Bayan sun koma ne, ya sami har Yunusa ya kawo masa abinci, ya karɓi nasa ya wuce wani wuri ya zauna shiru ba tare da ya iya ci ba. Shi kaɗai yasan abin da ke damunsa. Ji ya yi andafa kafaɗarsa ya juyo yana kallonta. Ta fahimci babu abin da Mu'azzam yake buƙata a yanzu da ya wuce kwantar masa da hankali. Da hannunta ta ɗibo abincin ta kai masa baki. Ya jima yana kallon hannun kafin ya buɗe bakin ta zuba masa. Idanunsa suka yi jazir, babu wanda ya faɗo masa a. . .
15