha zaki iya taimaka mini da tausa?”

Ta dan yi shiru. A hankali ta ce,

“Kayi alkawarin ba zaka yi mini komai ba ko?”

Ya ware idanunsa da suka yi masa nauyi.

“Ba mun gama maganar nan ba Samha? Ko kina tunanin bazan iya ba? Ki cire komai a ranki, ki daukeni tamkar wani babban wa agareki. Babban fatana kiyi mini aikin da na kawoki kiyi.”

Ta saki ajiyar zuciya, sannan ta karaso tana danna kyawawan kafafunsa dogaye. Kafafun babu wata alama ta datti akai.

Yadda take yi masa tausan yana ratsa shi har cikin kwakwalwa. Zai so yarinyar nan ta taimake shi ta kwanta kusa da shi su yi barci. Duk da har yanzu yasan babu kwayar sonta a zuciyarsa, ya zabi ya jawota jikinsa ne ta yadda zata iya sakin jiki ta yi masa aikinsa. Ya kula muddin yana mata mazurai tana da rawar kai, da kuma kafiya, aikinsa yana iya lalacewa.

Ji ta yi yana fitar da numfashi anatse alamun yayi barci. Ba ta daina tausar ba, dan ta kula yana jin dadin yadda take yi masa. Duk da ba tason ta fito ne, dan Sakina ta fashe.

Tana fitowa ta sameta kuwa ta cika ta yi tam! Kamar zata fashe. Ko kallonta ba ta yi ba.

“Yarinya bari dai ashanye zaqin amarcin. Nan zaki zo kina kai kararsa.”

Samha ta zabga mata harara sannan ta ce, “Idan na zama wawuya kenan ba.”

Sakina ta zare idanu,

“Au! Gaya maki yayi ina kai kaararsa gidansu? Kan uban can! Lallai Dokto.  Dama ance maza munafukai ne, musamman idan suka kara aure. Yanzu-yanzu daga shigarku har ya sanar da ke ina kai kararsa?”

Samha ta saki baki tana kallonta. Ahaka dai kamar mai wayo, ashe shashashace. Ta ja tsaki zata wuce. Sakina ta sha gabanta tana huci,

“Uban wa kike yiwa tsaki?”

Samha ta nade hannunta a kirji tana dubanta. Dama kwana biyu ba ta yi dambe ba.

“Uban wanda ya tsargu.”

Sakina ta zare idanu,

“Ubana kika ce? Ni kika zagarwa uba? Samha ni kika zaga? Yau sai kin ga gatana a gidan nan. Yau sai kin san kin taba mahaifina.”

Ta daga waya tana kururuwa,

“Hello Abba. Kazo yanzu dan Allah. Amaryar Dokto ce ta zageka. Abba mutanen nan kasheni za su yi.”

Duk abubuwan da Sakina take fada yana jinta. Domin hayaniyarta ce ya tashe shi.

Ya kasa sakkowa saboda yadda Samha ta gama kashe masa jiki. Ga kuma tunanin matakin da ya kamata ya dauka akan Sakina. Dama yasan ba zata taba bari a zauna lafiya ba.

Samha ta girgiza kai ta wuce zata shiga kitchen din kasa. Dan tana daga tsaye ta hango shi. Da sauri Sakina tasha gabanta,

“Wallahi baki isa ki shiga kitchen dinnan ba, ki bari har sai kindawo kasan sannan kike da izinin shiga. Kuma baki isa ki bar nan ba, har sai ubana ya zo kin maimaita zagin da kika yi min.”

Samha ta dai yi shiru wata zuciyar tana cewa tayi mata tsinannan duka ta gudu. Sunan mahaifiyarta da ya dawo mata cikin zuciya, yasa ta yi fatali da abinda zuciyarta ke sanar da ita. Zata jure tunda na dan lokaci ne. Amma ta yi rantsuwa ranar da Uncle Zayyad ya ba ta takardarta babu ko tantama sai ta rufe gidan ta zaneta, sannan zata gudu.

“Assalamu alaikum.”

Dukkansu suka kalli bakin kofar. samha ta kafeshi da idanunta tana jin kamar ta sanshi. Shima ita yake kallo.

“Ina mara kunyar da ta zageni?”

Sakina ta karasa jikinsa da gudu tana kuka.

“Abba gata can. Sun tsaneni ita da Dokto babu irin wulakanci da bayayi mini akanta. Yau kuma sunanka ta kira take zagi.”

Alhaji Bako da jikinsa yake tsuma saboda yadda masifa ke cinsa. Ya fara taku zai isa gareta yana cewa,

“Idan na dakeki sai inga uban waye gatanki a garin nan.”

Samha tana nan tsaye ko gezau ba ta yi ba.

Daga bayansa ya ji an ce,

“Wallahi ka daketa sai na saki diyarka saki uku, kuma in yi shari’a da kai. Nima in ga naku gatan..”

Alhaji Bako ya juyo a fusace yana duban Yadda Zayyad yake tsaye rungume da hannu yana kallon ikon Allah.

“Au haka kace?? To bari indaketa din in ga abinda ka isa kayi.”

Da gudu Sakina ta sha gaban mahaifinta, tana kuka tana cewa,

“Abba kayi hakuri ka kyale shi. Kayi hakuri Abba na yafe kawai.”

Zayyad ya karasa fitowa yana dubanta kamar ya shaketa,

“Dazun nan na gama ce maki banason rigima amma kika saka kafafu kika shure maganata. Sai ki bi mahaifinki ku tafi tare dan ba zaki zauna a gidan nan ba.”

Ya juya da nufin barin wurin, Samha ta mara masa baya.

“Zaka san ka tabani. Zan nuna maka ni Alhaji Bako ba irin wadanda ake wulakantawa a zauna lafiya bane.”

cak! Ta dakata da tafiyar da take yi. Kamar ance Zayyad ya waigo ya kalleta yadda ta dafe kirji ta kuma juya tana kallonsa. Sannan ta sake juyowa da sauri jikinta yana bari ta ce,

“Alhaji Bako? Dama shine Alhaji Bako? Na shiga uku! Mahaifiyata tana wurinsa kenan.”

Ta juya da sauri da nufin isowa wurin da yake yiwa diyarsa tsawa akan tazo su wuce bai yarda ta koma ta dauko komai ba.

Ji ta yi anrike mata hannu. Tanaso ta yi masa tirjiya ya dubeta cike da bacin rai. Yadda taga yanayinsa babu wasa ne ya sanyata saurin cigaba da tafiya.

Alhaji Bako ya cigaba da masifa yana kumfar baki. Da kyar Sakina ta yarda ta bi bayansa.

Samha kuma ta dawo falon bayan ta tabba tar da sun tafi. Ta zauna a falon tare da yin tagumi. Duk jikinta yayi sanyi. Ba taso ya kori matarsa akan wannan maganar ba. Tana tsoron ace daga zuwanta har ta kori matar gida. Amma kuma tunanin Alhaji Bako ya fi tsaya mata a rai. Ta ji takaicin yadda Uncle Zayyad yayi mata. Taso ta shake shi sai ta ji inda yakai mata mahaifiya. Domin kuwa Uncle Zayyad da kansa ya tabba tar mata da shi ya dauke mata mahaifiya. Dole zata bibiyi rayuwarsa, dole zata gano shi din waye sannan ta tona masa asiri. Hawaye kaca-kaca a fuskarta. Ta sake tsanar Sakina da ta fito daga tsatsonsa. Ta sake jin tabbas indai akan Alhaji Bako ne zata bashi hadin kai.

Tana nan zaune ya sake fitowa yana daura agogo.

“Ki je kiyi Sallah sai ki shirya mu je gidanmu.”

Yadda taga fuskarsa a daure ya sake firgitata. Da sauri ta tashi har tana tuntube. Bai kalleta ba, bare ta saka ran ya ce ta bi a hankali. Da gudu ta karasa saman tana haki. A gurguje tayi alwalan Ta sallaci magriba, sannan ta dauko wani leshinta da anti Rahama ta ce mata duk ranar da za su je gidan surukai shi zata saka.

Tayi kyau sosai, duk da ba ta yi kwalliyan zo a gani ba. Katon gyalenta ta yane kanta da shi.

“Ke Samha! Fito mana.”

Kakkausar muryarsa ta ji yana kwala mata kira. Da gudun gaske ta kwasa tana hardewa, kasancewar ba ta wani kware a daurin zani ba.

A kasa ta karasa saka dankunnenta ta saka takalmin. Sau daya ya kalleta ya kauda kai.

Har sun kai bakin kofa ta yi magana cikin sanyin murya,

“Uncle…”

Ya dawo da baya yana kallonta, domin kiran ya shige shi sosai.

“Kayi hakuri dan Allah.”

Ita kanta tayi mamakin dalilin da zai sa kawai ta bashi hakuri.

Bai ce mata komai ba, ya fito yana tunanin menene a tsakanin Alhaji Bako da su Samha?

Yayi mamakin wai Samha ba tasan ma waye Alhaji Bakon ba, sai dai sunansa a bakinta kamar me? Ta haddace sunansa ne saboda yawaita kiran da mahaifiyarta take yi masa.

Da kansa ya rufe gidan, ya mika mata key ta karba. Bayan sun shiga mota ne, yana jinta tana addu’a, sai a lokacin ya tuna, shima yayi. Yana sane da yadda yake wasa da ibadansa. Mai gadi ya wangale masa gate, sai dai bai fita da motar ba, ya tsaya daidai yadda zai iya magana da shi. Duk yadda ya tsuguna yake gaida shi hakan bai saka ya amsa ba.

“Kai ban hanaka barin Alhaji Bala shigo mini cikin gida ba? Ban gaya maka duk ranar da ya sake shigowa a bakin aikinka ba?”

Bakinsa yana rawa ya sake zubewa yana cewa,

“Kayi mini aikin gafara. Na hanashi shiga ya kwada mini mari. Ya cire babbar riga wai sai dai mu daku. Shiyasa na hakura ya shiga. Dama nace zanyi maka bayani idan ka fito. Ka gafarceni yallabai idan ka koreni bansan ina zanje har a mutuntani kamar yadda kake yi ba.”

Zayyad yana shirin sake yin magana, yaji tattausar hannunta abisa nashi. Ya dago suka dubi juna, da sauri ta janye idanunta saboda kwarjininsa. Baisan lokacin da ya hadiye abinda yake shirin furtawa ba. Ya ja motar suka bar gidan.

A hanya ya tsaya yayiwa mahaifiyarsa siyayyan kayan marmari da kaji da kayan sanyi. Duk da yasan akwai a gidan, amma wannan na musamman ne. Da yawan lokuta idan zai shiga gidansu sai yayi masu tsarabar kayan kwalama.

Bayan sun shigo gate din gidan ya ba ta ledoji biyu ya ce ta rike. Suna tafe kamar kurame. Sai yanzu ya kula da motar Alhaji Bala. Ya ja ya tsaya cak! Zuciyarsa tana gaya masa kawai ya koma. Ita kanta har ta gaji da tsayuwar, dan ba tasan me ya tsayar da shi ba.

Sai kuma ya cigaba da tafiya. Sallama suka yi a tare sannan suka shiga.

Sakina ce sai Sharifat da Abba da kuma Umma. Sai Alhaji Bala da ke zaune yana karkada kafafu.

Da Zayyad da Samha duk suka zube kasa suna gaida su Abba. Sai can Samha ta dan saci kallon Umma ta ce,

“Umma ya karfin jikin?”

Umman ta dago tana dubanta. A zuciyarta ta ce,

‘Masha Allah. Yanzu kasan kayi aure Zayyad. Kyawunka da zatinka ya wuce a kalli Sakina a ce wai ita ce matarka.’

“Jiki Alhamdulillah Samha. Ya wurin su iyayen naki?”

Ta dago ta dubi Zayyad, ya sake hade rai, da sauri ta ce,

“Suna nan lafiya. Sun ce a gaidaki da jiki.”

Umma ta jinjina kai.

“Kai Zayyad! Me matarka ta yi maka ka koreta?”

Ya dago yana duban Abbansa. Sai kuma yayi shiru.

“Wanene Alhaji Bala a wurinka?”

Ya sake dagowa ya dan dubi Alhaji Balan, da ke aikin watsa masa mugun kallo.

“Baban matata.”

Abba ya gyara zama,

“Kuma shine ka raina shi haka? Wai Zayyad me ya shiga kanka ne? Anya kuwa baka fara shaye-shaye ba? Ni Zayyad dina da nasani mutum ne mai daraja babba da yaro. Don meyasa a yanzu zaka canza? Ka bashi hakuri ko kaga bacin raina.”

Ya dan shafi sumarsa sannan ya ce,

“Abba zuwa yayi wai zai daki Samha, saboda sun dan sami matsala da Sakina.”

Abban ya kalli Samha sannan ya ce,

“Au! Akan auren da kayi ne kake so ka canza rayuwarka? Indai akanta ne ya saka kake son raina manya yanzu sai in raba auren in ga karyar rawar kafa da rashin kunya.”

Samha ta ji kirjinta ya buga, tunda take ba ataba tozartata irin yau ba. Ta sake yin qasa da kanta. Sharifat ta yamutsa fuska ba ta ji dadin furucin Abbansu ba. Umma ma sai da ta cije labba saboda takaicin furucin Abban.

“Ke yarinya. Sakina yayarki ce, indai kina son zaman auren da gaske, dole ki bita. Dole kiyi mata biyayya. Banason shegantakar banza.”

Samha ta dago idanu jajir tanaso tace masa ita ba ta taba son dansa ba, ko yanzu ya sakashi ya saketa ya ba ta mahaifiyarta. Kamar Zayyad ya shiga zuciyarta, dan yasan halinta, muddin ka furta sai ta baka amsa. Karaf Allah ya karbi addu’arsa suka hada idanu a lokacin da bakinta yake motsi. Ya cusa idanunsa a cikin nata, sannan yayi mata wata alama da idanu. Hakan yasa abinda take son fada ya subuce a bakinta. Ta kasa furta komai. Sai kanta da ta mayar kasa tana kukanta ahankali. Sakina ta murguda baki ta ce,

“Wai fa akan ya gaya mata cewa ni ina yawan kai kara wurinku ne, shine tana fitowa tayi min gori wai ni shashasha ce, tunda ina yawan kai kara wurinku.”

Da sauri Zayyad ya dago ya dubeta. Tsantsar mamaki ya kama shi. Bashi da lokacin yiwa wata bayani.

“Au! Kai kake hadasu fadan ashe?”

Abba yayi tambayar a fusace. Zayyad ya girgiza kai,

“Tunda Samha tazo gidan nan ban taba maganar Sakina da ita ba. Gata nan ka tambayeta.”

Yana maganar kamar ansaka shi dole sai yayi. Ransa yayi mugun baci. Ji yake yana neman wanke ladansa ta hanyar yin danasanin zuwansa.

Dakin kowa yayi shiru. Abba ya gamsu da maganar Zayyad dan yasan mutum ne da baya karya, baya kuma zama inuwa daya da makaryaci. Ita kanta Sakina jikinta yayi sanyi. Tasan mijinta baya kare kansa da inuwar qarya.

Abba ya dawo da dubansa kan Zayyad,

“To naji. Yanzu zaka ba Alhaji Bako hakuri ko ba zaka bashi ba?”

Zayyad ya kaskantar da kansa ya ce,

“Kayi hakuri Alhaji.”

Sai yanzu Alhaji Bako yayi magana,

“Kai Salisu kana zaune da yaronka ne amma bakasan halinsa ba. Hakurinsa din banza! Hakurin da zai bada agabanka a bayan idanunka ya ninka wulakancinsa. Wallahi muddin ya sake shiga gonata sai na baku mamaki da ga kai har shi. Domin dukkanku a tafin hannuna kuke.”

Ya fice fuuu yana cewa

“Ke Sakina tashi mu je.”

Abba ma ya mike yana rawar jiki,

“A’a ka bar Sakina anan zata koma gidanta da mijinta. Mu je daga waje Alhaji.”

<< Miskilin Namiji 7Miskilin Namiji 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×