Skip to content
Part 10 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Haka M.Y ya kwana yana barcin asara, ko neman su Gwaggo bai yi ba bare yasan sun kai ko ba su kai ba. A karo na farko da Salloli suka hau kansa. Da ƙyar ya ware idanunsa yana jin kansa ya yi masa nauyi.

Ya jima yana zaune riƙe da kansa, sannan komai ya shiga dawo masa kai. Tunawa da Gwaggo yasa ya yi saurin jawo wayarsa yana dubawa. Kiran Gwaggo yafi na kowa yawa a cikin wayar. Matansa kowa kowacce ta yi masa kira bibbiyu.

Tsoron ƙaryar da zai yi wa Gwaggo ya fi komai ɗaga masa hankali. Har ya danna lambarta bai san me zai ce mata ba.

“Gwaggo ki yafe min.”

Abin da bakinsa ya iya furtawa kenan cikin rashin sukuni. Gwaggo ta sharce hawayenta jikinta babu inda baya rawa,

“Babban mutum kana cikin ƙoshin lafiya? Sanar da ni halin da kake ciki.”

Tausayinta ya karyo masa. Tabbas da ya kasance mai saurin kuka da babu abinda zai hana shi zubar da hawayensa akan mahaifiyarsa. Bai taɓa ganin uwa irinta ba, sai dai cikin rashin sa’a bai taɓa ganin ɗa mai son Zuciya irinsa ba.

“Gwaggo ina sonki, Gwaggo zanyi komai dan inga na faranta maki. Kada ki dinga zubar da hawayenki saboda ɗanki, koda hawayen na farin ciki ne yakan zame mani gobara. Kiyi wa marayan Allah dariya ko zai ga haske.”

A yadda yake maganar, dole duk wani mai saurin kuka ya kauce daga wurin, saboda tsananin tausayi.

Gwaggo ta goge hawayen da sauri, tana janyo murmushi bisa fuskarta.

“Allah ya yi maka albarka. Yanzu ka gaya min me ya faru tun jiya baka ɗaukar waya.”

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin natsuwa,

“Wayar ce na manceta a gida na kulle ƙofa, kuma anyi min kiran gaggawa agun aiki. Sai yanzu na dawo gidan. Amma baku kira su Amina ba?”

Ta ɗan jinjina kai,

“Mun kirasu suka ce suna ganin wani aikin kake yi.”

Ya ji daɗi da abin da iyalansa suka ce. Ita kuwa Husna tagumi ta yi kawai tana duban Gwaggo. Dole Gwaggo taso M.Y saboda shikenan gareta. Hira suke yi, wanda rabinsa duk  nasiha ce akan rayuwar duniya. Bayan sun gama wayar ya kira matansa ya tabbatar masu yana tafe insha Allahu.

Jamilu ya shigo ɗakin yana dubansa,

“Abokina yanzu ya kake ji?”

M.Y ya ɗan dube shi,

“Naji daɗi sosai, musamman barcin da na yi. Sai dai inda zaka gane ƙwaya masifa ce, ka ga ya fara shiga tsakanina da Mahaliccina. Bari inyi Sallah.”

Jamilu ya ji daɗin yadda yaga M.Y ya wartsake don haka ya bar ɗakin yana murmushi. Wanka ya fara yi sannan ya gabatar da Sallolinsa. Yana fitowa ya sami abinci, ya sani Jamilu zai sa a kawo masa. Cikin ikon Allah cikinsa ya buɗe ya ci abincin sosai, sannan ya fito sanye da baƙin wando da farin riga mai yankakken hannu.

Tafiya yake yi yana jin wani abu acan ƙasar zuciyarsa. Akwai mutumin da yake so ya kashe da hannayensa, sai dai tun ranar ya kwatanta yin hakan ya kasa.

Wani ɓangare na zuciyarsa ya zuƙo masa munanan kalaman Gwaggo akan wanda ya aikatawa Husna wannan aika-aika. A hankali ya furzar da huci ya ce a bayyane,

“Ni kaina ba zan taɓa yafewa ba. Zan nemo hukunci mafi muni in aikatawa K…”

“M.Y”

Ya ji anƙwala masa kira. Ya juyo ba tare da ya ƙarasa abin da yake son cewa ba. Kallonsa yake yi kamar baƙin maciji a gabansa. Shi ne mafi munin mutumin da ba zai taɓa ɗagawa ƙafafu ba. A hankali Nasir ya ƙara so gabansa yana dubansa,

“M.Y naga kamar kana gaba dani ne. Don Allah ka…”

Da sauri ya ɗaga hannunsa,

“Idan baka bar wurin nan ba, ina tabbatar maka zaka zama gawa na farko da zan ɗauke numfashinsa ina mai farin ciki. Jeka kawai jeka.”

Yasa hannayensa biyu yana ture shi, har sai da ya yi masa wani irin ingiza sai gashi daɓas! A ƙasa. Da sauri M.Y ya bar wurin ya wuce ciki jikinsa har yana rawa, ya ɗauki key ɗin motarsa da nufin barin wurin.

“Ka zo Oga Saleh yana nemanka.”

Cak! Ya dakata da ƙoƙarin buɗe motar da yake yi. Idan akwai sunan wanda ya tsani ya ji a yanzu bai wuce Oga Saleh ba. Zai yi magana Jamilu ya girgiza masa kai, dole ya juya kawai suka kama hanyar sashen Ogan.

‘Yan mata ne kewaye da shi, wanda ba baƙi bane a cikin wannan gida, kasancewar watarana da su ake fita, ko kuma a haɗa baki da su wajen sace manyan mutane musamman masu neman mata.

Haka zalika ayyukansu yana da yawa a cikin gidan, domin kuwa mazan gidan sukan rage dare da kowaccensu, duk da ta Oga Saleh daban take a wurin anfi ji da ita ma sosai.

Tsaye ya yi yana kallon wani wuri.

“Yanzu M.Y kullum sai ka ɓata min rai kenan? Ka bini a hankali kada watarana ka tunzurani har mahaifiyarka ta…”

Shi kansa bai san lokacin da ya shaƙo wuyan rigar Ogan ba, yana wani irin huci. Duk rashin tsoro irin na Oga Saleh sai da ya firgita da yanayin M.Y. Bare kuma yaransu da ke kewaye da su.

“Idan ka sake ambatar sunan mahaifiyata sai na datse harshenka.  Kasan wacece mahaifiyata a gareni? Ita ce rayuwata, ita ce farin cikina. Duk mai yunƙurin ƙuntata mata, zan iya ganin bayansa ko waye. Idan nace ko waye ina nufin har mahaifina zan iya kashe shi muddin ya ce zai takura mata. Bare kuma kai!”

Ya faɗa da ɗan tsawa. A lokaci guda kuma ya hankaɗa shi ya faɗa kujera. M.Y ya sharce gumin kansa yana dubansu ɗaya bayan ɗaya,

“Kaf gidan nan babu wanda yake yi maku aiki irin wanda nake yi maku. Da ba dan ni ba da tuni ‘yan sanda sun antarwatsa ƙungiyar nan. Amma na tsaya maku. Ɗan adam mai saurin mantuwa yau ni kuke yi wa barazana da abin da na fi so a duniya. Yau ni kuke son tsomawa a cikin matsala.

“Kunsan wacece Gwaggo a wurina? Gwaggo ta yi min reno irin wanda ko kwanciya zanyi tana takani ba zan taɓa biyanta ba. Na yi ciwo irin wanda kowa ya gujemu muka koma rayuwa a kango, ina wari ina fitar da tsutsotsi a jikina amma haka Gwaggo zata rungumeni tana kuka. Da mai magani ya ce ta dinga yin nesa da ni, saboda warin da nake yi zata iya kamuwa da cuta kusan me Gwaggo ta ce? Cewa ta yi ta ji ana faɗin ina wari amma ita bata taɓa jin warin ba. Don haka kada a sake bata shawarar yin nesa da gudan jininta.”

Ya ƙarashe yana jin wani irin zazzaɓi yana shigarsa. Bakinsa yana rawa. Da zaka ƙura masa idanu sai ka hango hawaye maƙale a gefen idanunsa. Durƙushewa ƙasa ya yi ya dubi Oga Saleh ya ce,

“Wannan kaɗan ne daga irin abin da Gwaggo ta yi wa ɗan da ya zama dalilin saɓa mata. Ɗan da yake jawo mata dukkan abubuwan da ake yi. Duk da haka ba zaku ƙyale Gwaggo ba? Duk da haka ba zaku barta baƙin cikin mutuwar mijinta ya zama ajalinta ba? Sai kun ƙara mata da baƙin cikin mutumin da tafi yarda da shi fiye da kanta? Nayi alƙawarin duk wanda ya zama dalilin sake ɓatawa uwana rai, sai na bi kaf zuri’arsu na kashe Wallahi!”

Ya miƙe a fusace ya bar gabansu. Gaba ɗaya jikinsu ya yi matuƙar yin sanyi. Jamilu kuwa hawaye ne kwance a fuskarsa yana girgiza kai,

“Oga da gaske ba a kyautawa M.Y. yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen kyautata maku, amma ku kam kullum burinku ku ƙuntata masa. Zai fi kyau a daina yi masa barazana da mahaifiyarsa, abar matar nan don Allah. Ina da tabbacin duk ranar da tasan aikin ɗanta zata iya haɗiyar zuciya ta mutu. Ta ɗora soyayyar duniyar nan akan ɗanta ku barshi ya sarara.”

Oga Saleh ya yi magana cikin damuwa,

“Muna yi masa hakane saboda kada watarana ya ce zai gujemu.”

“Ya taɓa yunƙurin barinku ɗinne? Bana jin M.Y zai gujemu gaskiya.”

*****

A yau Husna take kammala Istibra’inta wanda dama shi suke jira shiyasa ake ta ɗaga bikin musamman ma yadda jinin hailanta ya dinga yi mata wasa.

A natse take ninke kayan sawanta tana jin yadda su Gwaggo suke hira da Salma cikin kwanciyar hankali akan biki da ke matsowa.

“Ke Salma jiya munyi magana da Babban mutum, ya ce ba zai bari kiyi nisa da ni sosai ba, ita kuma Husna bayan anɗaura auren da sati biyu haka mijinta zai dawo da ita garin Kaduna, saboda aikinsa ya koma can ɗin.”

Husna ta tsani hirar bikin nan wanda kullum sai Gwaggo ta yi, bata gajiya da maimaita maganar auren. Haka kullum sai ta yi masu nasiha irin wanda ke ratsa jiki.

Shirye-shirye ya yi nisa, babu angwayen guda biyu. Acan Kaduna kuwa M.Y ya ga tashin hankali irin wanda bai taɓa gani ba a cikin gidansa. Gaba ɗaya sun haɗe masa kai, sun tashi hankalinsa akan maganar auren nan. Abubuwan sun yi masa yawa, ga wani irin asara da yake yi na kuɗaɗe abin har yana bashi tsoro. Salima ta fi ɗan kauda kanta, ita kuwa Bilki ji take yi kamar ba a taɓa yi mata kishiya mai zafin wacce za a kawo ba. A lokacin kowacce ta miƙe da neman sa’a agun bokanta, dan kowacce ta je gun malaminta, magana ɗaya suke yi masu,

“Ku bi a hankali akan yarinyar da za a auro idan ba haka ba, kuna ji kuna gani zaman gidan mijin zai gagareku.”

Waɗannan kalaman sun ƙara tada hankulansu.

Ana gobe biki M.Y ya dira a Gombe da shi da abokansa harda Jamilu.

Husna tana ɗaki ta yi tagumi tana jin damuwa danƙare a zuciyarta. Idan ta tuna anrabata da budurcinta sai ta fashe da kuka tana mugayen kalamai akan wanda ya yi mata wannan aikin.

Gwaggo ta ƙwala mata kira, ta fito tana dubanta,

“Maza ɗauki furar nan ki je ki kaiwa Yayanku da mutanansa.”

Bata ce komai ba, ta ƙarasa ciki da Sallama. A lokacin ta ci nasarar jin hirarsu,

“M.Y ka nemi maganin ƙarfin maza kasan matan yanzu idanunsu a soye yake.”

M.Y ya yamutsa fuska,

“Ni me zan yi da ita? Wannan ai sai inkaryata. Wallahi saboda infaranta ran Gwaggo zan aureta. Tausayin da take bani, shi ne kishi da zata yi da su Bilki. Ban taɓa ganin mata irin su ba. Ni dama ba zata taɓa samuna a matsayin miji ba, ta yi min ƙanƙanta. Zan reneta ne idan ta ƙara girma inlallaɓa Gwaggo in saketa in aura mata wani. Kuma Allah na tuba ko tsofaffin matana bana shan masu maganin maza, saboda Allah ya bani lafiya.”

Duk suka fasa dariya, shi kuwa da ya hango Husna gaba ɗaya sai ya shiga addu’ar Allah yasa bata ji ba.

“Lafiya kika tsaya anan?”

Duk suka dawo da dubansu kanta. Ɗaya daga cikinsu ya ce,

“Au ita ce amaryar?”

Daga shi har ita aka rasa wanda zai yi magana. Ta ƙaraso ta ajiye masu furar ta gaidasu sannan ta wuce jikinta yana kyarma. Ta yaya zata gayawa Gwaggo kada ta kai Salma inda rayuwarta zata gurgunce? Babu soyayyar miji ga tashin hankalin kishiyoyi.

A daren ta kasa koda rintsawa. Sai juye-juye take yi.

Washegari da misalin ƙarfe goma sha ɗaya aka ɗaura aurarrakin biyu cike da dumbin albarka da kuma tarihi.

M.Y ya saki sassanyar ajiyar zuciya wanda ba zai ce ga dalilinsa ba, ko kuma ince ya bar dalilin acan ƙasar zuciyarsa. Lumshe idanunsa ya dinga yi yana jin hayaniyar abokansa ko alama basu da wata damuwa. Yanzu yake jinsa cikakken namiji tunda har ya ajiye mata huɗu. Wata zuciyar ta ce da shi,

‘Amma babu adalci.’

Ya yi saurin kawar da tunanin ya tashi kawai ya fito waje yana duban mutane yadda suke ta walwala abin su.

Kabiru ya ƙaraso yasha manyan kayansa ya miƙawa Mu’azzam hannu,

“Ina tayaka murna.”

M.Y ya miƙa masa nasa, fuskarsa a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba. Ya dubi Husna dake tsaye tasha lulluɓinta da alamun shi ya aika a kirata domin su ɗan gana. Ya ce,

“Husna shiga gida.”

Babu musu ta shiga gida. Kabiru kuwa ya sake yashe baki ya ce,

“Allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin matanka.”

Ya jinjina kai,

“Tare da kai. Kaima ina tayaka murna.”

Gwaggo suka gani ta ƙaraso kawai ta rungume Mu’azzam tana jin kamar bai taɓa faranta mata irin yau ba.

“Allah ya yi maka albarka babban mutum. Baka taɓa yin musu da ni ba. Dukkanku marayu ne kuma kunyi min halacci.”

Kawai ta fashe da kuka mai cin rai tana tuna rayuwarta a baya.

Ganin zata jawo hankalin jama’a yasa ya kamo hannunta suka shiga ciki.

<< Mu’azzam 9Mu’azzam 11 >>

1 thought on “Mu’azzam 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×