Gaba ɗaya M.Y ya zube bisa guiwowinsa, a gaban Gwaggo ba tare da yasan abin da zai iya cewa ba. Abba ya dube shi sosai, ya fahimci ɗansa baya cikin hayyacinsa.
"Mu'azzam kana addu'a kuwa?"
Abba ya tambaye shi yana ƙara nazarinsa. Gyaɗa kansa ya yi,
"Abba ina addu'a, amma bansan me ke faruwa da ni ba. Don Allah kada ku hukuntani akan abin da bani da laifi akai. Gwaggo kada ki juya min baya. Abba ku yafe min don Allah."
Duk yadda Gwaggo take jin haushinsa sai da ta ji zuciyarta ta girgiza. Ita. . .