Takun tafiyarsa da ihun kiran maigadi ya jawo hankulan wasu ma'aikatan da ke gidan.
"Ka datse ƙofar gidan nan tun kafin yarinyar nan ta fita."
Abin da kawai yake faɗa kenan. Hakan yasa Maigadi ƙarasowa yana cewa,
"Alhaji ai gidan nan babu ta hanyar da wata halitta zata iya ficewa ba tare da izininka ba. Gida a rufe yake."
Alhajin ya yi shiru yana nazarin wauta irin nasa. Ta yaya yarinya ƙarama zata iya yi masa wayo? Wato dai turota akayi. A can wani ɓangare na zuciyarsa kuwa zallar kwaɗayinta ne ke yawo a zuciyarsa. Har yana. . .