Skip to content
Part 25 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Mu’azzam ya yi murmushi. A ganinsa manyan mata irin su Salima sun kasa bare kuma ita? Ba zai iya barin Husna ta tafi gidan Alhaji Mu’azu ba. Gani yake itama idan ta tafi ba zata dawo ba. A yanzu kuwa bashi da wacce yake gani yake jin daɗi kamarta. Kamo hannunta ya yi yana dubanta,

“Husna ba zan iya yin kasadan rasaki ba. Ke yarinya ce ƙarama ba zan so kema ki zama tarihi ba. Ki duba ki gani, sunan ina raye ne, amma bani da maraba da matacce, tunda har mahaifiyata take kwana da baƙin cikina.”

Husna ta girgiza kai da ƙarfi,

“Ka yarda da ni, zan zama silar farin cikinka, Gwaggo zata yafe maka, Gwaggo zata fahimceka harma ta sa maka albarka. Ni zan ƙwato Abbanmu da ƙarfin ikon Allah.”

Ta ci gaba da shessheƙan kuka. Ya kwantar da kanta a jikinsa, duk suka yi shiru. Ganin dare yana ƙara yi, ya ce su koma ciki. Ta kwanta luf tana dogon tunani. Mu’azzam ya rintse idanunsa ya buɗe su jazir kamar gauta. Ya ciro ƙwaya a cikin aljihun wandonsa wanda ya matsawa Yunusa har sai da ya samo masa.

Kamar ance ta buɗe ido ta buɗe su tar akan fuskarsa, ta dube shi yana ƙoƙarin kaiwa bakinsa ta yi saurin riƙe hannun tana sake kallon ƙwayar cike da mamaki,

“Maganin menene wannan?”

Ta tambaye shi tana sake duban maganin.

“Wannan Jamilu yake bani, maganin yana taimaka min wajen sanyani barci yana hanani dogon tunani. Da ba dan maganin nan ba, ina jin da tuni na fara hauka.”

A hankali ta karɓe maganin tana girgiza kai,

“Uncle abin maye kake nufi? Babu kyau Uncle. Shi kansa Jamilu yana can yana cikin baƙin cikin yadda bai koya maka abin ƙwarai ba. Don Allah Uncle Ka daina sha kaji? Tunda ina tare da kai insha Allahu ba zan barka a cikin ƙunci ba ka yarda da ni.”

Har kullum idan Husna ta yi magana yakan jima yana dubanta, tana bashi mamaki sosai tana ɗaure masa kai. Ya tabbata ba ƙaramin baiwa Allah ya ba yarinyar ba. Komai nata na manyance kamar mai sunan.

“Kayi min alƙawarin ba zaka sake waiwayan wannan abun ba. Idan Gwaggo ta ji kana shan irin wannan abun sai zuciyarta ta kusa bugawa.”

Ta katse masa shirunsa da kalamanta masu tasiri a zuciya.

“Shikenan na yi maki alƙawari.”

Kwashe su ta yi ta ɓoye akan gobe zata zubar. Ta rasa abin da zata yi masa da zai faranta ransa. Gashi babu Qur’ani a kusa da ita. Yana zaune ta yi masa nuni da ya kwanta. Babu musu ya kwanta sai dai kuma ƙafafunta ya jawo ya yi matashin kai da su.

Ta jima tana kallonsa a hankali ta sauke hannunta a bisa kansa. Ya lumshe ido. Tasa hannu ta jawo abin rofa ta rufe masa jikin sannan ta cusa a hannu a cikin gashin kansa da babu wani yawa sai tarin taushi.

A natse take rero karatun Alkur’ani cikin Suratul Maryam. Tana son surar idan tana karantawa ita kanta sai ta ji kamar bata da wata damuwa.

Mu’azzam ya dinga lumshe idanunsa yana buɗe su, yana jin wani irin tarin natsuwa yana shigarsa, wanda zai iya rantsewa bai taɓa jin irin hakan ba, tun bayan da aka raba shi da Abbansa.

A zuciyarsa ya godewa Gwaggo, ya yarda ya amince duk wanda ya yi wa iyayensa biyayya ba zai taɓa taɓewa ba. Ya kuma sake yin imani da Allah. Tabbas musulunci gaskiya ce, duk wanda baya cikin haskensa yana tare da duhu mara yankewa.

A hankali yake jin wani irin ƙaunarta yana sake shiga duk wani sassa na jikinsa. Husna ta haɗa komai da duk wani namiji zai so ya mallaketa a matsayin matar aure kuma uwar ‘ya’yansa.

Sannu a hankali barci ya yi awon gaba da shi, wanda itama ta fara gyangyaɗi hakan yasa ta sauke kansa ta raqube kusa da shi barcin ya kwasheta har ta mirgino ta manne masa ta rungume shi tsam, shima kuma ya mayar da ita ƙirjinsa suka yi wa juna bargo.

Sai da hasken rana ya hudo sannan M.Y ya buɗe idanunsa yana Salati. Ji ya yi yana rungume da wani abu, hakan yasa ya yi saurin duban ko menene. Husna ce take kwance tana barcinta cikin natsuwa. Wayarsa ya janyo ya ga har takwas da rabi na safiya. Yau dai Sallah ta kubce masa. Kwantar da ita yake ƙoƙarin yi, sai dai ta hana faruwar hakan, ta hanyar janyo shi sosai ta nannaɗe masa a jiki. Ya zama dole ya tasheta tunda dukkansu basu yi Sallah ba.

A kunnansa yake kiran sunanta. Cikin barci ta tsinci wani irin yanayi wanda ya sa ta buɗe idanu babu shiri. Ganin yadda ta shige masa yasa kunya ta kama ta, ta yi saurin janye jikinta tare da addu’ar tashi barci. Ware idanu ta yi sosai ta ce,

“Uncle bamu yi Sallah ba.”

Kusan ma ta fi shi ruɗewa yana nan zaune yana kallonta ta fice da sauri ta zuba masa ruwa a buta, ta dawo ta ce,

“Ga ruwan alwalan.”

Bai ce komai ba ya tashi ya fice tare da ɗaukan butar ya zagaya can baya. Ita ma ta ɗauka ta ta sauya hanya ta je ta kama ruwa sannan ta yi alwala.

A tare suka yi Sallah, sannan ta gaida shi. Suna nan zaune shiru, sai ga Yunusa ya zo masu da abinci. Husna ta dubi Yunusa ta ce,

“Yunusa ka nemo min bayanai akan yadda zan shiga gidan Alhaji Mu’azu, ina son a cikin satin nan in isa gidan.”

Yunusa ya ɗan saci kallon Mu’azzam ganin bai ce komai ba yasa ya washe baki ya ce,

“Gaskiya zuwa gidan Alhaji Mu’azu har ki sami daman shiga abu ne mai matuƙar wahala.”

Husna ta jinjina kai,

“Idan naje a matsayin ‘yar aiki fa?”

“Zaki iya zuwa a matsayin ‘yar aiki hakanne kaɗai zai iya sadaki da gidansa. Amma kuma shiga gidanne aiki. Alhaji Mu’azu yana fita duk ranar Asabar da iyalansa, matarsa tana da tausayi haka ma akwai ‘yarsa guda ɗaya da yake so kamar ransa, idan ta furta magana ya zaunu. Sai dai ki je ɗan nesa da Gate ɗin gidan da misalin ƙarfe takwas na safiya, ki yi zaman jiran fitowarsu tara ko goma. Suna fitowa ki yanki jiki ta gabansu ki zube kamar kin suma. Daga nan idan Allah yasa suka ɗaukeki ki ce masu ke dai kin ganki anan garin ne amma baki san me ya kawoki ba, kindai san kina riƙe ne a hannun kishiyar mahaifiyarki. Insha Allah zamu sami nasara.”

Waɗannan bayanan sun fito ne daga bakin M.Y da yake fidda su cikin natsuwa da ƙwarewa.

“To shi Alhaji Mu’azu a wani garin yake? A labarin da ka bani ka gaya min yana Gombe ne baka ce min ya dawo nan Kaduna ba.”

Mu’azzam ya jinjina kai,

“A yanzu haka mahaifina da sauran mutanan da ya kama suna can a Gombe. Amma iyalansa da shi kansa suna nan a garin Kaduna, a cikin unguwar Dosa. Zoben nan yana nan a ɗakinsa anan Kaduna. Duk yadda kike tunanin shahara irin ta Alhaji Mu’azu ya wuce nan. Yana da manyan gidaje a jihohi da dama. Kafin ranar Asabar Yunusa zai je ya tabbatar mana da kasancewarsa a Kaduna ko akasinsa.

Husna ta jinjina kai tana sake jin ƙarfin guiwa a cikin wannan tafiya.

*****

Ranar asabar ta fito cikin atamfarta wacce da ita suka shigo daji kafin Yunusa ya kawo masu kaya. Yunusa yana tsaye yana jiranta dan shi zai kaita har ƙofar gidan.

Suka fito da ita da M.Y yana riƙe da hannunta.

“Yanzu idan zan ganka ya zamu yi?”

Ya girgiza kai,

“Dole sai kin ɗan yi haƙuri da ganina zuwa lokacin da zan san abin yi, domin gidansa cike yake da CCTV. A binciken da na yi na gano har wajen gidansa akwai cctv yana iya ganin abin da ke faruwa tun daga wajen gidansa har zuwa cikin gidan. Don haka Yunusa zai ajiyeki nesa da gidan ki tako kina abubuwa kamar mara hankali, ki nemi wuri ki kwanta kina juye-juye.”

Yana maganar yana zura idanunsa a cikin nata. Ya fahimci kuka take son ta yi, shi kuma kukanta zai iya karyar masa da guiwa. Domin shi kansa ba ƙaramin kokawa ya yi da zuciyarsa ba, da har ta ƙyale shi yake shirin tura Husna gidan Alhaji Mu’azu.

“Ki kwantar da hankalinki, zan dinga kula da duk wani motsinki. Idan kuma kina ganin ba zaki iya ba, don Allah kada kiyi gangancin raba kanki da ni. Kin ga yanzu ni ɗaya zan ci gaba da zama anan, tunda shiga cikin gari a yanzu dai hatsari ne a gare ni.”

Da sauri ta mayar da hawayenta, ta sakar masa murmushi,

“Zan iya insha Allahu. Kawai ka dage da yi min addu’a.”

Har ta juya zata tafi ya ce,

“Husna.”

Ta ja ta tsaya ba tare da ta waigo ba, domin hawayen sun cika mata idanu. Zagayowa ya yi yana dubanta, ya manna mata sumba a goshi ya kama kafaɗunta yana ɗan murmushi,

“Ki kula da igiyoyin auren da ke kanki. Alhaji Mu’azu yana da son mata, idan ya ƙyalla ido akan mace sai ya sameta zai iya samun natsuwa.”

Itama murmushin ta sakar masa,

“Idan zan mance da komai bana jin zan iya mance igiyoyin nan guda uku, domin sun fi komai mahimmanci a cikin rayuwata, tunda da su ne nake neman Aljannahta.”

Ya gyaɗa kai cike da gamsuwa. A wani ɓangare kuma na zuciyarsa yana gargaɗinsa akan wannan ganganci da zai yi. Yana ji a ransa idan wani abu ya sami Husnansa ba zai taɓa yafewa kansa ba. Jawota ya yi sosai jikinsa ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana jin zuciyarsa tana harbawa da sauri da sauri.

Yunusa ya yi gyaran murya, hakan yasa ya saketa yana dubansu. Jikinta babu ƙwari ta wuce ta shiga cikin napep ɗin da Yunusa yake zuwa a cikinta.

Yana nan tsaye har suka ɓace masa da gani. Ya koma ciki ya hau shiri, yana son ko za a kashe shi sai ya kashe Alhaji Saleh. Har ya gama shirinsa tsaf, ya kama wani tunani. Dole ya koma ya zauna shiru yana jin tun yanzu ya fara kaɗaici.

Wayar da Jamilu ya bashi ya ɗauko yana jujjuyata. Wayar ta mutu babu caji. Shima ta hannunsa Yunusa ke karɓa yana kai masa wurin Caji. Yana da buƙatar kiran matansa duk da yaji labarin sun bar gidansa. Ya ɗauki sabon sim ɗinsa yasa a waya ya fito cikin gari wuraren da baya jin za a iya ganinsa, ya kuma rufe fuskarsa sannan ya fara kiran Bilki.

A yadda ya ji muryarta bata tare da wata damuwa, bayan sun gaisa ne ta gane mai magana a zabure ta ce,

“M.Y! Kai ne?”

Sai kuma ta yi shiru. Can zuciyarta ta dinga ingizata har ta soma gaya masa maganganu daga ƙarshe ta ce tabbas kashe shi za ayi Gara ya saketa. Murmushi ya yi mai ciwo sannan ya ce,

“Yanzu Bilki kina ganin zan iya kisan kai?”

Ta ware idanu kamar yana ganinta,

“Ƙwarai kuwa. Ni dai ka bani takardata.”

“Abin da na kira inyi maki kenan. Na sake ki saki ɗaya. Sannan kiyi wa mahaifinki godiya. Ina so kuma inbaki shawara, idan sata ba halinki bane akaina kika koya, don Allah ki daina. Tabon sata bala’i ne musamman a rayuwar ‘ya mace. Ƙila ni ne bana haihuwa zaki iya yin wani auren ki haihu, ki kuma shayar da abin da kika haifa da nononki wanda anan gaba zaki yi danasani. Na barki lafiya Bilki, sai watarana Bilki.”

Kafin ta yi magana ya katse wayar. Jikinta ya yi matuƙar sanyi, tabbas tana son M.Y Soyayya mai zafi, sai dai ba zata iya ɗaukan irin wannan riskin ba. Ga shi kunya ta kamata, bata taɓa sanin M.Y yana sane da irin ɓarnar da take yi masa ba. Ta fashe da kuka mai ciwo tana jin zafin zawarcin da zata yi, tana jin zafin M.Y yasan asalin fuskar da take ɓoye masa..

Yana kashewa ya yi shiru yana jin zuciyarsa tana zafi. Da ƙyar ya daure ya kira Salima. Waya take yi don haka ya yi ta kiranta bata ɗaga ba, har sai da ta kammala wayarta sannan ta ɗauka tana masifa,

“Waye yake ta damuna haka da kira? Ko ana bina bashi ne?”

Ajiyar zuciya ya yi ya ce,

“A’a ko ɗaya. Ya kwana biyu.”

A gigice ta ce,

“M.Y! Yanzu dama kana raye ka ƙyale mu? Kana ina ne?”

Ya yi murmushi ya ce,

“Nima bansan inda nake ba. Kema kina buƙatar takardarki ne?”

Ta ɗan yi shiru, daga bisani ta ce,

“To ko baka bani takardata ba, kasheka za ayi M.Y ka ga babu amfanin riƙe takardar.”

“Kema kin yarda zan iya yin kisa?”

Ya tari numfashinta. Ta yi shiru. Hakan yasa ya jinjina kai,

“Na sakeki saki ɗaya. Don Allah ina son kiyi wa kanki faɗa, ki daina maɗigo saboda illarsa yafi na mazinaci. Kuma ƙila ni ne bana haihuwa, kinga zaki haihu zaki barwa ‘ya’yanki mummunan tabo. Sai watarana Salima.”

Ya sauke wayar ba tare da ya barta ta furta komai ba, duk da daman babu abin da zata iya furtawan. Domin maganar maɗigon nan ya girgizata uwa uba ga saki. Duk da ita ta nema amma bata yi tunanin samun takardarta cikin sauƙi har haka ba.

Amina ita ce ta ƙarshe da ya kira itama ta nuna masa kawai a haƙura ya danƙara mata saki ɗaya ya kuma ja hankalinta akan zina. Sai dai ita ta sami daman furta masa abin da ke ranta,

“M.Y na aikata zina ne saboda baka bani hakkina na aure.”

Ya girgiza kai yana jin ɓacin rai,

“A wurin Allah ba ki isa ki furta hakan a matsayin uzurinki ba. Kuma ko da na aureki ban sameki a budurwa ba, duk me ya jawo hakan? Amina ki ji tsoron Allah. Ki kuma yi wa mahaifinki godiya.”

Ya datse kiran. Yana gamawa ya cire layin ya cillar, sannan ya koma cikin dajin. Su kuwa kai tsaye suka kira ‘yan sandan suka ce ya kira su tare da miƙa masu lambar.

Sai dai ko da akayi tracking aka gano a daidai inda ya tsaya ya yi wayan, anje wurin anyi binciken duniya ba a gano inda yake ba.

Shi kuwa yana dawowa ya kwanta yana kallon saman jinkan, yana jin kamar ya sauke wani kaya ne mai tsananin nauyi, haka zalika yana jin ɓacin rai a Zuciyarsa. Shi yanzu Yunusa yake jira ya ji ko andace.

Daga nesa Yunusa ya ajiyeta ya kuma gaya mata da tasha kwana gidan yana nan mai kalan madara.

Wawakeken Gate ɗin gidan kaɗai abin kallo ne da ban sha’awa. Sai juye-juye take yi tana ƙara kusanta kanta da Gate ɗin. Sai dai zabgegiyar bulalar da ta hango a hannun murtukeken mutumin ya sa taja ta tsaya tana zare idanu. Babu kowa a layin, haka zalika ya mamaye ko ina da girman ginin gidan ta yadda ya zama kamar unguwarsa ce shi ɗaya.

Alhaji Mu’azu yana cikin makeken ɗakinsa yana shiryawa, kasancewar yau ne ranar fita yawon shaƙatawarsa da iyalansa. Wanda hakan yake burge ɗiyarsa Zuhura.

Wani ɗaki ya shiga da nufin ya ɗauki wani takarda, wanda wurin ya zama kamar Office ɗinsa. Har ya ɗauka zai fita idanunsa suka hasko masa ‘yar kyakkyawar yarinya mai cike da talauci, ta cikin kwamfutan da ke zaune a ofishin. Yadda take zazzare idanu yasa ya shagala da kallonta. Duk da hijabi ne a jikinta hakan bai hana shi ƙurawa ƙirjinta idanu ba. Gaba ɗaya ya shagala da kallonta, har zuwa lokacin da ta yi wa kanta makwanci a ƙasan titin da ke shimfiɗe a layin.

Jiki babu ƙwari ya fice ya ƙarasa shiryawa cikin gaggawa gudun kada ta bar wurin.

Zuhura tana hakimce a falon kusa da ita yayarta ce Zakiyya tana latsa waya. Kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci kuɗi ya zauna masu.

“Baby mamanku fa?”

Zuhura da aka kira da baby ta yamutsa fuska ta ce,

“Daddy bata gama shiryawa ba.”

Ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, ya hau masifar ba zai tsaya jiranta ba. Babu shiri Hajiya Mimi ta fito ɗankwali a hannu, ta ce

“Yi haƙuri mu je kawai.”

Har suka fito wajen Gate idanun Alhaji Mu’azu yana kan titin gidansa yana neman Husna. Ganin bai ganta ba, ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba.

Kamar ance ya dubi gaban Driver ya ganta a zube. Cikin rawar murya ya ce,

“Dakata kada kayi kisa.”

Direban shima yaja birki kasancewar ya ankare da ita. Alhajin da kansa ya fito yana faɗin bata cikin hayyacinta akaita asibiti. Hajiya Mimi ta dube shi yadda yake ɓarin jiki ta ce,

“Alhaji kasanta ne?”

Zuhura ta ce,

“Momi ko bai santa ba ya kamata a taimaka mata. Dubi kamar sumewa ta yi.”

Ko dubansu bai yi ba yasa Zuhura da Zakiyya suka ɗauketa akasa a mota. Zakiyya dai takaici ya hanata furta komai, ganin ‘yar ƙauye ce kuma ta jawo masu sunyi asarar fita.

‘Yar mutan Bornonku ce.

<< Mu’azzam 24Mu’azzam 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×