Skip to content
Part 34 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Gaba ɗaya M.Y ya zube bisa guiwowinsa, a gaban Gwaggo ba tare da yasan abin da zai iya cewa ba. Abba ya dube shi sosai, ya fahimci ɗansa baya cikin hayyacinsa.

“Mu’azzam kana addu’a kuwa?”

Abba ya tambaye shi yana ƙara nazarinsa. Gyaɗa kansa ya yi,

“Abba ina addu’a, amma bansan me ke faruwa da ni ba. Don Allah kada ku hukuntani akan abin da bani da laifi akai. Gwaggo kada ki juya min baya. Abba ku yafe min don Allah.”

Duk yadda Gwaggo take jin haushinsa sai da ta ji zuciyarta ta girgiza. Ita kanta Husna ɗagowa ta yi ta kalle shi, cike da tausayin kalamansa.

Abba ya miƙe ya ce,

“Zo mu je Mu’azzam. Mahaifiyarka tana da buƙatan hucewa tukun.”

Jiki babu ƙwari ya biyo bayan mahaifinsa. A can kusa da wani dutse suka zauna. Abba ya ɗan yi murmushi ya ce,

“Kowane ɗan adam sai anjarabce shi, sai dai jarabawar Allah bata da wuya, musamman idan ka kasance mai imani. Kai Jarumi ne Mu’azzamu, wanda bana kokwanto akanka zaka iya. Matarka marainiya ce, ko yaya ka cutar da maraya sai Allah ya kama ka. Dole mahaifiyarka zata ji zafi akan yadda taga Husna ta koma, domin kuwa amana ce a hannunta, ita kuma ta damƙawa ɗan da ta yarda da shi.”

Abba ya sauke kalamansa a hankali yana sake duban ɗansa, yadda ya natsu yake saurarensa.

“To Abba me ya ke damuna? Husna bata taɓa yi min laifin komai ba, ban taɓa jin tsanarta ba, amma nakan manceta a cikin rayuwata.”

Abba ya gama fahimtar asiri ne a jikin ɗansa, ya zama dole su kansu su tashi tsaye da addu’a tun kafin Salima ta haukata masu ɗa.

“Ka ci gaba da addu’a. Mu da kanmu zamu dage da yi maka zamu sa ayi kuma insha Allahu.”

Ajiyar zuciya ya ƙwace masa,

“Abba ka ba Gwaggo haƙuri kada ta ce zata rabani da Husna.”

Murmushi ya sakar masa irin nasu na manya,

“Ba zan iya ba Hafsa haƙuri ba, ba zan shiga tsakanin ‘ya da uwa ba. Ni kaina kunyarta nake ji, ta ba ɗana amana ya kasa riƙewa. Ka kwatanta yadda uwa take ji a lokacin da ta kai ‘yarta gidan miji aka wulaƙanta mata.”

M.Y ya yi shiru yana nazarin kalaman Abba.

Har dare Gwaggo taƙi kula M.Y haka zalika bai sake sa Husna a idanunsa ba. Ita kanta Salima tunda ya kawo mata abinci bata sake sa shi a cikin idanunta ba. Don haka dabara ta faɗo mata, ta kira shi a waya ta ce zata mutu cikinta na ciwo. Kamar ba zai je ba, ya daure ya shigo. Suna haɗa idanu shikenan ya nemi duk wata damuwa akan Husna ya rasa.

Shiru-shiru Gwaggo tana jiran fitowarsa babu shi babu dalilinsa. Ita kanta Husna sai zaro idanu take yi, tana fatan ya zauna zaman hira da Gwaggo kamar yadda yakan yi, idan tana jin muryarsa tana samun natsuwa. Har sha ɗayan dare babu M.Y. Abba yana kula da yanayin Gwaggo sai dai ya yi alƙawarin ba zai taɓa sa masu baki ba.

Washegari da safe Gwaggo ta bar gidan zuwa nemawa M.Y taimako. Shi kuma Abba ya nufi gidan gonarsa. Don haka M.Y ya shigo yana neman Gwaggo bai ganta ba, hakan ya bashi daman shigewa ciki.

A kwance ya ganta gashin kanta a baje tana sanye da ɗan ƙaramin rigar barci. Ba barci take yi ba sai dai ta faɗa duniyar tunani.

Duk abubuwan karyawan da aka ajiye mata bata ci abin kirki ba. Surar jikinta kullum ƙara fizgarsa yake yi  bare kuma yadda ya kwana biyu bai ji ɗumin jikinta ba. Sai duk ya rikice.

Jin hannu ta yi a tsakiyar kanta hakan yasa ta waiwayo a tsorace. Tana ganin shi ne ta kauda kanta tana jin ɓacin rai. Ganin yana son rikitata yasa ta tashi zaune ta turo baki kawai ta miƙe ta kama hanyar barin ɗakin. Babu abinda ba a gani a cikin ‘yar rigar barcin. Tun kafin ta kai ga fita ya kamo hannunta, ta fara ƙoƙarin ƙwacewa. A jikin bango ya manneta kafin ya sami sa’a ya lalubo bakinta. Ya riga yasan abinda ke karyar da taurin kanta, don haka ta yi tsit idanunta a lumshe sai numfarfashi da suke saukewa.

A lokaci guda duk suka fita hayyacinsu, babu tunanin komai ya jawota har zuwa ƙofa ya rufe sannan ya ɗauketa ya maidata gado.

Hankalinsa ya kai ƙololuwan tashi ta yi magana cikin wani irin sanyi,

“Uncle gadon Gwaggo ne fa.”

Kamar anzare masa lakka haka ya ji. Ba abin da ta furta ya sa ya dawo hayyacinsa ba, a’a tunawa da ya yi bai ga Gwaggo ba, kuma tana iya dawowa a ko wane irin lokaci yasa shi ya mirgina gefe yana sauke numfashi. Husna tana buƙatar mijinta, don haka ta rintse idanu duk suka yi shiru.

“Baby zaki biyo ni ɗakina?”

Bata iya cewa komai ba har ya tashi yana haɗa hanya.

“Ki zo yanzu kin ji?”

Bayan ficewarsa ne, ta kwashe duk abubuwan da ya rabata da su, ta ɗaura zane tasa hijabinta. Cikin ikon Allah Salima tana ɗakinta tana barcin asara. Tana shigowa ya rufe ƙofar. Anan suka nunawa junansu irin kewar da suka yi.

Ji ta yi yana cewa,

“Innalillahi Wa Innaa ilaihirraji un..”

Cak! Ta ji numfashinta yana shirin tsayawa, a lokacin da ta laluba ta fahimci abin da ya sanya shi gigicewa. Ita kanta jikinta ya yi mugun sanyi ta yadda ta ji wani tashin hankali ya bayyana ƙarara. Yanzu yanzu lafiyarsa ƙalau, ya kasa yin kwanciyar aure da matarsa. Wata zuciyar ta ce da shi,

‘Ko dai gabanka mutuwa ta yi?’

Da sauri ya girgiza kai saboda yanzu-yanzu lafiyarsa lau, sai da ya zo saduwa da matarsa ne abu ya gagara. Ga ciwon ciki mai tsanani da ya rufe shi. Ita kanta ta ruɗe ta rasa yadda zata yi sai kawai ta fice da sauri ta barshi anan.

A farfajiyar gidan ta zauna ta yi tagumi. Gaba ɗaya idanunta sun kaɗa sun yi jazir. Har Gwaggo ta shigo bata sani ba, ta jawo kujera ta zauna kusa da ita tare da cire mata tagumin.

Tana ganin Gwaggo idanunta suka kawo ruwa. Cikin dabara ta shanye su.

Gwaggo ta shiga fiddo magungunan tana yi wa Husna bayanin inda ta samowa M.Y. Ita dai Husna sai kallonta take yi, ta yaya zata iya sanar da lalurar da ta sami M.Y yanzun nan, a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ɗanta ya juya ya zama ba namiji ba. Tana son sanin a halin da yake sai dai babu dama.

“Lafiyrki lau nake magana kina banza da ni? Sai yaushe zaki daina irin wannan zazzafan tunanin?”

Da ƙyar ta kalato yamu ta samu ta haɗiye ta jiƙa maƙoshinta.

“Gwaggo ba tunani nake yi ba. Kaina ne yake min ciwo.”

Gwaggo dai bata ce komai ba, har fitowan M.Y yana riƙe da cikinsa. Har zata tashi ta ƙarasa gare shi, Gwaggo ta harareta dole ta koma ta zauna.

“Gwaggo taimaka min da magani ciwon ciki nake yi.”

Kamar Gwaggo ba zata yi magana ba, sai kuma ta ce,

“Allah ya ƙara afuwa. Bani da maganin ciwon ciki.”

Jiki babu ƙwari ya wuce cikin falonta ya buɗe frij ya ɗauko lemon tsami. A cikin ruwan ɗumi ya matse ya samu ya sha. Zufa kawai yake keto masa don haka ya kwanta a tsakiyar falon yana wani irin numfarfashi.

Husna ta miƙe ta bi bayansa Gwaggo tana kallonta. Ihun Husna kawai ta ji, hakan yasa Gwaggo ta shigo a gigice. A shimfiɗe suka sami M.Y jikinsa ya saki. Husna ta dinga girgiza shi tana kuka da iya ƙarfinta.

Cikin ikon Allah sai ga Abba, shima a rikice ya yi kansa yana kiran sunansa. Da ƙyar suka iya kama shi suka fita zuwa cikin motar Abba. Gwaggo saboda tsabar rikicewa magana ma ta kasa yi sai hawaye kawai ke fita daga idanunta.

Har Abba ya fara tuƙi basu daina kuka ba, shi kuma bai ce masu komai ba, gabansa ne kawai ke faɗiwa.

Taku ‘yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 33Mu’azzam 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×