Skip to content
Part 3 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Babu natsuwa cikin ransa a lokacin da wata kira ta shigo cikin wayarsa. Ya jima yana duban fuskar wayar yana jujjuyata, daga bisani ya fice tare da amsawa kamar ransa a ɓace.

A lokacin Husna ta miƙe ta nufi tsakar gidan domin ta kwashe kayan shanyar da ta yi. Ta rasa dalilin tsayawarta tana sauraren maganganun da yake yi cikin zafin rai,

“Sau nawa zan gaya maku idan ina tare da Gwaggo ku daina kirana? Me kuke nema? Me zanyi maku don Allah? Wannan ne karo na ƙarshe da zan sake ɗaga kiran da wani daga cikinku ya yi min.”

Har zai kashe ya tsinkayi Muryar wanda ya kirawo yana magana,

“M.Y ka cika zafin rai. Oga ya ce yana nemanka gobe-gobe kuma dole ka zo babu maganar uzuri. Idan ka ƙi zuwa kuma kasan shi.”

Tuni gumi ya shiga tsattsafo masa. Jiki babu ƙwari ya sauke wayar a lokacin da ya fahimci Nasir ya jima da sauke tasa wayar. A fili ya furzar da wani huci ya ce,

“Allah ga bawanka nan ka aiko masa da mafita cikin gaggawa.”

Juyawan da zai yi ya sake haɗa idanu da Husna, da ta kafe shi da fararen idanunta tana dubansa kamar mai son dole sai ta fahimci wani abu.

Sosai ya sha mur, yana ƙoƙarin barin wurin ya tsinkayi siririyar muryarta tana magana,

“Uncle M.Y ana nemanka a wurin aiki ne?”

Har zai hau yi mata masifa, sai kuma ya fahimci ita tsakaninta da Allah take tambayar. Tunda yake da ita bayan gaisuwa babu wata magana da ke haɗa su, domin gani yake ta yi ƙanƙanta ya tsaya yana magana da ita. Shafo sajensa ya yi, tare da sake tamke fuska, yana jin ɓacin rai sosai a zuciyarsa.

Salima ya hango daga ita sai riga da wando na barci tana tunkaro shi. Ya kafeta da idanunsa yana nazarin ada yasan Salima tana da jiki mai kyau, amma tunda ta yi ƙiba komai ya lalace.

Tana isowa ta maƙale shi cikin rawar jiki, kasancewar tasha maganin mata, gaba ɗaya a gigice take.

Shi kuwa a yanayin da yake ciki baya jin zai iya aikata wani abun, don haka ya zame dukkan hannayenta da ke jikinsa yana mata wani duba,

“Ke baki ganin ƙanwata anan wurin ne? Ki natsu don Allah.”

Ya furta mata yana ƙara jin ɓacin rai.

Yadda ta ji muryarsa yasa ta ɗan janye cikin tsoro ta bashi wuri. Ya ɗan juya yana waigen Husna babu ita babu dalilinta, hakan yasa ya sha jinin jikinsa, bai yi tunanin yin wani abu ba, da ya wuce zuwa yiwa Gwaggo sai da safe.

Daga bakin ƙofa kunnuwansa suka zuƙo masa muryar Husna tana cewa,

“Gwaggo aikin me Uncle M.Y yake yi?”

Gwaggo ta ɗan yi shiru kamar mai nazari kafin daga bisani ta bata amsa,

“Ma’aikacin banki ne.”

Husna ta ɗan yi shiru, can kuma ta ce,

“A’a Gwaggo ko dai aikin soja?”

Gwaggo da barci ya fara cika mata idanu, ta yi hamma tana jin ta ƙosa da tambayoyin Husna,

“Ko kuma ɗan sanda ba.”

Ta furta mata tare da ƙarasa lumshe idanun, ta rufe su ruf. Duk da haka Husna bata haƙura ba, ta shiga tashin Gwaggo. Sai dai shigowar M.Y ya taka mata burki daga barin aikin shisshigi da ta tsoma kanta. Da hannu ya yi mata gargaɗi hakan yasa ta haɗiye wani abu mai kama da tsoro. Ita ko alama ba tana tambayar bane da wata manufa, tsakaninta da Allah take tambayar tana so ta san dalilin ɓacin ran M.Y daga kiransa agun aiki.

Gwaggo ta ware idanunta da suka kaɗa suka yi jaaa ta dube shi a lokacin da yake dauke hannunsa. Ko alama bata fahimci komai ba ta ce,

“Zaka je ka kwanta ko?”

Ya gyaɗa kai yana faɗin,

“Zanje inkwanta gobe insha Allahu zan koma Kaduna. Amma bana jin zan yi kwanaki biyu zan dawo insha Allahu.”

Ta ware idanunta tana dubansa. Kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci zancen bai yi mata daɗi ba. Ya girgiza mata kai, ya ƙaraso ya jawo bargo ya rufeta. Addu’a ya yi tare da tofa mata. A hankali ya ce,

“Ki yi barci yanzu gobe zamu yi magana. Sai da safe Gwaggona.”

Kawai ya juya yana sake jin tsanar kallon inda ‘yar ficiciyar yarinyar nan take, mai shegen tambaya.

Yana ficewa kai tsaye ɗakinsa ya wuce. Salima ta yi ɗai-ɗai tana jiran miji, sai dai ko kallonta bai yi ba, baya jin zai iya sake yin wankan saboda irin sanyin da ake dokawa. Brush kawai ya yi, ya koma kan gadonsa yana juye-juye. Salima ta sake maƙale shi tana yi masa wasu abubuwa, amma ko a jikinsa. Da ya ga za ta dame shi, sai ya miƙe ya wuce ɗakin Bilki yasan ita ce zata iya haƙuri ba tare da ta matsa masa ba.

Sai dai kuma me? Har ya fara rufe idanu Salima ta faɗo ɗakin, suka yi ta tashin hankali. Yana kwance yana jinsu bai iya ce masu komai ba, shi kaɗai yasan abinda ke damunsa. Da yaga suna sake ɗaga murya ya miƙe cikin zafin rai ya ce,

“Wallahi duk wanda yasa mahaifiyata ta ji irin wannan haukan da kuke yi, Wallahi sai na baku mamaki. Wani irin sakarci ne wannan?”

Salima da bakinta baya shiru ta ci gaba da maganganu. Cikin takaici ya bar masu ɗakin kawai ya fice wajen motarsa ya buɗe ya shiga ya kwantar da kujera, ya yi kwanciyarsa. Da yaga hakan ba zai yi masa ba, ya lallaɓa ya koma ya ɗauki abubuwa masu mahimmanci kawai ya tashi motarsa ya yi gaba, ba tare da tsoron komai ba.

*****

Yana tsaye a gaban ogansa cikin ɓacin rai, hakan yasa sauran yaran suka zuba masu idanu, domin idan da sabo sun saba ganin fushin M.Y… Haka zalika shi kaɗai yake taka ogansu ya taku.

“Me ya sa zaka sa a kirani ina tare da mahaifiyata da na jima ban ganta ba? Zan sami matsala da duk wanda ya sake kirana a waya. Akan me? Wai dole sai na aikata zunubi?”

Ogan ya shafi kansa ya ce,

“Sai kuma kayi… Ka buɗe Laptop ɗinnan kayi min bincike akan gidan Alhaji Sani..”

M.Y ya ja tsaki ya juya da nufin barin ɗakin. Wasu majiya ƙarfi suka tokare hanya. A fusace ya zari bindiga daga ƙugun ɗaya ya saita akansa.

“Idan ka sake tare min hanya zan kasheka inkashe banza! Kada ka sake yi min irin wannan gangancin.”

Ya jefar da bindigar Yana huci. Sai yanzu yake jin me ya sa ma ya amsa kiransu?

A natse ya dawo ya zauna ya amshi Laptop ɗin ya gama bincikensa ya gaya masu komai. Ogan ya sake murmushi ya ce,

“Ka shirya da kai zamu je Makarantar da babban ɗansa yake zamu ɗauke shi. Kai nake son ka jagoranci tafiyar.”

Ji ya yi kamar ya caka masa wuƙa a ƙirji. Sai dai ko alama bai nuna wani abu ba, kawai ya gyaɗa kai,

“Shikenan?”

Shima ya karkaɗa kansa alamun haka yake nufi. Ɗakinsa ya wuce ya kwanta kan gado, yana tunanin irin ƙaryar da zai yi wa Gwaggo. Tun ɗazu take kiransa tana faɗa, amma ya kasa yin komai da ya wuce bata haƙuri. Ya yi alƙawarin gobe zai koma gareta. A lokacin ne kuma tunanin siyan sabon layi ya zo masa, yadda idan ya koma babu wanda ya isa ya same shi a waya har ya gama ganin gida.

A lokaci ɗaya kuma tsoro da firgici suka shige shi, haka kawai yake jin baya son zuwa inda Ogan ya tura shi…

Mu je zuwa

‘Yar Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 14

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 2Mu’azzam 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×