Skip to content
Part 15 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Bayan ya fice daga gidan Bilki ta dubi Salima jiki a sanyaye. Idan a girmene ta girmi Salima, amma kullum sai Salima ta nuna mata sabon makirci ta kasa fahimtarta.

Salima da ta kula da Bilki tana shirin ja baya da ita, sai ta dafa kafaɗanta ta ce,

“Ni yanzu M.Y tsoro yake bani. Da zarar mace ta yi masa abu sai ya ce zai daketa. Kema ina baki shawara ki daina barin yana magana kina tsayuwa kusa da shi. Yanzu dai menene abin yi? Dole mu zauna mu nemo mafita.”

Amina ta zauna asanyaye, haka ma Bilkin ta nemi wuri ta zauna kamar wacce Salima ta rufewa baki.
Har ta ƙaraci kame-kamenta bata fito masu da mafita ba, har zuwa lokacin da Husna ta gaji da zaman yunwa ta fito domin samawa kanta abinda zata ci. Idanunsu ya sauka akanta sai duk suka ji ɓacin ransu ya ninku. Salima ta miƙe tana dubanta,

“Husna manya. Yanzu ai kin zama babba.”

Salima ta ƙyaftawa Bilki ido, aikuwa kamar jira take ta kama Husna da duka bata ji bata gani. Amina dai tana tsaye tana dubansu.

Babu abinda zai bayar da mamaki sama da ɓacewan Salima a wurin. Ita kaɗai ta hango M.Y a lokacin da shi kansa bai ganta ba. Kuka kawai Husna take yi tana basu haƙuri amma idanun Bilki ya rufe. Da sauri ya ƙwaceta daga hannun Bilki, sai a lokacin suka haɗa idanu. Bai ce komai ba ya jawo hannun Husna yana jin wani irin ɓacin rai. Gani yake kamar Husna ta fara zame masa kaya, wanda duk inda ya fita sai ya ji ya kasa samun natsuwa dole sai ya dawo gida. Yanzu gashi ya dawo ya tarar da wata matsalar.

Dubanta ya sake yi a karo na barkatai, yana jin mugun haushinta a zuciyarsa. Dole Salima zai kaiwa amanar Husna tunda ya kula Bilki shirin kasheta take yi.

A zuciyarsa ya gama tanadar irin wulakancin da zai yi wa Bilki, sai ta gwammace bata taɓa zama inuwa ɗaya da shi ba.

“Ke! Ki rufe min baki na tsani kuka, so ki daina damuna. Kin zame min damuwa, da alamun zaki kawo min nakasu a cikin aikina.”
Husna ta cusa hijabinta a baki tana kuka babu ƙaƙƙautawa. Gwaggo kawai take son gani, ita ɗaya ce zata goge mata hawaye. Yau shikenan ta tabbata marainiya.

Tsaki ya ja ya fice daga ɗakin kai tsaye kitchen ya Shiga ya rufe mai aikin da faɗa. A lokacin mai aikin ta ce masa Anti Salima ce ta hanata kai abincin. Ya dubeta ransa a ɓace kamar ya rufeta da duka. A ganinsa Bilki za ta ce ta yi suɓutan baki saboda ruɗewa.

Da plate ɗin abincin ya dawo ya ajiye a gabanta ya nemi wuri a gefen katifa ya zauna yana latsa waya. Idanunsa sun juye sun zama jazir saboda ɓacin rai. Ganin taƙi ɗauka yasa ya daka mata tsawan da babu shiri ta shiga cuccusa abincin. Sai da ya tabbatar ta cinye tas sannan ya miƙa mata ruwa ta sha. Addu’ar godiya ga Allah ta karanto duk da yadda kuka ke cinta tana dannewa.

Yana alfahari da mahaifiyarsa, a duk lokacin da yaga waɗanɗa ta ba tarbiyya sai ya ji farin ciki ya rufe shi.

*****

Kwana biyu kenan gidan ya zama kamar babu kowa, saboda irin fushin da M.Y ya ɗauka da kowa. Bilki ta fi shiga matsala saboda ko gaisuwarta baya amsawa. Ya daina basu Kuɗaɗensa, duk da gara Salima takan samu idan ta tambaya. A kwanaki biyun nan ko inda Husna take bai leƙo ba, hakan yasa zaman kaɗaici ya yi mata yawa. Ta yanke shawarar fara zama a cikin ‘yan aiki ko zata sami kwanciyar hankali.

A hankali a hankali Husna ta saba da ‘yan aikin, kusan tare suke aikin abincin gidan, duk da wani irin girki akeyi mara kan gado. Tunda Salima ta ƙyalla ido taga Husna a kitchen, shikenan ta zama baiwarsu. Hatta idan sun yi baƙi ita ke shiga ta dafa masu abinci, suna ci suna zaginta. Haka kawai sai Bilki ta kirata ta sanyata aikin matsa ƙafafu.

Wata ranar laraba, Husna tana kitchen suna ta aikinsu suna hira Salima ta kirata ɗakinta. Ta nuna mata hanɗakinta taje ta wanke saboda zatayi baƙi. A wannan lokacin anyi Sallar magrib. Tana shiga banɗakin ta toshe hanci saboda masifar ƙarni da zarni da yake yi. Ita kanta Husna ta kasa iya gyara gidan saboda girmansa da kuma irin yadda gidan ya ƙazance.

Ta cire hijabinta ta hau wankin bayi. Haka ta gama ta fito da ninyar ɗaukar hijabinta idanun Salima yakai kan dukiyar fulaninta. Kasancewar rigar da ta sanya babu nauyi dan haka ana iya hango su cikin riga. Wani irin sha’awarta ya shigeta, ta fizgota ta rungumeta jikinta har yana wani kyarma. Tunda Husna take bata taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba. Duk yadda taso ta ƙwace abin ya faskara, a haka ta kaita har gado. A lokacin ne Husna ta raramo abin da bata san ko menene ba, ta buga mata akai.

Salima ta yi wani ƙara ta riƙe wurin ta zube akan gadon. Jikin Husna ya kama rawa ganin yadda jini ke zuba akanta. Da gudu ta fice ta shiga ɗakinta ta rasa me zata ɗauka ta gudu ta bar gidan.

Saboda tsananin ruɗewa ta yi waje da gudu. A lokacin M.Y ya dawo yana shirin shigowa. Kamo kafaɗunta ya yi yana mamakin yadda duk ta sauya masa. Ta rame ta zama kamar ‘yar aikin da bata samun kulawa daga gidan da take zama.
“Ke lafiyarki kuwa? Jinin menene wannan a jikinki? Ina zaki je?”

A lokacin kuma ta ji muryar Salima a bayanta tana cewa,

“Ka riƙeta kada ka barta ta bar gidan nan sai na kaita wurin ‘yan sanda.”

Ganin Salima cikin jini ya ɗaga masa hankali. Ko ba ayi masa bayani ba, yasan Husna ce ta fasa mata kai. To amma ta yaya? Tunda yake bai taɓa jin ance wani daga cikin gidansu zai iya yin dambe ba, bare har akai ga fasa kai. Husna ta sake gigicewa jin ankira sunan ‘yan sanda, ta nemi guduwa tana ture M.Y da iya ƙarfinta.

Fizgo hannunta ya yi ya mayar da ita falon yana huci. Gaba ɗaya sai ta zube a falon tana kuka tana roƙonsu su rufa mata asiri su barta zata tafi ta bar rayuwarsu kada su haɗa ta da ɗan sanda.

M.Y ya tsareta da idanunsa yana dubanta,

“Me ya sa kika ji mata rauni?”

Bakinta na rawa zata yi magana, ta ji muryar Salima tana magana cikin kuka da rikicewa,

“Daga nace yarinyar nan ta taimaka bana jin daɗi ta wanke min banɗaki, kawai sai ta kama cewa ita ba baiwata ba ce. Bance mata komai ba har ta zo fita na dawo da ita nace sai ta gaya min wanda take zagi. Shikenan yarinyar nan ta ce wai insakar mata hannu ko ta yi min illa. A zatona wasa take yi min sai ta buga min abu akai bansan ko menene ta ɗauko ba.”

Bilki da Amina suka kalli juna. Dole duk wani mai hankali ya yi nazarin wannan maganar. Kowa yasan Husna ba mai son hayaniya ba ce, dama ace takwararta ce ansan zata yi abin da ya fi hakan.

Babu zato M.Y ya rufe Husna da duka kamar zai kasheta. Tun tana kuka tana roƙonsa, har ta yi shiru tana sauraren irin dukan da yake yi mata. Wani duka da ya kai mata a baya ta fasa ƙara wanda hatta shi kansa sai da ya gigice. A lokacin ya tuna Husna ƙaramar yarinya ce kuma amanar Gwaggo, ita yake yi wa haka? Sakin Belt ɗin ya yi, gaba ɗaya ya haukace ya rasa me zai yi. Da sauri ya kama hannun Salima suka fice zuwa wani ƙaramin asibiti dan a duba kan.

Bilki ta tuntsure da dariya, ta ce

“Shegiya mayya! Salima ce maganinki a cikin gidan nan da ni kike zance.”

Duk suka wuce babu tausayawa.

Anan ta gaji da kukan babu mataimaki sai Allah ta ja jikinta ta shige ɗakinta ta rufe ƙofar.

Bayan ya dawo ne ya ce Salima ta je ta kwanta ta huta, ya dawo falo ya zauna. Gaba ɗaya ya rasa me ke yi masa daɗi. Ya miƙe da nufin shiga ɗakin Husna, ya ji shi a rufe gam! Ya ƙwanƙwasa shiru. Ya yi ta masifa yana bugun ƙofar amma tsananin tsoro ya hanata buɗewa.

Ta gigice da yawa, tunda take ko faɗa Gwaggo bata yi mata sai dai nasiha, bare akai ga duka. Sai gashi yau akan gaskiyarta anduketa har anji mata ciwo. Ta ƙara fasa kuka tana roƙon Allah ya ɗauki ranta ta huta.

A dogon kujera ya koma ya kwanta yana jin zuciyarsa babu daɗi. Bai yi Sallar isha’i ba dole ya rarrafa ya shiga ɗakinsa dan baya jin zai iya sake fita.

Washegari ya sake buga ƙofarta a rufe, ya fice ya dawo da rana bata buɗe ba, da yamma shiru. Anan kuma sai hankalinsa ya ƙara tashi. Babu shiri ya nemo ɗayan key ɗin ɗakin ya zura ya buɗe. Tana ƙudundune gwanin ban tausayi. Yana shiga ya jawota gaba ɗaya ta faɗa jikinsa. Jikin yayi zafi sosai ta sake fasa kuka cikin rawar baki take cewa,
“Uncle kayi haƙuri kada ka sake dukana, banyi Komai ba ka yi haƙuri Uncle ba zan sake ba.”

Wani abu ya ji a darsu a zuciyarsa, ya jawota sosai ya rungumeta. Yakai hannu bayanta ya ji ta ɗan yi ƙara, hakan ya sake sanya jikinsa mutuwa, ya tabbata akwai ciwo a bayan.

Dole ya miƙe ya kamo hannunta suka fice. Salima ta fito tana duban Bilki.

“Kin ga namiji munafuki? Ina zai je da ita? Hmmmn.”

Bilki Sarkin kishi ta zabura,

“Ni wannan abubuwan da M.Y yake yi ya isheni. Yasan zai lallaɓata ai bai kamata ya daketa ba.”
Ta zauna tana huci, itama Amina anfara wayewa ta haɗa rai tana jin ɓacin rai.

Asibiti ya kaita, aka yi mata allura da magani. Kasancewar bata ci komai ba yasa ya biya restaurant ya siya mata abinci a mota ya matsa mata ta ci kaɗan tasha magani. Kafin su iso gida har zazzaɓin ya sauka, sai gumi da take yi. Yasa hannu zai cire mata Hijabin ta riƙe tana girgiza masa kai. Dole ya ƙyaleta. Bayan sun shigo gida suka sami Bilki ta cika ta yi tam! Saboda Salima ta gama yi masu famfo harda ƙarya ta haɗa masu.

Bai kalle su ba, ya wuce da ita ɗaki ya zaunar da ita. Ya fice ya je ya kwaso su auduga da spirit… Duk suka sake kallon juna suna mamaki. Yana shiga ɗakin ya sa hannu zai cire mata hijabin. Ta yi kamar zata yi kuka ya ɗaure fuska sosai,

“Idan kika sake yi min gardama dukan tsiya zan yi maki.”

Babu shiri ta sakar masa Hijabin ya cire mata. Ya ɗaga rigarta yaga yadda ya ji mata ciwo. Shiru ya yi yana wani nazari, daga bisani ya fara wanke mata. Ƙanƙame shi ta yi tana gumi, dan ta kasa yin kukan saboda gargaɗin da ya yi mata.

Yadda ta ƙanƙame shi ya sanya shi yana jin abubuwa suna sauya wurin zama daga jikinsa. Ada can baya yakan kira kansa da wanda ‘ya mace bata gabansa, sai gashi Husna tana son sauya tunaninsa.

Ji ya yi anbanko ƙofar da ƙarfi, wanda yasa dukkansu suka ɗago suna duban mai wannan aikin.

Muje zuwa dai.

<< Mu’azzam 14 Mu’azzam 16    >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.