A hankali ya sake kai duba gareta, tana nan zaune babu alamun tsoro a idanunta, hasalima idanun sun ƙafe babu ɗigon hawaye a cikinsu.
Mamaki ya ƙara kama shi, ya nufota ya sake ganin rashin tsoro. Bai ce komai ba ya ɗauki wayarta ya fice da sauri. Ba zai taɓa yarda Husna zata aikata hakan ba, dole ya dawo hayyacinsa dole ya yi dogon tunani kafin ya yanke hukunci cikin fushi. Amma kuma ba zai sake barinta zuwa Makaranta ba, domin samarin wannan zamanin babu abin da ba za su iya ba domin ganin sun rushe duk wata tarbiyya. . .