Haka ya kwana cikin rashin sukunin zuciya. Ya rasa me ke damunsa, ga wani irin zazzaɓin dare da kusan kullum yake damunsa.
Ya sani indai da Husnarsa zai yi rayuwa babu shi babu wata damuwa bare tashin hankali.
Kwance yake a gadonsa ya yi shiru kalaman Salima ke sake dawo masa ƙwaƙwalwa,
‘Ina son ka dawo dani ɗakina. Ba zan iya zuba idanu kana rayuwa da wata ba ni ba.’
M.Y ya sake yin juyi ya rungumo filonsa Yana jin ƙarin damuwa musamman da ya baiwa Salima kwanaki uku jal da zai dawo mata da amsar maganarta. Ta yaya zai iya tunkarar Gwaggo da Abba da maganar nan? Uwa uba Husna baiwar Allah.
Ji ya yi anɗora hannu mai taushi a bisa kansa hakan yasa ya lumshe idanu,
“Duk da bansan wacece ba zuciyata ta sanar da ni, wacce ta fi kowa mahimmanci ne a zuciyata a cikin mata.”
Murmushi ta sakar masa wanda iyakarsa fuska. Duk abubuwan da yake ciki kwana biyu tana kula da shi, sai dai ta yi alƙawarin ba zata taɓa tambayarsa dalili ba, har sai idan shi ne da kansa ya so ta ji.
Wayarsa takai hannu zata ɗauka kasancewar kullum a wayarsa take buga game, ko kuma ta hau twitter kamar yadda ya sabar mata. Sai dai abin mamaki da sauri ya janye wayar yana sake yi mata murmushi.
Bata damu ba ta haɗe fuskarsu wuri guda ta yadda yake iya jin saukar numfashinta a bisa fuskarsa. Ya fahimci Husna tana dagewa ne tana yi masa wasu abubuwan don saboda ta cire shi daga cikin tunani.
“Ka kwanta a ɗaki kai kaɗai ka bar babynka ita ɗaya a kitchen babu abokin hira.”
Bakinsa ya kai bisa nata ya sumbata sannan ya ce,
“Sorry na yi laifi. Yanzu me kike son intayaki?”
Girgiza kai ta yi kafin tasa hannu cikin ƙirjinsa tana yi masa kamar susa ta ce,
“Bana buƙatar komai da ya wuce wannan murmushin naka.”
Ƙara faɗaɗa murmushin ya yi sannan ya mirginota gaba ɗaya ya koma shike sama ita ke ƙasa. Hakan yasa ta kama ture shi tana faɗin,
“A’a Uncle bana so, bana so..”
Ya kafeta da ido kafin ya ɗan kwaikwayi muryarta,
“A’a baby ina so ina so.”
Ƙyalƙyacewa ta yi da dariya hakan yasa ya saki ajiyar zuciya. Yana son ganin farin cikin Husna baya son ganinta a cikin damuwa ko ƙanƙani.
***
“Haba Salima! Wai me ya ke damunki ne? Na gaya maki ki kwantar da hankalinki indai gidan M.Y ne kamar kin shiga kin gama.”
Salima ta dubeta cikin cizon yatsa,
“Yaushe zan kwantar da hankalina bayan da idanuna na ga tsinanniyar yarinyar nan a kwance a ƙafafunsa? Ke wai baki kula da yadda M.Y ya canza bane? Ya yi kyau ya ƙara haske alamun hutu da kwanciyar hankali sun bayyana a jikinsa. Yau wai nice naga M.Y da wata a cikin wani yanayi kuma ban ɗauki mataki ba. Wallahi kada yarinyar nan ta yarda inshigo, domin sai na mayar da dariyarta kuka. Sai ta zama abar ƙyamata a idanun M.Y. Hatta iyayensa ɗin sai nasa sun ƙyamaceta sun gujeta.”
Shukra ta jinjina kai ta san ƙaramin aikin Salima ne ta yi duk abubuwan da ta lissafa.
“Ki dai bi a hankali, ina nufin idan zaki haƙa ramin mugunta ki haƙa shi ƙarami. Shi sharri ɗan aike ne.”
Salima ta zabura,
“Sai dai ya dawo maki,ba dai ni Salima ba.”
*****
Garin Abuja suka dira a wani hotel domin gudanar da wani kasuwancinsa. Ba zai iya barinta a gida ba shiyasa ya taho da ita. Ruwa ake tsugawa kamar da bakin ƙwarya, hakan yasa ya yi mata rumfa da jikinsa har sun fara tahowa ma’aikatan suka yi saurin tarbansu da lema. Gaba ɗaya suka kalli juna a cikin leman sai duk suka yi murmushi.
Kallo ɗaya idan kayi masu baka buƙatan na biyu zaka tabbatar cikakkun masoyane masu ji da kansu. Yana rungume da ita a gefen damansa har zuwa inda ɗakinsu yake. Suna tsaye ma’aikacin da aka kira tun isowarsu domin ya jira zuwansu ya buɗe masu ƙofa, tare da basu izinin shiga.
Suna shiga suka datse ƙofar, anan jikin ƙofar ya matseta har sai da ta ɗan yi ƙara.
“Baby.”
Ya kirata. Idanunta a lumshe ta amsa. Ya girgiza kai kamar tana ganinsa,
“Buɗe idanunki ingaya maki wata magana.”
A hankali ta buɗe tare da hawaye sharr!! Domin kuwa tun bayan da suke shirin tahowa Kaduna ta ji shi yana waya ƙasa-ƙasa hakan yasa bayan ya gama ya ajiye wayar ta ɗauka, abin mamaki da Salima yake waya. Sannan ta duba cikin saƙonni anan ta fahimci soyayya a tsakanin mijinta da Salima ya yi nisa. Ta fahimci yana son mayar da matarsa yana tsoro, hakan yasa har suka yi wa kansu wurin haɗuwa a cikin wannan hotel ɗin. Zuciyarta tana yi mata ɗaci. Ita kuwa da zai nuna mata abin da yake buƙata na maido Salima zata amince fiye da ace mijinta ya koma aikata zina.
Yadda yaga ta buɗe idanun da hawaye kamar ruwan famfo ya tashi hankalinsa. Da sauri ya kama kafaɗunta sai kuma ya cire hannunsa ɗaya a kafaɗarta ya ɗago haɓarta,
“Menene? Wani abu ya faru ne?”
Gaba ɗaya ya gigice. Girgiza kai ta yi ta ce,
“Babu komai. Rayuwarmu ce abin burgewa da ban sha’awa, bana son watarana ta zo da zamu rasa farin cikin nan.”
Nan da nan ya sake shan jinin jikinsa, ya yamutsa fuska ya ce,
“Kina tunanin akwai ranar da dukkanmu muna raye farin cikin nan zai gagaremu? Ina laifin ki hango mana mutuwa a matsayin dalili mai ƙarfi da za ta iya raba mu?”
Ta gaji da maganar zuciyarta ta fara jin haushin kalamansa, don haka ta taƙaita da cewa,
“Abin da nake nufi kenan.”
Ajiyar zuciya ya ƙwace masa, yasa baki yana lasar hawayen, ta yi saurin duƙar da kai ta ɗan ture shi tana cewa,
“Na gaji da yawa barin inwatsa ruwa.”
Yana tsaye kaman gunki ta shige banɗakin ta sa key. Yana tabbatar da ba zata fito da wuri ba, sai ya ɗauki wayarsa ɗaya ya mance ɗayan ya fice.
Har ta yi wanka ta kimtsa bai dawo ba. A lokacin ta ɗaga kai tana duban agogo, har ƙarfe taran dare ya gota. Da ƙyar ta iya shan shayi a cikin uban kayan abincin da aka zube masu.
Rigar sanyi ne a jikinta mai hula, ta ɗauki key ɗin har zata fice ta ga wayarsa don haka ta ɗauka tare da buɗeta. Lambar ɗakin Salima ne da ta turo masa. Ajiye wayar ta yi, tare da buɗe ƙofar ta fice. Can wani wuri ta samu daga saman benen yana hasko mata ɗakin Salima, ta zauna shiru cikin tunani kala-kala.
Ta ƙi yarda ta baiwa zuciyarta daman zarginsa domin tasan hukuncin hakan.
Tana nan zaune ta ƙurawa ƙofar idanu ba tare da ta iya kawar da kai ko da na sakwan ɗaya ba.
A lokacin taga ya fito daga ɗakin, ba zata iya tantance a yanayin da fuskarsa take ciki ba, kasancewar ta fi kallon Salimar ita da take ɗaure da tawul. Sun jima anan tsaye suna magana daga bisani Salimar ta nemi da ta rungume shi, ya ƙi amincewa hakan wanda ke nuni da yana nuna mata mutane suna kallonsu.
Takaici da baƙin ciki suka taru suka sake lulluɓe Husna. Ganin ya tunkaro saman bai sa ta bar wurin da take a zaune ba.
Kafin ya ƙaraso wani kakkauran mutum ya ƙaraso kusa da ita yana yi mata wani mugun kallo na ‘yan duniya
“‘Yan mata kina neman abokin taya hira? Yaya sunanki ne?”
Takaici ya ƙara kama Husna, tana shirin yarfa masa baƙar magana ta hango M.Y yana huci yana isowa ya shaƙe wuyan rigarsa,
“Uban wa ya baka izinin kula matata? Iyye! Na ce uban wa ya baka izinin kulata?”
Mutunin ya samu ya cire hannun M.Y da ƙyar yana taɓa wuyar rigarsa ya ce,
“Allah ya baka haƙuri, bansan matar aure ba ce. Da ka damu da ita ai ba zaka barta anan tun ɗazu ita kaɗai ba, kuma da baka tafi wurin wata ka ƙyaleta ba.”
Yana maganar yana tafiya, hakan yasa daga Husna har M.Y suka bi shi da kallo. Idan bata yi ƙarya ba wato shima ya ganshi kenan da Salima.
M.Y ya dubeta cikin borin kunya da kuma tsananin kishi, ya ce
“Uban wa ya ce ki fito nan? Ke baki san irin hatsarin wurin nan ba?”
A hankali ta ɗago cikin jin zafin furucinsa ta ce,
“Ubana ya taso daga ƙabari ya bani izinin fitowa.”
Kawai ta juya tana tafiya a hankali har ta isa ƙofar ɗakinsu ta buɗe ta shiga. Ko da ya shigo bai sameta a ɗakin ba, ya murɗa ƙofan banɗakin anan ya ji a rufe.
Komawa ya yi ya zauna yana sake dawo da kalaman mutumin can. Can ta fito idanun nan sun kumbura saboda kuka. Bai ce mata komai ba ya shiga banɗakin ya yi wanka sannan ya fito ya tayar da Sallah. Mamaki da tashin hankali suka bayyana a fuskarta. Yau M.Y ne ke haɗa Sallar Magrib da kuma Isha’i? Anya lafiyarsa ƙalau kuwa? Duk yadda take kokawa da zuciyarta akan kada ta zarge shi da aikata wani mugun abu, sai da zuciyarta ta girgiza.
Ƙirjinta ta dafe tana karanto Innalillahi Wa Innaa ilaihirraji un…
Wasu ruwan hawayen suka sake tsinke mata babu ƙaƙƙautawa. Ta sa bayan hannu ta goge. Bayan ya idar ya zuba abinci ya ci kaɗan ya ture. Ya kira kitchen ya ce su zo su kwashe kayayyakin. Shi da kansa ya miƙawa ma’aikatan komai suka fita da su. Ya je ya yi brush ya dawo ya kwanta ba tare da ya dubeta ba. Itama ta kwanta ta juya masa baya.
Duk yadda yake tunanin zai iya fushi ya ƙyaleta abin ya faskara. Ita kanta wannan shi ne karo na farko da ta taɓa kwanciya ta juya masa baya. Dukkansu suna ta juye-juye. Ita baƙin ciki yafi komai yawa a zuciyarta. Kishin Salima ya yi mata yawa. Addu’a kaɗai ke sanyaya mata rai.
Ji ta yi ya juyo da ita suna fuskantar juna,
“Baby fushi kike dan na yi maki faɗa? Ba nufina inzageki ba bansan yadda akayi furucin nan ya fito daga bakina ba. Nasan laifina ne da na tafi na barki ke ɗaya kiyi haƙuri ki yafewa Uncle kin ji? Na ɗan fita ne muna tattaunawa akan zaman meeting ɗinmu na gobe. Kada ki sake kwanciya ki juyawa mijinki baya dan banason tsinuwar mala’iku su tabbata akanki.”
Wani baƙin ciki ya sake kamata, kawai ta fashe da kuka mai ƙarfi. Shikenan daga yanzu ba zata sake yarda da shi ba, tunda har ya zama maƙaryaci. Ta kasa magana sai kuka, ya yi ta lallashinta har ta yi shiru. Babu kunya ya fara lalubanta bata iya hana shi ba, haka bata mayar masa da martani ba. Shi kaɗai ya yi rawarsa ya kuma yi kiɗansa.
Sai ya gwammace ma da bai nemeta ba, don har gwara ta ce masa ba zata amince ba, da ta yi masa hakan. Bai ce komai ba domin yasan laifinsa ne dole ya yi lallashi.
A ƙirjinsa ya kwantar da ita yana shafar gadon bayanta,
“Baby yanzu akwai laifin da zan yi maki ki kasa yafe min?”
Jikinta ya ɗan yi sanyi, mata iyayen rauni nan da nan ta ji bata kyauta masa ba, a hankali ta ce,
“Ai na yafe maka.”
Ya girgiza kai,
“A’a baki yafe min ba. Baki taɓa yi min irin hakan ba, ko laifina ya yi girman da zaki kasa yafe min a irin wannan lokacin ne?”
Ta haɗiye wani abu mai nauyi a zuciyarta ta yi dabarar goge ƙwallan da ya sakko ta ce,
“Kayi haƙuri na yafe.”
Ya rungumeta a ƙirjinsa yana jin wani abu yana ƙoƙari da ƙarfi da ya ji sai ya tunkuɗe soyayyarta ya maye da na Salima, amma hakan ya gagara.
****
Washegari yana shiryawa da Safe ita kuma tana haɗa masa Break ɗin da aka kawo masu ya dubeta babu walwala a tare da ita ya ce,
“Ki shirya mu je wajen meeting ɗin tare.”
Kanta kawai ta girgiza masa. Ya fahimci dole akwai wani abu da yake damunta, amma kuma baya son matsa mata da yawan tambaya. Sai da ya kai gasasshen bread ɗin baki ya gutsura sannan ya miƙa mata. Ta ɗan kauda kai, ya haɗa rai. A hankali ta buɗe bakin ya saka mata. Kasancewar yana sauri yasa ya yi mata sallama sai ya dawo.
Yana ficewa itama ta fito ta nufi wurin da ta tsaya jiya. Kai tsaye ɗakin Salima ya shiga bai jima a ciki ba, suka fito tare ta rako shi, suka ɗan yi magana tana kallon yadda Salimar take kwasar dariya har ya bar wurin bata daina ɗaga masa hannu ba.
Husna ta yi ajiyar zuciya ta koma ciki ta rufe ƙofa ta ciro ƙaramin Alqur’aninta tana karantawa tana kuka. A tsakanin jiya da yau duk ta soma fita hayyacinta.
Ji ta yi ana ƙwanƙwasa ƙofa. Kamar ba zata buɗe ba, sai kuma ta ɗauki Hijabinta bayan ta goge fuskarta ta buɗe.
Kallon kallo suke yi wa juna tsakanin Husna da Salima. Kallo ne mai cike da saƙwanni. Idan banda neman rigima irin na Salima me ya kawota nan?
Ta tambayi zuciyarta a lokacin da ɗayan ɓangaren na zuciyarta take gaya mata kawai ta rufe ƙofar. Hakan ta yi yunƙurin yi sai dai tuni Salima ta fahimci abinda take shirin aikatawa don haka ta tureta ta shigo ɗakin tana murmushi.
Muje zuwa dai.