Mu'azzam ya rage murya kamar mai rarrashi ya ce,
"Gwaggo ita haihuwa ta Allah ce. Idan Allah ya nufa zan haihu sai ki ga a cikinsu wata ta haihu. Bana son kina tayar da hankalinki don Allah."
Ya ƙarashe cikin nuna damuwarsa a fili. Gwaggo dai shiru ta yi bata ce komai ba, har ya gaji da shirun ya miƙe dan ya samu ya sakarwa kansa ruwa.
Husna tana banɗakinsa tana wankewa, bayan ta kammala gyaran ɗakin. Shi kuma bai san tana ciki ba, don haka yana shigowa ya dubi ɗakin cike da annashuwa. Rabon da yaga. . .