Skip to content
Part 33 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Washegari da sassafe Husna ta tashi ta kama aikin abin karyawa da ita da sabuwar mai aikinta. Don haka nan da nan suka kammala ta jere komai ta koma ɗakinta ta yi wanka ta zura doguwar riga ta nemi wuri ta kwanta shiru. 

Tun tana sa ran ganin M.Y har ta soma fidda rai. Dole ta lallaɓa ta fito tana duban Larai mai aiki, ta tambayeta ko maigidan ya fito? Ta amsa mata da eh ya fito ya kwashi abin karyawansu ya koma ciki. Bata sake cewa komai ba, ta nufi kitchen suka soma aikin na rana.

Shinkafa da miya suka yi, har suka kammala babu motsin M.Y. abin ya soma damunta, amma sai danne kanta take yi bata son wani dalili da zai sa mata damuwa irin na jiya. Wannan karon bata koma ciki ba ta nemi wuri ta zauna. Sai kuwa ga su nan sun fito sai zuba ƙamshi suke yi. A hankali ta cira kai ta dube shi. Sun ɗan ɗauki lokaci suna duban juna, daga bisani Husna ta kauda kanta cikin tashin hankalin abubuwan da take karanta a cikin ƙwayan idanun M.Y ta ce,

“Barkanku da warhaka.”

M.Y ne kaɗai ya amsa mata da barka, ya wuce gurin cin abinci. Kai tsaye Salima ta bi bayansa tana wani shu’umin murmushi. Da kansu suka zuba abincin suka kama ci suna hirarsu cikin farin ciki. 

Sai gaba ɗaya Husna ta zama ‘yar kallo. Gani ta yi Salima ta ɗauki nama ta sawa M.Y a baki, sai da ya saci kallon Husna sannan ya buɗe bakin ya karɓa. 

Husna ta yi murmushi tana ji a zuciyarta lokacin jarabawanta ya zo. Addu’a take yi Allah ya bata ikon ci.

Bai ce mata za su fita ba, don haka tana barin falon suka fice gaba ɗaya. 

Shiru-shiru babu M.Y babu Salima. Sai wajen sha biyun dare suka dawo, a lokacin tsoro ya gama kama Husna. Kuka kawai take yi tana addu’ar Allah yasa lafiya. A falo ya sameta tana zazzaro idanu.

“Uncle…” Sai kuka ya ƙwace mata. Bata san lokacin da ta ƙarasa ta rungume shi ba.

“Uncle kayi min ko wani irin horo, kada ka sake horani da lafiyarka, ta fiye min komai.”

Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi. Yana ji a can ƙasan zuciyarsa bai yi mata adalci ba, bai kamata ya bar yarinya ƙarama a cikin tashin hankali ba.

Hannunsa ya maida bayanta yana bubbugawa. Gaba ɗaya ya mance da wata Salima da ke kusa da su tana kallon ikon Allah. Tana mamakin duk yadda ta kai ga juyar masa da hankali, maganin bai cika tasiri sosai ba. Muddin zai haɗa idanu da Husna sai ya ji tausayinta ya karyo masa.

“Sorry ki daina irin kukan nan.”

Wani irin kishi ya rufe wa Salima idanu ta yadda ta watsar da gyalenta, ta fizgo Husna da ƙarfin gaske ta watsar da ita, wanda hakan ya yi sanadin bugewan kanta, ta fasa ƙara

M.Y ya ƙarasa wurinta cikin gigicewa, sai kuma ya ɗago yana masifa,

“Akan me zaki yi mata haka? Kin mance matsayin Husna a gidan nan ne? Ki bi a hankali akan Husna babu ko shakka zan iya rabuwa da kowa idan aka cire iyayena. Wannan ai shirme ne. Ke baki da tausayi ne? Idan ke ce na ɗauketa muka fice irin hakan zaki ji daɗi? Haba! Yarinyar nan bata san kowa ba anan garin don me zaki dinga wulakanta min ita? To kinyi na farko kinyi na ƙarshe.”

Ya ƙarashe yana wani irin huci. A lokaci ɗaya ya koma ya kamo Husna suka shige ɗakinta. Hannunsa yasa yana liliya mata wurin da ya kumbura, tana rintse ido alamun zafi.

A ɗakin duk suka yi shiru aka rasa mai ƙarfin halin magana, har Salima ta shigo tana karkaɗa ƙafafu. Yana ɗagowa suka haɗa ido ya ji gabansa ya faɗi da ƙarfi.

“Ka tashi mu tafi bana son ganinka a ɗakin nan.”

Abin mamaki kawai ya tashi jikinsa har yana kyarma, ko sake kallon Husna bai yi ba suka fice tare. Salima ta dawo da baya tana murmushi,

“Sannu a hankali zan koya maki hankali. Tunda kika sa M.Y ya wulakantani a gaban mutane ni kuma sai nasa kin ɗanɗani tashin hankalin da baki taɓa tunani ba.”

Husna bata ce komai ba, ita dai kallonta take yi tana neman tsari da ita. Bayan ficewarta ta fashe da kuka, tana jin ciwo da kishin mijinta. Dole ta tashi ta rufe ƙofarta ta dawo ta kwanta shiru tana tunani kala-kala.

*****

Tun Husna tana tunanin abubuwan da ke faruwa masu ƙarewa ne, har aka kai matsayin da ganin M.Y yana gagararta. Dama babu maganar raba girki. Shi kansa ya fita harkarta. Da zai tafi Abuja ma da Salima ya tafi aka bar Husna ita ɗaya.

Cikin ƙanƙanin lokaci Husna ta fita hayyacinta. Dokto Salim ya kira Gwaggo a waya ya gaya mata abubuwan da ke faruwa. Hakan yasa hankalin Gwaggo ya tashi, ta kira M.Y ta ce ya tattaro da shi da matansa su zo Gombe tana son ganinsu.

Salima bata so zuwa ba, dole yasa ta bi su. Husna tana bayan mota farin ciki kamar ya kasheta.

Suna isowa ta shaƙi wani iska mai daɗi, ta lumshe ido ta buɗe sai hawaye..

Salima ta fita a motar ya juyo yana kallon Husna da take shirin fitowa.

“Ki share hawayenki kada Gwaggo ta yi zaton ina wahalar da ke ne.”

A hankali ta ɗago fararen idanunta ta watsa masa. Rabon da ya yi mata wata magana ta arziƙi har ta mance.

Bata ce masa komai ba ta fice. Gwaggo ta kafeta da idanu babu wata alama ta farin cikin ganinta. Abba ma ita yake kallo. Ko a mafarki aka ce wa Gwaggo Mu’azzam ɗin da ta sani zai iya barin marainiyar Allah ta yi irin wannan rayuwar ba zata taɓa yarda ba. Husna ta koma daga ita sai karan hanci. Yadda take kallon Husna yasa mata rauni. Shi kansa sai ya ji wani irin tashin hankali ya mamaye shi. 

Ya sani babu abin da Husna take so kamar kwanciya a gefen kafaɗarsa, ya sani ta fi ƙaunar ɗumin jikinsa fiye da komai. Amma duk yasa ƙafafu ya yi fatali da hakan, duk ya mance wahalar da tasha akansa, ya zaɓi wata mai saɓawa Mahalicci. Kunyar Gwaggo ya kama shi.

Basu ankara ba sai kukan Gwaggo suka ji, da kuma hawaye masu yawa da suke kwaranyo mata. Tausayin Husna ya huda zuciyarta. Da sauri Husna ta ƙaraso ta ƙanƙameta itama ta fasa kuka, mai nuni da dama can kukan yana kusa neman sanadi take yi. 

Abba yana tsaye yana kallonsu idanunsa sun kawo ƙwalla. Ba zai taɓa mance da taimakon Husna ya sami dawowa cikin iyalansa ba. Ba zai mance Husna ta zaɓi farin cikinsu akan nata ba. Abba ya dawo da kallonsa kan M.Y kallo mai cike da tuhuma, kallo ne da yake nufin abubuwa da yawa. Hankalin M.Y idan ya yi dubu to ya tashi. Salima kuwa ko a jikinta tsayawa ta yi ta zuba masu idanu tana mamakin irin wannan so da suke gwadawa akan Husna. Ya zama dole ta raba wannan ƙaunar idan ba haka ba zata sami matsala.

Kukan da Husna take yi, yafi na Gwaggo hakan yasa Gwaggo ta tsagaita da nata kukan ta jawo Husna ɗakinta. M.Y yana shirin biyo bayansu ta waiwayo ta aika masa da wani irin kallo,

“Ku wuce sashenku.”Abin da ta iya furtawa kenan. M.Y ya dubi Salima ya ce,

“Ki wuce ciki zan shigo.”

Daga haka ya bi bayan Gwaggo. Ba zai iya ganin mahaifiyarsa tana hawaye kuma ya iya tafiya wani wurin ba.

Abba ya shiga shima ƙaton falon wanda M.Y yasa aka fasa aka gyarawa Gwaggo ɓangarenta tunda yanzu tana buƙatar wuri mai girma saɓanin da da take ganin me za ta yi da ƙyale-ƙyalen duniya.

Tunda Husna ta ƙudundune a jikin Gwaggo ta ƙi ɗagowa. Ta riga ta yankewa kanta ta dawo kenan. Bata taɓa yi wa Gwagogo musu ba, amma a wannan karon idan aka matsa sai ta koma gidan M.Y za su iya nemanta su rasa.

Kuyi haƙuri da ni. 

Ta ku har kullum ‘yar mutan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 32Mu’azzam 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×