Skip to content
Part 28 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

“Innalillahi Wa Innaa ilaihirraji un…”

Addu’ar da M.Y yake furtawa kenan. Tabbas bai mance kowane tsanani yana tare da sauƙi ba. A hankali ya tashi yana jin jiri na ɗibarsa, sai dai ba zai iya zama a cikin gidan nan ba. Har ya kai farfajiyar gidan ya tsugunna yana jin kansa yana sara masa. A hannu ya ji ansa andafa shi, bai waiwayo ba dan bai da buƙatar yin hakan.

“M.Y mahaifiyarka tana nan a raye. Ina zaka je?”

Wani farin ciki ya lulluɓe shi, ya tashi yana duban Dakta Salim, da kuma su Husna da duk suka rufa masa baya.

“Dakta ina take?”

M.Y ya buƙata cikin farin ciki.

“Gani nan. Lafiya kake nemana?”

Gwaggo ta ƙaraso duk tana dubansu. Mamaki ya kama Dakta Salim da matarsa. Ba za su iya tuna ranar da ta furta komai ba, idan ba sunan M.Y ba. Duk yadda take cikin baƙin cikin abin da ya aikata kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci tana buƙatar ganin ɗanta.

Duk ta lalace ta zama kalan tausayi. Jikinsa na rawa ya fara taku zuwa gareta. Husna tana tsaye bata yi yunƙurin barin inda take tsaye ba.

“Kada ka taɓa ni da hannunka mai datti! Na tsaneka Mu’azzamu, na cireka daga cikin ‘ya’yan da na taɓa haifa a duniya.   Idan ka sake nemana ko ka kusanto inda nake sai na tsine maka ka bi duniya.”

M.Y ya girgiza kai cikin tashin hankali,

“Gwaggo ki yafe min, Gwaggo ki saurareni ki saurari uzurina.”

Gwaggo ta fidda hannu cikin zafin rai ta wanke shi da mari tana jin ɓacin rai yana sake dawo mata cikin tsakiyar kai.

“Insaurari uzurin wanda ya ha’inci jama’a? Wanda ya munafunci iyayensa? Wanda ya ciyar da mahaifiyarsa da haram? Idan baka wuce ka bani wuri ba zan tsine maka. Fita ka bani wuri.”

Yadda duk suka ga idanunta ya rufe sai masifa take yi, hakan yasa suka ƙara tsorata da lamarin Gwaggo. Lallai ranta ya yi mugun ɓaci. Juyawa ya yi yana tafiya a hankali da nufin barin gidan gaba ɗaya. Zai yi haƙuri zai rungumi ƙaddararsa, dan ya tabbata Gwaggo ba zata taɓa yafe masa ba.

Zuciyar Husna ya dinga tafarfasa. Don me ya sa Gwaggo ba za ta tsaya ta fahimci ɗanta ba?

“Uncle Mu’azzam.”

Ta kira sunansa, bai juyo ba amma ya dakata. Ta fara taku tana son isowa gare shi. Gwaggo ta ware murya ta ce,

“Idan kika sake bin bayansa kika zauna da shi ba zan taɓa yafe maki ba Husna.”

Abin mamaki juyowa ta yi ta sakar mata murmushi mai ciwo, sannan ta kama hannun M.Y ta dawo da shi har gaban Gwaggo tana dubanta duba irin wanda ya girgiza zuciyar Gwaggo.

“Duk duniya kowa ya shaida Uncle ɗanki ne na halak! Kin mare shi kin haɗa masa da kalamai masu muni, daga ƙarshe kin ce zaki tsine masa. Gwaggo me ya sa baki tsine masa ba? Kin sha gaya mana tun muna ƙanana Wallahi sai Allah ya jarabce mu. Gwaggo me ya sa da taki jarabawar ta iso gareki kika kasa karɓanta?”

Hawaye suka kubce mata babu ƙaƙƙautawa bakinta yana rawa ta ci gaba da cewa,

“Kinsha gaya mana kullum kina yi wa ɗanki addu’a, shin kina shakka ne akan addu’ar da kike yi masa? ‘Yan fashi sun shigo mana, suka ce ko su kashe shi ko ya aikata mafi munin aiki wato luwaɗi Gwaggo kin mance abin da kika ce masu ne? Bari intuna maki, cewa kika yi kin amince ɗanki ya aikata mummunan aiki wanda ganin masu aikatawa ma idan kayi masifa ce. Duk a lokacin kin mance komai ɗanki kawai kike buƙata.”

Ta sharce hawayen da ke gangaro mata har baki sannan ta ci gaba

“To ina laifin wanda ya yi duk abubuwan da ya yi don ya kuɓutar da mahaifinsa? Ina laifin wanda ya tsaya ya jajirce ya hana kansa cin haram, ya hana kansa cutar da wasu mutane ya kuma dage akan ganin ya amso mahaifinsa? Menene laifinsa a ciki da har ya cancanci irin wannan kalamai daga bakin uwa mahaifiya mai addini kamarki? Sau tari rashin tsayawa mu saurari bayanin ɗayanmu shi ke kawo mana danasani. Duk wanda zai aikata kuskure dole yana da dalilinsa. Yanzu maganganun da kike yi masa baki tunanin idan ya fita ya sake zuwa ya aikata abin da yafi wanda kike zato muni?”

Gwaggo ta dubi Husna kamar ba Husnarta ba, ta dubeta sosai duba na mamaki.

“Husna ban fahimceki ba. Jamilu aka tsinci gawarsa a gidan Mu’azzamu duk hakan ba hujja bane? A gabanki muka ji da kunnuwanmu suna tattauna mugun aikinsu duk ba hujja bane? A yanzu haka ‘yan sanda sun bazu suna neman Mu’azzamu.”

Husna ta girgiza kai,

“Ko a yanzu hukuma suka kama shi burinmu ya cika, kuma zai fito insha Allahu. Daga yanzu ba zai sake guduwa ko ina ba, zai miƙa kansa ga hukuma har su gano gaskiyar komai.”

Sannu a hankali ta warwarewa Gwaggo komai har zuwa karɓo Abba da kuma yadda suka yi zaman jinyarsa.

Husna ta ƙarasa cikin kuka sosai,

“Duk abubuwan nan da Uncle ya tsallake su saboda addu’arki ne Gwaggo, duk yadda ya guji haram saboda ke hakan ya faru. A yau ko Uncle ya aikata abubuwan da ake zarginsa ya yi ne saboda ya taimaki mahaifinsa da kullum yake yi masa magiya akan ya taimake shi.”

Gwaggo ta dinga jin maganar Husna tamkar a mafarki, kafin wani lokaci ta nemi zubewa ƙasa a sume, sai dai Mu’azzam bai bari ta kai ƙasa ba ya tarairayota yana jijjigata.

A lokacin ne kuma suka ji jiniya yana tashi ko ta ina, kafin yasan abin yi ‘yan sanda sun kewaye shi da bindigogi.

Bai dubesu ba hankalinsa yana kan Gwaggo da yake faman jijjigata yana cewa,

“Gwaggo ki tashi ki yafe min, don Allah Gwaggo ki yafe min na tuba.”

Dakta Salim ya yi ƙoƙarin raba shi da Gwaggo amma abin ya faskara, ƙanƙameta ya yi yana jijjigawa. A lokacin ‘yan sanda suka raba shi da ita yana ji yana gani suka sa shi a mota.

Husna kuwa sai ta dube su cikin hawaye ta ce,

“Ku tafi da shi, amma kada ku taɓa shi akan abin da baku da hujja.”

Babu wanda ya tanka mata suka fice da shi yana kallon mahaifiyarsa a kwance a jikin Dakta Salim.

Matarsa ta kawo ruwa suka shafa mata cikin hukuncin Allah ta farfaɗo da sunan Mu’azzam a baki,

“Ina Mu’azzamu yake? Ku kirawo min shi.”

Husna ta kama hannayenta cikin tashin hankali ta ce,

“‘Yan sanda sun tafi da shi.”

Ta samu ta tashi zaune ta rungume Husna ta sa kuka mai taɓa zuciya. Haƙiƙa taso ta yi wa Allah butulci, ta kama bawansa da laifin da bai ji ba bai gani ba. Ga shi Allah ya nuna mata ikonsa tunda har ya bar mata masoyinta a raye.

“Husna ki taimakeni ki sada ni da Malam, ina son ganinsa ki kaini wurinsa mu taru mu yi wa Mu’azzamu addu’ar samu nasara.”

Gabanta ya faɗi da ƙarfi da ta tuna ba zata iya kai kanta gidan ba. Ya zama dole ta bi M.Y har police station indai tana son isowa wurin Abba.

Ta dubi Dakta Salim bakinta yana rawa ta ce,

“Ka gane wani station za su kai shi? Don Allah ka kaini.”

Miƙewa ya yi ya ce su tafi ita kuma matarsa ta zauna da Gwaggo. Har suka bar gidan idanun Gwaggo bai daina zubda hawayen nadama ba.

<< Mu’azzam 27Mu’azzam 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.