Bilki ce ke tsaye tana huci.. Bai ce komai ba ya mayar da kansa bayanta inda ita kuma take ƙoƙarin rufe jikinta a tsorace. Tsawa ya daka mata, da yasa ta nemo natsuwa ta ɗorawa kanta.
A natse ya juyo yana duban Bilki sai kuma ya yi magana cikin ɗaga murya,
“Fice a ɗakin nan, tun kafin ɓacin raina ya ƙare akanki.”
A yadda ta kula babu abin da ba zai iya yi ba, don haka ta juya tana kumfar baki. Bayan ya kammala ne ya kula duk ta sakar masa jikinta, sai dai baya jin zai iya taɓa komai da ke jikinta, duk yadda zuciyarsa ke ingiza shi kuwa. A tunaninsa girmansa ne kawai zai zube a idanunta.
Har ya kai bakin ƙofa ya sake dawowa ya ce,
“Kada ki sake rufe ƙofa, idan kina son mu shirya.”
Ta gyaɗa kanta. Sosai tausayinta ke ratsa shi. Ya ɗan sunkuya ya kamo yatsun hannunta. Anan ma ba ƙaramin dauriya ta yi ba, saboda tsananin tsoro.
“Kin yafe min? Don Allah kada ki gayawa Gwaggo idan kika gaya mata zata iya yin fushi da ni. Kinsan fushinta a gareni baya taɓa barina rufe ido bare inyi barci. Ki ce kin yafe min Husna.”
Yadda ya yi maganar ya bata mamaki, bata taɓa ganinsa yana yi wa wata magana haka ba. Da sauri ta ɗaga kanta bakinta yana rawa,
“Na yafe maka Uncle.. Baka yi min komai ba.”
Ya kula a tsorace take, don haka ya miƙe ya fice yana jin dole ya dira ɗakin Bilki don tana son wuce iyaka.
Hankaɗa ƙofar ya yi, a lokacin ta kasa tsaye ta kasa zaune. Duk bokayen da ta baiwa aiki babu nasara. Tana ganinsa ta zabura ta shige banɗaki ta datse ƙofar.. Duk a tunaninta dukanta zai yi. Saboda tsabar takaici girgiza kansa kawai ya yi, ya ƙara so har bakin ƙofar banɗakin ya ce,
“Kiyi kuka da kanki duk ranar da kika kai ni ƙarshe. Kada ki ce ban ja maki kunne ba.”
Ya juya da sauri ya fice, yana jin zuciyarsa tana sanar da shi ya nemo Jamilu a duk inda yake dan ya bashi ƙwaya.
Kai tsaye gidansu da ke cikin dokan dajin ya wuce, anan ya sami Jamilu yana ta shaye-shayensa da ‘yan mata biyu a gefensa. Dukka ‘yan matan ba baƙi bane a gidan, don haka ya kwanta a bisa gadon yana lumshe idanu.
Akwai wasu kalamai da duk idan ya rufe idanunsa sai sun yi ta masa yawo a tsakiyan kai. Duk yadda yake ƙoƙarin ya goge su hakan ya faskara. Zai watsa ƙwayan a baki kenan wayarsa ta yi ƙara. Babban yaron da ke tafiyar masa da harkokin business ɗinsa ne. Ya ɗauka cike da kasala. Kafin ya yi magana ya ji muryar yaron yana magana cikin ruɗu,
“Oga manyan shagunanka biyu duk sun kama da wuta, babu abin da aka iya cirewa. Tun safe nake cikin tashin hankalin ‘yan damfara sun yi mana gaba da manyan kuɗaɗenka yanzu kuma sai ga wannan masifa.”
A maimakon M.Y ya rikice sosai, sai kawai ya ɗan rintse idanu ya ce,
“Ya Allah…”
Shi kansa yasan indai asarar da Sadiq yake gaya masa da gaske ne, ba ƙaramin taɓa tattalin arziƙinsa hakan zai yi ba. Ya jima anan zaune kafin ya dubi Jamilu ya Gaya masa abubuwan da ke faruwa. Yana gama koro masa bayani ya ɗaga wayar zai sha, cikin sauri Jamilu ya karɓe yana dubansa duba na mamaki.
“Ya za ayi kasha wani abu? Ka tashi don Allah muje ba zama ya kamata mu yi ba.”
Ya yi wani irin murmushi ya ce,
“Idan muka je zamu dawo da kayayyakin ne? Ko zan dawo da dukiyoyina?”
Jamilu ya ce,
“Duk da haka tashi mu je.”
Kai tsaye wurin Ogan su suka nufa. Jamilu ne yake magana cikin damuwa,
“Oga yau ba zamu fita ko ina ba, saboda matsala ta sami M.Y zamu je mu kasheta.”
Ogan ya nemi ƙarin bayani aka gaya masa. Gaba ɗaya gidan sun shiga tashin hankali, don haka suka kama hanya.
M.Y ya yi danasanin zuwa wurin, shiyasa yaso da barcinsa ya yi da ya fi samun natsuwa. Ba ƙaramin asara ya tafka ba, irin asarar da baya jin zai sake dawo da makamancinsa.
A lokacin kiran wayar Gwaggo ya shigo. Ya dubi wayan yana jujjuyata. Indai zai shiga matsala ita ke fara kiransa. Bayan sun gaisa take tambayar ina Husna, anan yake gaya mata abin da ya faru da shi, sai dai ya nuna mata ba wata matsala ba ce mai girma. Duk da haka hankalin Gwaggo ya tashi ta ɗauki buta ta zagaya yafi a ƙirga. Da ƙyar ya iya kwantar mata da hankali ya ajiye wayar.
Ya koma cikin mota ya zauna shiru… Ya zama dole ya gaggauta tuba kafin ranar nadama… Amma kuma ta ina zai fara? Bayan gaba ɗaya lulluɓe yake da masifu. Addu’a kaɗai da iyayen yara suke yi akansu ba zai taɓa barinsa kwanciyar hankali ba.
Lumshe idanunsa ya yi yana fatan Allah yasa iya wahalar kenan.
A wahalce ya koma gida ya sanarwa Salima abinda ya faru, ya kuma ce baya son kowa ya shigo ɓangarensa, ya wuce abinsa. Maganganun da su Salima suke yi a falon shi ya sanar da Husna abubuwan da suke faruwa. Ta shiga tashin hankali. A lokaci guda ta fara tsoro kada ace mata mai farar ƙafa, dan ta taɓa jin wata da irin hakan ya faru da ita akayi ta cewa ya auro mai farar ƙafa.
Kwanaki biyu suka shuɗe kamar ba ayi ba, Oga Saleh ya yi fuska bai nemi da abaiwa M.Y wani abu dan ya rage zafi ba, shima kuma bai nemi hakan ba.
A irin lokacin ne kuma sace ‘ya’yan masu kuɗi ya yi masu wahala, saboda tsaron da ke tare da su. Idan suka kama ‘ya’yan talakawan babu wani kuɗin kirki.
Ko a fuska babu wanda zai ga M.Y ya ce wai yana cikin damuwa ko kuma halin rashi, kasancewar har yanzu bai durƙushe ba.
A karo na farko ya yanke shawarar sanya Husna a Makaranta, ya kuma siya mata waya ya buɗe mata duk chatting ɗin zamani a ganinsa zata rage kewa.
Sai dai abin da bai sani ba, wannan wayar da ya bata ita ce asalin Makarantar da har abada ba zata daina gode masa ba. Da sannu da karanbani ta iya kutsawa cikin groups irin na facebook. Tun bata fahimtar komai har ta gane babu abin da ba zaka koya a ciki ba.
*****
Sannu a hankali ta fara cin karo da mata masu kawo matsalarsu cikin group ana basu mafita. Ita dai ta yi alƙawarin ba zata yi tambaya ko kuma ta gayawa kowa matsalar ta ba, amma tana samun ilimi daga irin amsoshin da ake bayarwa.
Gwaggo kuwa kusan kullum suna waya da juna, tana gaya mata Uncle yana kulawa da ita. Hakan yasa hankalin Gwaggo ya sake kwanciya.
Su kuwa su Bilki basu taɓa yi mata wani abu sai sun tabbatar M.Y ya yi nisa, anan ne take komawa kalar tausayi. Amma ita tunda ta sami Makaranta da waya sai abin ya rage damunta. Har yanzu gidan M.Y babu sauyi daga irin ƙazantarsu, ita kuma Husna abubuwan sun fi ƙarfinta bata ma san ta inda zata fara ba, don haka sai itama ta zama kalarsu gaba ɗaya suka haɗe.
Yau tana kwance daga ita sai vest ta saki jikinta, kasancewar tasan babu wanda zai shigo mata a irin wannan lokacin. Kawai sai gani ta yi mutum ya faɗo ɗakinta yana zare idanu, rigarsa a hannu. Har zata yi ihu sai kuma ta toshe bakinta jikinta babu inda baya kyarma. A lokacin ta ji anhankaɗo ƙofarta ta kafe su da ido tana mamakin me ya kawo mutunin nan ɗakinta? Ga kuma M.Y yana kallonta kallo irin wanda tunda take ba a taɓa yi mata irinsa ba. Sai yanzu ta tuna abin da ke jikinta ta yi saurin jawo hijabi tana kare ƙirjinta.
Abin ƙarin mamaki mutunin ya durƙusa yana roƙon M.Y tare da nuna masa Husna yana cewa,
“Wallahi ita ta kirani, bansan matar aure ba ce.”
Bata dawo daga duniyar mamakin da ta shiga ba, sai ganin su Salima da Bilki da Amina ta yi duk sun shigo suna tafa hannu suna Salati.
A hankali ta mayar da dubanta ga Amina, sai taga tana duƙar da kai. Bata da mafita da ya wuce ta amshi duk wani hukunci da za ayi mata. Ta ji matuƙar ciwon wannan ƙazafi wanda ba zata taɓa yafewa ba.
M.Y ya damƙi wuyan rigar kwarton ya dinga dukansa yana cewa sai ya gaya masa wanda ya buɗe masa ƙofar gidansa ba tare da anganshi ba. Kawai Amina ta bashi hanya a lokacin da ya samu ya kufce daga irin riƙon da M.Y ya yi masa. Aikuwa ya hayayyaƙo mata,
“Dan me zaki bashi hanya ya wuce? Akan me zaki barshi ya tafi ba tare da nasan ta yadda ya shigo gidana ba?”
Amina ta girgiza kai ta ce,
“Haba baka ga yana ƙoƙarin tureni bane? Idan na tsaya ya ji min ciwo fa? Ta yaya ma zan yarda wannan ƙazamin mai ɗauke da dattin zina ya taɓa jikina?”
Bilki ta yi tsalam ta ce,
“Ai ba shi bane abin tuhuma, tunda shi kirawo shi akayi. Husna ce wacce ya kamata kayi mata dukan kawo wuƙa har sai bakinta ya buɗe ta yi bayanin tun yaushe take kawo mana gardi gida? Kai wannan yarinya akwai jarababbiya.”
Wani abu ya soki zuciyar M.Y wanda gaba ɗaya kansa ya kulle. Da ace bai gani da idanunsa ba, baya jin zai iya yarda wai Husna ce take mu’amala da wani. Ko a yanzu ɗin zuciyarsa rawa take yi, amma kuma idan ya tuna a yadda ya gansu ya zama dole ya amince tunda ido biyu ne ba barci take yi ba, bare ace haɗa baki akayi. Shi kuwa me zai zauna ya yi da macen da ta keta masa haddin aure?
‘Gwaggo.’
Zuciyarsa ta ambaci mahaifiyarsa. Da ƙarfi ƙirjinsa ya buga. Ya tabbata ko sama da ƙasa za su haɗe ne Gwaggo ba zata taɓa yarda da abin da zai gaya mata ba. Sai yanzu yake jin kuskuren da ya tafka na sakarwa Husna babban waya, da kuma Makaranta da ya sanyata.
Mu je zuwa ‘yar mutan Borno.
Good