Bayan ya fice daga gidan Bilki ta dubi Salima jiki a sanyaye. Idan a girmene ta girmi Salima, amma kullum sai Salima ta nuna mata sabon makirci ta kasa fahimtarta.
Salima da ta kula da Bilki tana shirin ja baya da ita, sai ta dafa kafaɗanta ta ce,
"Ni yanzu M.Y tsoro yake bani. Da zarar mace ta yi masa abu sai ya ce zai daketa. Kema ina baki shawara ki daina barin yana magana kina tsayuwa kusa da shi. Yanzu dai menene abin yi? Dole mu zauna mu nemo mafita."
Amina ta zauna asanyaye, haka ma Bilkin. . .