Ya fahimci me take nufi, sai dai ko a fuska bai nuna mata komai ba, ya shige banɗaki. A ciki ya shirya ya yi komai sannan ya fito ya wuce Masallaci. Jikinta asanyaye ta shiga ta yi alwala ta fito tana nazarin Gabas.
Duk yadda taso ta rintse idanu ta yi barci abin ya faskara. Gani take yi tana rufe idanu wani abu zai cutar da ita. Ga shi dare yana ƙara tsalawa babu idon M.Y don haka ta sake rintse idanunta ta fara rera kuka,
“Gwaggona ki zo ki taimakeni, Gwaggo wanda kike so kika yarda da shi ya kawoni inda za a kasheni.”
Kamar ance ta ɗan buɗe idanunta, ta ganshi zaune a gefen gadon ya kafeta da idanu kamar mai dogon tunani. Da gaske ta bashi tausayi, domin bata fara kuka ba tukun yanzu dai zata fara.
Ƙanƙame jikinta ta sake yi tana jin kamar shi kansa cutar da ita zai yi. Bai ce komai ba yasa hannu da ninyar ɗaukan filo, anan ya ɗan taɓa jikinta ai sai ta zabura ta na ninyar guduwa, jikinta babu inda baya kyarma.
Wani abu ya tsaya masa a wuya, ji ya yi kamar ya shaƙeta. A ciki-ciki ya ja tsaki ya ɗauki filon ya jefa a ƙasa ya yi kwanciyarsa. Sai kuma ta yi shiru tana dubansa. Tana son ta ce masa ya koma gado ta dawo ƙasa, tana tsoronsa. Dole ta koma ta kwanta. Sai dai ta kasa barcin kamar yadda shima ya kasa barci.
A hankali ta sakko bata san yana jinta ba, ta tofa masa addu’a ta koma ta kwantar da kanta shiru. Abin ya bashi mamaki da al’ajabi.
‘Me ya sa ta yi min addu’a?’
Ya tambayi kansa. Tunawa da tarbiyya irin na Gwaggo yasa ya sauke ajiyar zuciya. Tabbas duk wanda ya rayu da Gwaggo bai ɗauki tarbiyya ba, babu ko shakka mara rabo ne, kamar yadda yake yawan kiran kansa.
Sai da ya gama tabbatar da ta yi barci sannan ya tashi ya buɗe jakarsa ya ciro ƙwaya wanda daman da guzurinsa. Idan bai sha ba yana jin tashin hankali ba zai barshi yin barci ba.
Har zai zuba a bakinsa, suka haɗa idanu da Husna. Sosai ta kafe shi da ido tana al’ajabin menene wannan kuma zai sha da daddare? Tunaninta ya tsaya ne ko dai bai da lafiya? Ko kuma maganin ciwon kai.
Wani irin kunyarta ne ya kama shi, wanda tunda yake bai taɓa jin hakan ba akan wata ‘ya mace. Yarinya ƙarama ta yi masa kwarjini. Dole ya sauke ƙwayar ya rufe yana jin lallai yarinyar nan ta takura masa.
Komawa ya yi ya kwanta yana ta juye-juye. Allah Allah yake gari ya waye. Husna kuwa tashi zaune ta yi, ta ɗauki Alqur’aninta ta fara karantawa cikin suratul Rahman.
A yadda take raira karatun cikin fidda Tajwid dole abin ya burgeka. Tana baiwa komai hakkinsa ba tare da ta tauye ba. Wannan karatu shi ya taimake shi ya sami barci mai daɗi irin wanda yake rasawa sai tare da ƙwaya.
Bayan ta dire ne ta kula da abin rufansa ya yaye, ya ƙudundune ta tashi a hankali ta gyara masa rufan sannan ta dawo ta kwanta shiru…
Yau ne karo na farko da zata yi barci babu Gwaggo a kusa da ita. Ta saba idan zata kwanta sai ta nannaɗe a jikin Gwaggo. Tun Gwaggo tana mita akan tana sanya mata ciwon jiki har ta koma itama ta saba idan babu Husna kusa barci bayayi mata daɗi. Yau ga aure ya raba su.
A hankali hawaye ya dinga tsiyaya a idanunta. Har aka kira Sallar asuba idanunta biyu bata yi barci ba. Sai bayan da ta yo alwala sannan ta bubbugi filonsa. Ya buɗe idanu yana mamakin yanzu-yanzu ya rufe idanu amma wai har gari ya waye.. Banɗaki ya shige ita kuma ta tayar da Sallah.
Yana fitowa daga banɗakin ya fice abinsa bata sake ganinsa ba, har aka kawo mata abincin kari, ta ɗan ci kaɗan ta ture.
Ya shigo a ɗan gurguje ya ce ta tashi za su wuce. Babu musu ta tashi ta tattara ‘yan tarkacenta shima ya tattara nasa suka bar ɗakin.
Sun kama hanya barci yana ƙoƙarin fin ƙarfinta amma ta dake ba zata yi ba, da yake ɓarawo ne ya kwasheta sai gata kwance a gefen kafaɗansa. Tunda ya ji zuciyarsa ta buga sau ɗaya, ya ɗan saci kallonta bai sake kallon inda take ba, ya ci gaba da tuƙinsa.
Bai san dalili ba da ya tsinci kansa da yin tuƙi a hankali, yana jin wani irin damuwa yana sake lulluɓe shi.
‘Nasir!’
Ya furta a zuciyarsa da ƙarfi,
‘Nasir! Oga Saleh!! Kun aikata kuskure mai girma, wanda bana tunanin ko zan yafewa kowa zan iya yafe maku. Kun dasa min ciwo wanda har abada ba zai warke ba. Da hannayena zan kasheku.’
Zancen zuci yake yi zuciyarsa tana tafarfasa. Yana tunanin tabbas wannan abin da suka yi masa shi ne ajalinsa idan bai yi wasa ba. A kullum ya kwanta tunani yake ta ina zai fara ɗaukar fansa?
Har suka shigo Gate ɗin gidansa bata farka ba. A wannan lokacin Salima ta yo rakiyar ƙawarta takai duba ga gaban motar, gabanta ya faɗi ras! Ganin wata kwance a gefen mijinta. Bilki tana jin tsayuwar motar itama ta fito, sai aka hau kallon kallo.
Shi kansa zaune yake shiru baya son ta tashi, domin a yanayinta ya fahimci bata sami barci ba a daren jiya. Idan ma zai tasheta ta yaya?
“Ke Husna!”
Ya kirata da ‘yar tsawa. Ta buɗe idanunta tare da addu’ar tashi barci, ta ƙara da Hamdala.
Ganin manyan giwaye a gabansu yasa ta juyo tana dubansa jikinta babu inda baya rawa.
“Don Allah Uncle kada ka gaya masu ni ka aura don Allah.”
Ya kasa cewa komai sai fitowa da ya yi bai dube su ba ya wuce falon daga nan ya cusa kai ɗakinsa yana jin wani irin ƙarni a falon kaman anyi ɓarin ƙwai. Husna ta ƙaraso ta gaida su, suka amsa babu yabo babu fallasa ta wuce falon kawai gabanta yana faɗiwa.
Duk suka bi bayanta, a inda ta ajiye akwatinta anan ta yi wa kanta mazauni. Salima ta kafeta da ido cike da mamaki,
“Ke kuma ina zaki je akwati?”
Sunkuyar da kai ta yi, ba tare da ta furta komai ba. Hakan yasa Salima da Bilki suka kalli juna suna sake ware idanu. Sai a lokacin Amina ta fito, itama sai ta yi turus tana duban Husna.
M.Y ya fito yana duban Husna ya ce,
“Ki tashi ki koma ɗakin can da kuka sauka kwanakin baya da Gwaggo. Idan na gyara maki ɓangarenki sai ki tare.”
Duk suka dube shi suka yi magana a tare,
“Sai ta tare fa ka ce?”
Bilki ta ɗora da cewa,
“Me kake nufi? Kayi mana bayani.”
A lokaci guda yaji tsoron da ke zuciyarsa ya kau. Kawai yana jin gara ya gaya masu ya ragewa kansa fargaba. Sai da ya taɓe baki sannan ya ce,
“Ita Gwaggo ta aura min ba Salma ba. Salma tana can da mijinta.”
Yana gama bayaninsa ya fice da sauri. Yana jin Bilki tana manya-manyan ashar bai ce komai ba, bai kuma dawo ba.
Amina kawai ta fashe da kuka, sai ta gwammace ya auri Salman fiye da Husna, kasancewar Husna tafi kowa iya laɓe tana jin sirrikansu. Duk suka rasa abin da za su yi mata sai kawai suka zuba mata idanu. Jikin Husna yana rawa ta ce,
“Don Allah kuyi haƙuri nima bansani ba sai…”
“Rufe mana baki munafuka! Duk duniya a rasa abin da za a ba M.Y a matsayin matar aure sai ragowar masu fyaɗe? Ragowar dajin hanyar Kaduna ce matar M.Y? To Wallahi ba zai yiwu ba, don babu wanda yasan irin cutan da suka zuba maki a jiki, azo a goga mana tsiya.”
Wannan munanan kalaman duk daga bakin Salima suke fitowa. Husna ta fasa kuka mai ciwo. Ashe haka mutane suke yin amfani da ƙaddara wajen yin gori? Ashe watarana zata zama abin ƙyama a idanun duniya? Ita kuwa yaushe zata iya yafewa wanda ya aikata mata wannan abu? Ya tafi ya barta da mummunan tabo, wanda ta sani har abada ba zai taɓa gogewa ba, idan ma ta haihu har ‘ya’yanta watarana sai anyi masu gori da abin da bata ji ba, bata gani ba.
Bilki ta yi tsalam ta ce,
“Rufewa mutane baki. Gwaggon nan yanzu na gama fahimtar bata da kishin nata. Ɗanta ɗaya jal! Zata ɗauka ta baiwa ragowar wani? To mu ba zamu yarda ba. Tashi ki fice ki tafi duk inda zaki je ko kuma yanzu jikinki ya gaya maki.”
Ji ta yi anɗauketa da mari mai tsananin shiga jiki. Gaba ɗaya sai ɗakin ya ɗauki shiru, sai Bilki da ke riƙe da kuncinta cikin gigicewa. Duk suka dubi mai marin. M.Y ne tsaye yana huci kamar tsohon soja. Bai ji kalaman Salima ba, kasancewar har ya shiga Mota da ninyar tafiya, sai kuma ya tuna ya bar Husna a cikin matsala. Shigowarsa kenan kunnensa suka jiyo masa munanan kalaman da Bilki take jifan ƙanwarsa da Gwaggonsa da su.
Nan da nan Salima ta dawo hayyacinta ta nemo natsuwa ta ɗorawa kanta. Ɗaga hannu ya sake yi da nufin sake wanketa da mari, ta yi saurin guduwa ta koma bayan Salima. Ita kuwa Salima muguwa ta dinga tureta alamun babu ruwanta.
“Gwaggo kike son ki zaga? Kinyi na ƙarshe Bilki! Kuma ita ƙaddara ba a gorinta, domin baki san me zai faru da ke yanzu ko anjima ba. Ke Husna tashi muje.”
Jikinta yana rawa ta tashi ta biyo bayansa ya kaita har cikin ɗakin da babu komai sai katifa, duk ya yi ƙura. Ya fito ya ƙwala wa mai aiki kira, ta zo jikinta yana kyarma. Ya ce su kaiwa Husna abinci da duk abubuwan da take buƙata. Ya dubi Amina ya ce,
“Ga amanar Husna a hannunki.”
Itama cikin tsoro ta gyaɗa kanta. Ya juyo ya nuna Bilki da hannu,
“Zan haɗu da ke.”
Ya sa kai ya fice yana jin komai yana sauya wurin zama a zuciyarsa. A yadda ya ga idanun Salima ya fahimci dole anjima yaje ya nuna mata shi ba son Husna yake yi ba, don ya kula tana tunanin tunda ya yi sabon aure matsayinta a zuciyarsa zai ragu ne, abin da bata sani ba, duk cikin matansa yafi sonta a ganinsa duk ta fi su hankali.
Wannan kenan…
Thanks