Skip to content
Part 23 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Ficewa ya yi ya nausa cikin dajin, hakan yasa ta fito ta nemi wuri ta zauna shiru tana nazarin maganganun da M.Y ya faɗa mata.

Yunusa ya ƙaraso tare da sallama. Dubansa ta yi cikin damuwa suka gaisa.

“Ina yallaɓai?”

Haka kawai ta ji haushin tambayar don haka ta haɗa rai ta ce,

“Ina zan sani.

Bai ƙara ce mata komai ba ya nemi wuri ya zauna.

“Kinyi dacen mijin aure.”

Ya furta mata yana dubanta.

Ko tari bata yi ba, illa ma zuba masa idanu da ta yi tana jin kamar ta shaƙe shi.

“Duk da mijinki auren da ya yi dukka ba ra’ayinsa ya aura ba. Ke kaɗai ce macen da ya aura saboda yana sonta.”

Gyaɗa kanta ta yi,

“To kai ya akayi ka sani?”

Gyara zamansa ya yi yana dubanta cike da tausayawa,

“M.Y ya auri dukka matansa ne a dalilin tursasa shi da akayi. Ya aure su ne abisa wasu sharuɗɗa. Asalin Salima bayerabiya ce. Bilki yarinyar ce ga wani mutum, da ya yi wa M.Y alƙawarin zai tsaya masa wajen cikar burinsa, amma sai ya auri ‘yarsa. Bai wani ja ba, kasancewar yana ganin soyayya ƙarya ce don haka ya amince zai yi aure ko babu soyayya kuma zai zauna lafiya da matar. Ita kuma bayan auren sai take kwasar dukiyarsa tana kaiwa gidansu. Shi kuma saboda yana zaman jiran cikar nasa burin bai taɓa nuna ya sani ba.”

Yunusa ya numfasa, sannan ya ci gaba,

“A gaskiya samun namiji kamar Oga Mu’azzam sai antona. Bai taɓa haɗa dukiyarsa da na haram ba, yana tsananin ƙyamatar haram. Yana kiyaye dokokin Allah. Shiyasa da naji ‘yan sanda suna nemansa na yi dariya kawai. Kada kiyi tunanin mijinki ya gudu ne saboda yana tsoron kamu, ko ɗaya akwai abin da yasa a gabansa ne idan ba ya samu ba ba zai taɓa fitowa ba.”

Baki buɗe Husna take kallonsa. Gaba ɗaya ta kasa fahimtar inda ya dosa. Ta yaya lokaci guda zai zo yana ƙoƙarin wanke M.Y? Ta yaya zata yarda da shi? A lokaci guda tunani ya zo mata cikin ƙwaƙwalwa akan tabbas M.Y ne ya turo shi domin ya zo ya tsarata.

“To ita Amina me ya sa ya aureta?”

Ta tsinci bakinta da tambayarsa ko ba komai tana jin daɗin tatsuniyar da yake mata,

“Uhumm… Ya auri Amina saboda Babanta ya yaudare shi, ya tabbatar masa idan ya auri ‘yarsa ya yi masa alƙawarin zai taimake shi akan wani abu da yasa a gaba. Da farko ya yarda da batun mahaifinta, abin da bai sani ba dukiyarsa ce ta ruɗe su, suke neman hanyar gaje dukiyoyin. Shi kuma M.Y muddin ka furta zaka taimake shi akan abin da yasa a gaba, zai iya yin komai dan yaga ya sami biyan buƙata. Sai dai kuma bayan auren Amina ya yi iya yinsa akan mahaifinta ya taimaka masa ɗin, sai ya nuna abin ya fi ƙarfinsa ya bashi nan da wasu shekaru domin ya samu hanyar da zai nazarci komai. Kamar dai yadda ya faru akan Bilki, To yanzu haka yana zaman jiran mahaifin Amina da mahaifin Bilki waɗanda duk suka yaudare shi.”

Shiru ta yi tana nazari, kafin ta ce

“Menene wannan abun? Ka gaya min ƙila nima in iya samo masa.”

Yunusa ya yi dariya, yana shirin yin magana ya hango M.Y yana ƙarasowa hakan yasa yaja bakinsa ya yi shiru. Husna ta bi inda yake kallo itama sai ta yi saurin dawowa cikin hayyacinta.

Fuskarsa a ɗaure ya ƙaraso yana kallon Yunusa. Bayan sun gaisa ne suka koma bayan wata bishiya suna magana. Husna ta lallaɓa ta je ta laɓe,

“Me kake ce mata?”

Yunusa ya duƙar da kansa ya ce,

“Babu abin da na gaya mata. Hirar dajin nan kawai muke yi.”

Sai yanzu ta gazgata abin da Yunusa yake gaya mata. Ta koma ta yi tagumi. Ya ƙara so har gabanta yasa hannu ya janye mata tagumin yana dubanta,

“Babu kyau tagumi.”

Ta yi masa murmushi a karo na farko. Ta dubi hannunsa ta kai hannu tana shafa wurin harbin ta ce,

“Yanzu ya kusa warkewa ko?”

Ya girgiza kai,

“Har yanzu yana min zafi, dauriya kawai nake yi.”‘

Ta gyaɗa kai cike da tausayawa,

“Sannu.”

Da haka bata sake cewa komai ba, ta kuɗunɗune jikinta alamun tana jin sanyi. Bai ce mata komai ba ya koma ciki ya ɗauko abin rufa ya rufa mata. Ta dube shi sosai, ko alama ba shi da siffar mara imani,

“Na gode.”

Ta furta tana sake sunkuyar da kai, kasancewar idanunsa suna yi mata wani iri da zarar ta kalle su.

“Me zaki ci anjima?”

“Duk abin da zaka ci.”

Ta bashi amsa ba tare da ta dube shi ba.

Shima sai yanzu ya ɗago yana dubanta,

“Tashi muje yawo.”

Kamar ba zata tashi ba sai kuma ta tashi tana binsa a baya. Wajen wani dutse suka nufa suna shirin gangarowa jiri ya ɗebeta ta yi saurin riƙo shi tana ihu. Abin ma dariya yaso ya bashi, don haka ya murmusa ya riƙeta tsam a jikinsa. Wani irin abu yake ji yana yawo a cikin jikinsa, a hankali ya furta mata kalma mai daɗin saurare a kunnenta,

“Ina sonki Husna.”

Firgigit ta yi ta buɗe idanunta tana son ganin ko mafarki take yi. Duk suka zubawa juna idanu, daga bisani ta kauda nata idanun ta maidosu ƙasa.

Hannu yasa ya ɗago haɓarta ya ce,

“Husna buɗe idanunki.”

Ta buɗe su a hankali, a lokacin ta tuna da Gwaggo, a lokacin ta tuna da shi ya yi mata fyaɗe ba tare da ya tuna da dangantakarsu ba. Ta yi saurin rintse idanunta sai hawaye,

“Don Allah ka ƙaryata kanka ka gaya min ba kai ne wanda ya yi min fyaɗe ba, ka ce ƙarya ne.”

Ta bashi tausayi matuƙa ya rasa me zai ce mata sai kawai ya jawota gaba ɗaya ta faɗa ƙirjinsa ta fashe da kuka. Bai iya furta komai ba da ya wuce bubbuga bayanta.

A saninsa bai iya lallashi ba, don haka yake mamakin yadda akayi yake lallashin Husna.

Dole suka nemi inuwa suka zauna shiru. A hankali ya ce,

“Husna ki yafe min.

Bata ce komai ba sai hawaye da ke bin fuskarta,

“Husna ke ce na taɓa cuta a duniyata. Ke ce alhakinki yake ta bibiyana.”

A hankali ta dube shi,

“Sai ka gaya min dalilinka na aikata min haka.”

Hannunsa yasa ya jawota jikinsa ya kwantar da kanta a ƙafafunsa ya kama hannayenta ya kafe su da idanu.

“Idan na gaya maki zaki yafe min?”

Gyaɗa kai kawai ta yi, ba tare da ta sami daman furta komai ba.

“Ranar da kuka fito zuwa Kaduna na damu sosai, musamman da Ogana ya sanar da ni a ranar zamu fita aiki. Cikin hukuncin Allah a cikin motocin da aka tsaida harda motarku. Ina daga gefe hasken wata mota ta hasko min fuskarki. Na shiga ruɗani na shiga tashin hankali. Don haka na biyo su na sami Nasir a gefe na nuna masa ke nace ƙanwata ce su taimakeni su barku ku wuce gidana za su je.

“Nasiru bai yi ƙasa a guiwa ba ya sanar da Oganmu, ya kuma gaya masa yau ya kamata ya ɗauki fansar ɓata masa rai da nake yi. Tunda naga Oganmu ya kirani hankalina ya tashi ya dubeni ya ce a cikin dajin nan yake son inkwanta da ƙanwata ko kuma ya sa Nasir ya kwanta da ke, kuma ya kasheki. Na dube shi cikin tashin hankali nace ba zan aikata ko ɗaya ba, kuma bazan bari wani ya taɓa ki ba.”

M.Y ya yi shiru kamar mai tunanin abinda zai ci gaba da faɗi. Sai kuma ya girgiza kai ya ci gaba da kallon wani gefe yana jin zuciyarsa tana ƙuna,

“Na yi masu dogon gardama, hakan yasa ya bada umarnin a riƙeni ayi maki fyaɗe agaban idanuna. Mutanan da suka riƙeni sun fi ƙarfina. Ina kallo Ogana yana gyara bindiga a cikin dajin nan wurin da muka yi sansani domin aiwatar da kwashe mutane. A gaban idanuna Nasir ya cire wandonsa yana cikin farin ciki.

“Abin da ya zo zuciyata shi ne, bayan Nasir ya gama cimma burinsa, za kuma a kasheki baki ji ba baki gani ba. Ina kallo aka kawo ki wurin aka cire maki hijabi. Ba zaki iya gane su waye ke wurin ba, a lokacin da aka shimfiɗeki sai kika sume a wurin. Babu kunya babu tsoro Nasir ya hau ruwan cikinki.”

Zumbur ta yi ta miƙe tana dubansa,

“Kayi wa Allah ka ƙarasa bani labarin nan kada ka katse.”

Bai dubeta ba, don ba zai iya dubanta ɗin ba ya ci gaba da cewa,

“Wannan rana ita ce rana ta uku da naga tashin hankalin da yafi ƙarfina. Roƙon oganmu na koma yi akan kada ya bari Nasir ya ɓata rayuwar ƙanwata na yarda na amince zan aikata abin da ya ce muddin zai janye maganar kasheki da kuma maganar Nasir ya yi maki fyaɗe. Ogana yana dariyar mugunta ya ce Nasir ya tashi kada ya aikata komai. Anan suka sakeni nayi wurinki da gudu, ina taɓaki na tabbatar da babu abin da suka yi maki. Na roƙe su da su bani wuri suka ce tunda a duhu ne ba za su bani wuri ba. Duk yadda naso inyi masu dabara hakan ya faskara, don haka na amince nayi maki fyaɗe ba tare da na bari kowa a cikinsu ya matso kusa da ke ba, bare yaga jikinki. Naso inyi maki a hankali yadda ba zaki sha wahala ba, sai na sameki a cikin matan da Allah ya yi masu baiwa irin wanda duk namijin da ya ɗanɗanaki ba zai taɓa yarda ki kufce masa ba.”

Wani ɗaci ya kwaranyo masa har cikin maƙoshi, ya rintse idanunsa yana jin kamar yau abin ya faru. Ya ci gaba da cewa,

“Husna wannan ne laifi mafi muni da na taɓa aikatawa ina cikin hankalina. Na tsani kaina. Bayan Oga ya tabbatar da nayi abin da yake so, ya ce a ɗaukeki akai cikin mota. Anan ma na hana faruwar hakan, ni na ɗaukeki na kai mota. Rayuwar ta yi min baƙinƙirin, na kasa barci na kasa cin abinci.

“Gwaggo kawai nake hange, da kuma rayuwarki a hannun Kabiru. A lokacin tausayinki da soyayyarki suka yi min wani irin mamaya. Na shiga ruɗu. Ban sake fita hayyacina ba sai da Gwaggo ta dinga tsinuwa akan wanda ya aikata maki hakan, ta dinga sa malamai suna addu’a. Wallahi Husna tun daga wannan ranar zuwa yanzu ban sake ganin daidai ba. Asarar dukiyoyin da kika ga ina yi, ba komai bane face bakin Gwaggo. Tunda Gwaggo ta aibatani nake ganin manyan asara. Idan baki yafe min ba, bana jin zan sake jin daɗin rayuwar. Idan kika yafe min kamar Gwaggo ce ta yafe min.”

Ya ƙarashe da wata murya mai tsananin sanyi.

Husna ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Kafin ince wani abu ina son Ka gaya min ƙaddarar da ta kaika ga shiga cikin masu garkuwa da mutane? Ka gaya min don Allah. Ina son sanin komai akan rayuwarka kaji Uncle?”

Miƙewa kawai ya yi ya fara tattakawa alamun zai tafi. Da sauri ta biyo bayansa tana jin ta gode Allah da bai bari Nasir ya keta mata mutunci ba, da yau sai ta fi kowa baƙin ciki. Duk da bayan ya gama kasheta za su yi.

Da sauri tasha gabansa, ya dubeta kawai ya aika mata da murmushi ya juya ya ci gaba da tafiya.

“Wash!”

Ta furta tare da zama a ƙasa. Da sauri ya dawo da baya yana duba ƙafafun cikin kiɗimewa. Hakan yasa ta kafe shi da idanunta. Dole ta daina ƙaryata zuciyarta da ke gaya mata da gaske ta kamu da soyayyar Uncle Mu’azzam. Ba zata iya ci gaba da ƙaryata kanta ba. Jin ta yi shiru yasa ya ɗago yana dubanta. Karaf suka haɗa idanu. Da ace zuciyarsa zata natsu, da ta gaya masa gaskiyar abin da ke cikin zuciyar Husna. Sai dai gaba ɗaya gani yake tana yi masa kallon mara adalci, tana yi masa kallon mugu azzalumi.

‘Yar mutan Bornonku ce.

<< Mu’azzam 22Mu’azzam 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×