Skip to content
Part 32 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Husna ta kalmashe hannunta ta zura mata idanu tana son ganin iya gudun ruwanta.

“Sunana Salima. Ko kin ganeni?”

Salima ta furta da izza. Husna ta yi murmushin takaici ta ce,

“Baki buƙatan sake sanar da ni ko wacece ke. Mutanen banza kamarki ba lallai a iya mance su cikin sauri ba. Me ke tafe da ke? Ina da abubuwan yi.”

A gadon ta yi wa kanta mazauni tana kallon ko ina, sannan ta ce,

“Nazo insanar da ke zancen kome da zan yi ne. Ina nufin kayan da na baki aro zaki maido min.”

Husna ta ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali ta ce,

“Uncle ba aro yake a gareni ba, domin jinina ne ko babu aure. Haka zalika baya ɓoye min komai, ya gaya min tun daga tahowarki har zuwa ɗakinki da ya yi jiya. Me kike son sake sanar da ni wanda ban sani ba?”

Bakin Salima a buɗe take kallonta. Lallai ita M.Y ya maida sha ka tafi. Jikinta ya yi mugun sanyi, da ta shigo ne ta gaya mata komai dan ta ƙuntata mata, sai kuma ga shi reshe yana son juyewa da mujiya.

“Don Allah ta shi ki bar min ɗaki ina da abubuwan yi.”

Husna ta faɗa tare da nuna mata hanyar ficewa, tana kallonta ido cikin ido. Tana son Salima ta bar ɗakin tun kafin ta fashe da kuka a gabanta har ta gane laggonta.

Babu musu Salima ta miƙe ta ce,

“Ki jira dawowana. Wallahi sai kin fita da ƙafafunki kin bar min M.Y ni ɗaya. Ki tambayi sauran matansa, ko da can ban yarda na raba kwana da wata ba, bare kuma yanzu. Ki saurari kaidina.”

Husna ta lumshe ido ta jingene da bango. Da ƙyar ta iya furta,

“Allah ya fi ki Salima.”

Har Salima ta fice Husna bata iya motsawa ba, bare ta rufe ƙofar. A haka hawaye suka kama gudu a kuncinta. Bata damu da ta goge su ba, ta fi buƙatan su fito ɗin ko hakan zai sa ta sami sasaauci.

Mantuwa ya yi don haka ya dawo da gaggawa, anan ya sameta tsaye ga dukkan alamu ta daɗe a tsayen. Ga kuma ƙofa a buɗe. Tsoro da firgici suka shige shi a lokaci guda.

“Husna lafiyarki ƙalau kuwa? Menene?”

Ya haɗa mata tambayoyin a lokaci guda. Tana buɗe ido ta tabbatar da shi ne, kawai ta rungume shi tsam jikinta yana karkarwa. Allah kaɗai yasan girman son da take yi masa. Furucin Salima ya gigitata, bata ƙaunar wani dalili da zai sa ta rabu da shi. 

Shima ƙanƙameta ya yi tare da janyota zuwa kan gado. A hankali yake bubbuga bayanta har ta daina kukan sai ajiyar zuciya.

“Faɗa min babyna waye ya taɓa min ke? Kada ki ɓoyewa mijinki komai kinji?”

Ya ɗago fuskarta yana sake goge mata hawayen. A hankali ta yi magana, wanda da ace bai kasa kunne ba ba zai taɓa ji ba,

“Babu komai. Bana son watarana ka rabu da ni ko ka juya min baya.”

Murmushi ya wadaci fuskarsa. Ya dawo da ita kafaɗansa yana shafan gadon bayanta,

“Har abada ba zan taɓa juya maki baya ba. Ki daina irin wannan tunanin kada depression ya kama min ke.”

Luf ta yi a jikinsa tana jin wani tarin natsuwa yana ziyartarta. A zahiri kuwa tsoron Salima ne cike da zuciyarta.

Hijabinta ya ɗauko mata yasa mata, sannan ya ɗauki abin da ya zo ɗauka ya kamo hannunta suka fito tare.

“Ina zamu je Uncle?”

Ta tambaye shi cike da rashin son fitan. Bai bata amsa ba har sai da ya rufe ƙofar sannan ya ce,

“Tare zamu koma wurin meeting ɗin ba zan iya barinki ke ɗaya ba.”

Bata sake cewa komai ba yana riƙe da hannunta har suka fito. Ya zagaya ya buɗe mata ƙofar motar, sai da ya tabbatar da ta shiga sannan ya rufeta. A lokacin idanunsa suka sarƙe da na Salima. Ya ɗan kauda kansa kamar bai ganta ba, ya zagaya ya shiga. Husna ta kafeta da idanu har suka bar harabar hotel ɗin. 

Tabbas ta hango tashin hankali a cikin ƙwayar idanun Salima hakan yasa ta nausa cikin tunani. 

A cikin ɗakin meeting ɗin duk suka bi shi da kallo, ganin ya shigo da Husna ya nema mata wuri ta zauna sannan ya dube su ya ce,

“Ku yi haƙuri na taho da matata nan wurin dan insami ƙwarin guiwar yi maku dukkan bayanan da kuke buƙata.”

Gaba ɗaya suka hau dariya tare da tafi. Abin ya burge mutane da yawa daga ciki. A yayin da wasu suke ganin Allah ne ya kama shi ‘yar ƙaramar yarinya tana son zauta shi. 

Sun yarda da abin da M.Y ya ce domin kuwa bayanan da yake yi masu a yanzu ya fi gamsar da su fiye da na ɗazu. 

Bayan sun tashi kai tsaye ya nausa da ita wuraren shaƙatawa suka yi ta nishaɗi. Nan da nan Husna ta mance da wata aba wai Salima.

Shi kansa ya mance da Salima har sai wajen Magriba sannan ta faɗo masa a rai, dalili ma saboda kiran da ta yi masa ne. Bai ɗauka ba har suka dawo hotel ɗin. Bayan ya yi Sallah ne ya fice zuwa ɗakinta. Husna tana kula da duk abin da yake yi, bata nuna masa ta gane komai ba. 

Faɗa sosai suka yi da Salima a lokacin da ya juya zai fice ta fashe da kuka tana roƙonsa kada ya tafi. Ya dawo yana kallonta ido jajir ya ce,

“Kin sanni kin san halina bana son raini. Duk irin son da nake yi wa mace da zarar naga tana son rainani zan kiyayeta. Sannan ina ƙara jan kunnenki ki daina magana kina sa Husna a ciki, ko ba komai ƙanwata ce kuma matata.”

Kalamansa sun sake ɗaga mata hankali amma sai ta danne tana bashi haƙuri. Taso ta gaya masa ta je har wurin Husna, amma ganin Husna bata gaya masa ba, yasa itama ta rufawa kanta asiri ta yi shiru.

“Kasan ina sonka, ina sonka me ya sa zaka dinga azabtar da zuciyata? Ka amince min mana mu dawo da aurenmu.”

Sai da ya rabata da jikinsa sannan ya koma ya zauna.

“Nasan kina sona, kema kinsan ina sonki. Na gaya maki ki bani lokaci zan je inshawo kan iyayena tukun. Bana son matsala kin ganni nan, iyayena sune rayuwata bana aikata komai ba tare da yardarsu ba.”

Anan Salima ta dinga jansa da hira da makircinta har ya kai ƙarfe goman dare ba tare da ya sani ba. A lokacin da ya dubi agogon wayarsa duk sai ya shiga damuwa. Babu shiri ya yi mata sallama ya fice da sauri. Ita kuwa farin ciki ne a ranta ko ba komai zata kuntatawa Husna kamar yadda itama ta yi mata ɗazu.

Yana shigowa ya sameta ta lulluɓa da bargo ya buɗe ya shiga ciki tare da jawota jikinsa. Jikinta ya yi zafi sosai alamun zazzaɓi hakan yasa ya cire bargon gaba ɗaya yana dubanta. Idanunta a rintse suke amma kuma hawaye basu daina sauka ba. 

“Baby baki da lafiya ne?”

A hankali ta ware idanunta da suka yi ja, ta sa hannu ta goge hawayen ta ce,

“Kaina ne ke ciwo amma nasha magani.”

Ya kafeta da idanu yana son gane wasu abubuwa da take ƙoƙarin ɓoye masa,

“A ina kika samo maganin?”

Shiru ta yi kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta daure ta ce,

“Da su na zo.”

Bai ce komai ba, ya nufi banɗaki ya haɗa mata ruwan wanka, tana kwance tana kallon ikon Allah. Ya cire mata kayan jikinta ya ɗagata kawai ya nufi banɗaki da ita. Girgiza kai take yi tana cewa,

“Don Allah kada ka sanyani a ruwa na yi wanka.”

Bai bi ta kanta ba ya tsomata a kwamin wankan. A tare suka saki ajiyar zuciya. Ta kafe shi da ido tana son yin magana, amma kwarjininsa ya hana hakan.

Tana jinsa ya haɗe bakinsu wuri guda, bata yi yunƙurin hana shi ba, har sai da ya ji ya gaji dan kansa ya ƙyaleta. Sai da ya tabbatar ruwan ya ratsata sannan ya kamo hannunta ta fito ya sanya tawul yana goge mata jiki. 

Duk yadda taso ta ci gaba da kauda kanta akansa hakan bai yiwu ba, domin M.Y irin mazan nan ne da suka san kan lallashin mace, da iya bata kulawa. A daren nan bai rabu da ita ba, sai da ya tabbatar ya cire mata duk wata damuwa.

Bayan sun koma Kaduna ne ta fahimci gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa. Ga yawan barci musamman idan yana tare da ita. Abubuwa sun taru sun yi masa yawa. 

Yau tana fitowa daga ɗakinta ta ɗebo ƙananan kayansa da yake bari a ɗakinta zata kai nasa ɗakin, har ta kawo bakin ƙofar ɗakinsa ta ji murya yana waya wanda ga dukkan alamu da Gwaggo yake magana.

“Gwaggo duk abin da kuka ce haka za ayi, ita Husna nasan bani da matsala da ita. Na yi magana da Abba ya ce min babu ruwansa ba zai iya sa baki ayiwa ‘yarsa kishiya ba, amma ina iya tambayarki.”

Shiru bata ji me Gwaggon take cewa ba, amma ta ji sautin muryarsa yana mata godiya tare da alƙawarin zai gayawa Husna idan ta yarda zai sanar da ita.

Da ƙyar Husna ta janyo natsuwa ta ɗorawa kanta sannan ta shigo da Sallama. Ya dubeta na wasu ‘yan daƙiƙu, ya sunkuyar da kai. Bayan ta gama jera kayanne ta nufi hanyar fita, bata son dalilin da zai sa ta tsaya kusa da shi. 

“Husna dawo ina son magana da ke.

A hankali ta dawo ta zauna gefen gadonsa tasa hannu ta janyo wani riga tana ƙoƙarin ninkewa.

“Ki yi haƙuri da abin da nake shirin gaya maki. Kin fi kowa sanin ina sonki. Ƙaddara tasa zan dawo da Salima ɗakinta. Amma sai kin amince.”

‘Namiji kenan! NAMIJI MUTUM!’

Husna ta furta a zuciyarta, a lokacin da dukkan jikinta ya kama rawa. Ba tsoron shigowar wata cikin gidanta take yi ba, tsoron dalilin da zai sa ta rabu da mijinta ko kuma a daƙile zaman jin daɗin su, shi ta fi ji.

“Lahh wannan ai ba wata matsala ba ce. Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu.”

Ta furta cikin sakin fuska da fara’a. Wanda da ace zaka leƙa zuciyarta sai kayi zaton gobara ce ta kama. Ita kanta ta yi mamakin jarumtarta.

Shima idanu ya zuba mata yana son dole sai ya hasaso yanayin da take ciki, amma fir ta ƙi bashi daman hakan. 

Rigar ta ɗauka ta adana sannan ta ce,

“Bari induba miya a wuta.”

Bai iya cewa komai ba har ta fice. Jikinsa asanyaye ya kira Gwaggo ya gaya mata yadda suka yi da Husna. Ita kanta Gwaggon sai da ta ji shakka akan abin da ya faɗa. Ta yanke hukuncin zata kira Husnan da kanta. Duk da haka sai da tausayin Husna ya cika ko ina a cikin zuciyarta. Da ace ɗanta zai ji shawararta da ya haƙura da auren nan. A lokaci guda Gwaggo ta botsare ta ce ita bata yarda da wannan auren ba, kawai ya haƙura. Idan kuma ya zama dole sai ya ƙara aure to ya nemi wata amma ba Salima ba.

Hankalin M.Y idan ya yi dubu to ya tashi. A yanzu ji yake idan bai dawo da Salima ba zai iya mutuwa. Babu shiri ya nufi ɗakin Husna. Wanda har lokacin hawaye sunƙi sauka daga idanunta. Azaba kawai take ji a cikin zuciyarta irin wanda bata taɓa jin irinsa ba.

Zama ya yi kusa da ita ya kama hannayenta,

“Husna ki taimakeni ki kira Gwaggo a waya ki ce mata ta yi haƙuri ta amince da auren nan don Allah.”

Ɗagowa ta yi ta zuba masa idanu. Hakan yasa kunya ya lulluɓe shi. Har mamakin irin ƙarfin halinsa yake yi. Sai da ta ɗan kauda kanta sannan ta ce,0

“Yanzu dai aiki zan yi, zuwa anjima zan kirata insha Allahu.”

Ko ɗaga ƙafafunsa ya kasa yi. Ya rasa me ke yi masa daɗi. Shi kansa zuciyarsa raɗaɗi take yi. Rungumeta ya yi tsam a jikinsa yana shafa bayanta. Sai a lokacin wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta. Da sauri tasa hannu ta goge tun kafin ya gani. Bata san lokacin da ta sami ƙarfin halin furta magana ba,

“Duk abin da ka ga ya faru da sanin Allah. Dama komai a rubuce yake. Babu wanda ya isa ya kaucewa ƙaddararsa.”

Kalamanta sun ɗan taimaka wajen kwantar masa da hankali. Hannunsa ta jawo suka koma suka zauna. Ta amshi wayar hannunsa ta danna lambar Gwaggo. 

Sosai ta saki jiki tana yi wa Gwaggo hira, har suka gangaro kan maganar dawowar Salima. Ta tabbatar mata da ita bata da matsala. Husna har da marerecewa Gwaggo har dai ta amince. Dama so take ta tabbatar da Husnan bata cikin damuwa. 

Tana kallon farin ciki a idanun mijinta ta bi shi da kallo kawai tana ji a ranta koma menene ba lafiya lau ba. Ya zama dole ta sake dagewa akan addu’a fiye da wanda take yi. 

Tun bayan da Gwaggo ta amsa ya saki ajiyar zuciya. Ya jawota jikinsa ya ƙanƙameta yana sakin ajiyar zuciya da sauri da sauri. Addu’a take tofa masa, bata ankare ba sai jin saukar numfashinsa ta yi. Dama jiya tana lura da shi kwata-kwata bai yi barci ba. 

Shiru ta yi tana ji a zuciyarta kamar wani ƙalubale ke shirin tunkararta.

Kiran da ake yiwa wayarsa ne yasa ta dubi lambar. Salima ce kamar mayya, ta ƙi daina kiran. Hakan yasa ta kashe wayoyin gaba ɗaya ta gyara masa filo sannan ta sauka ta fito falo.

Tafukan hannayenta tasa a tsakanin fuskarta ta matse kanta a cikin cinyoyinta ta fashe da kuka mai cin rai. Kuka kawai take rusawa da iya ƙarfinta. Jikinta har wani rawa yake yi saboda tsabar kuka.

Sai da ta yi ma’ishinta sannan ta haƙura, ko ba komai ta ji sauƙi a cikin zuciyarta.

Tana kallon yadda ake ta shirye-shirye kamar wanda zai yi sabon aure. Ko ɗan lallashin nan da yake mata yana kwantar mata da hankali ya daina. Husna dai ta rungumi Alqur’ani da carbinta kullum tana maƙale da su. Duk ta fara fita hayyacinta, duk da irin dauriyar da take yi tana kauda kai.

Sun so su zuba kaya ya ce gidansa babu wurin zuba wasu kaya kawai daga ita sai kayan sawanta za ta zo. 

A daren yau aka kawota, da gogaggun ƙawayenta. Dama su Abba basu sami zuwa ba, tunda ba biki ne sabo ba, sun dai yi alƙawarin idan ankwana biyu za su zo.

Ko a yau ɗin ma da aka ɗaura auren kuma aka kawota cikin gidan Gwaggo tana manne da waya tana yi wa Husna nasiha. 

Tana ɗakinta ya shigo yana dubanta, yasha manyan kaya abinsa kamar wanda ya auri budurwa. Leda ya miƙa mata ta daure ta karɓa ta ajiye a gefenta. 

“Zo mu je ki rakani ɗakin Salima.”

Babu musu ta miƙe, dama da hijabinta. Bayan sun zauna ne ya kirawo Salima ta fito daga ita sai rigar barci tana yamutse-yamutse. M.Y ya ɗan yi masu nasiha ya kuma jawo hankalin Salima a matsayinta na mai shekaru da ta kama kanta, sannan baya son hayaniya ko tashin hankali.

Husna ta tashi tana murmushi

“To ni zan kwanta. Sai da safenku.”

M.Y ya kasa amsawa. Tausayin Husna ya darsu a zuciyarsa. Yaushe rabon da su raba makwanci? Abubuwan alkhairin da ta yi masa suka dinga yawo a tsakiyar kansa.

Husna tana shiga ɗakinta ta jingine da ƙofa ta sulale ƙasa ta zauna tana jin zuciyarta tana tafarfasa kamar wuta. Hannunta ta kai ta dafe daidai wurin tana ambaton sunan Allah.

Kuka sosai take yi, kukan tausayin kanta, kukan baƙin ciki kuka mai dalili. Abubuwa da yawa take tunawa waɗanda suka taru suka cushe a zuciyarta. Ina ma Gwaggonta tana kusa? Wannan dare sunansa baƙin dare a wurinta. Dare ne mai tsawo wanda ganin wayewar gari zai zame mata abu mai wahala. 

A hankali ta ja ƙafafunta ta zauna a ƙasa ta kwantar da kanta akan gadon tana kuka harda sarƙewa. M.Y kawai take hangowa kwance tare da Salima. Tarairayar da yake yi mata yau zai maida shi wurin tsohuwar matarsa.

Shi kuwa M.Y har ya yi wanka ya kintsa hankalinsa ya gaza kwanciya. Yanayin da ya ga Husna abin ya tsaya masa a rai. Tausayin yarinyar yake ba zai iya rintse idanunsa ba tare da ya je ya lallasheta ba. 

Salima ta dube shi da mamaki,

“Ina kuma zaka je?”

Sai da yakai ƙofa sannan ya ce,

“Zan ɗauko abu ne.”

Ta zauna cike da zargi a zucuyarta.

Tura ƙofarta ya yi ya ji ta a buɗe don haka ya tura kansa.

Ya daɗe tsaye akanta bata sani ba. Yau shi ne karon farko da ya taɓa ganin damuwarta ƙarara akan bikin nan. Amma ko alama bata taɓa nuna masa komai ba. Sau tari yakan zauna ya yi tunanin ko dai bata sonsa ne? Indai ƙaramar yarinya kamar Husna zata iya irin wannan dauriyar shi me ya sa bai iya haƙura da Salima ba? 

A lokaci guda ya kirawo kansa da mara adalci wanda ya kasa farantawa Husna. Ada can baya yana gane damuwar Husna ko da ace bata furta ba, amma wannan karon aure ya rufe masa idanu bai ankara ba har sai bayan da aka ɗaura aka kawo masa matarsa. 

Ji ta yi andafata hakan yasa ta ɗago a gigice. Da gaske shi ne a gabanta ba mafarki take yi ba. Bata san lokacin da ta rungume shi ba, ta sake fasa kuka jikinta yana kyarma.

Ɗago kanta ya yi ya haɗe bakinsu wuri guda. Dukkansu suka yi shiru sai bugun zuciyoyinsu da ke fitowa da ƙarfi. Sai da ya tabbatar ta yi lakwas, sannan ya ɗauketa ya ɗora akan gado ya jawo masu bargo. 

Ta kasa yin magana shi kuma bai daina yi mata alamun lallashi ba.

“Sorry baby. Ke kike ƙarfafa min guiwa, ganin hawayenki zai sa inshiga damuwa. Ki yi haƙuri ki yafe min, na ƙuntata maki.”

Ajiyar zuciya kawai take yi da ƙarfi. Bakinsa yasa daidai kunnenta yana hura mata iska a kunnen. Cikin hukuncin Allah barci sama-sama ya ɗauketa. Ya yi ajiyar zuciya. Har ya rufeta da bargo ya manna mata filo, sai kuma ya dawo ya yi mata addu’a ya tofa mata. Ya jima a sunkuye Yana kallon kyakkyawar fuskarta.

Husna ba irin macen da namiji zai kauda idanunsa akanta ba ce. Kiss ya manna mata a goshi sannan ya ce,

“Good night Dear.”

Ya fito jikinsa a sanyaye, kukan da ya ganta tana yi ya firgita shi, ya sanya shi a cikin damuwar da baya tunanin zai iya rintsawa. 

Salima da take jin zuciyarta kamar ta mutu bayan taga inda ya nufa ta dafe ƙirjinta tana fatan ta danne komai tun kafin ta ɓata daren da ta ci buri akansa. Ba ƙaramin kewar M.Y ta yi ba, ta ƙosa ta sake jin lafiyayyan jikinsa a tare da ita. 

Wani turare ta ciro ta goga ta ɗibi magani ta zuba a cikin drink ɗin ta jujjuya. Don haka ne yana shigowa ya shaƙi ƙamshin sai ya ji gaba ɗaya ya mance da wata damuwa akan Husna. Ya zauna ta bashi drink ɗin anan ma yana sha ya ji duk duniya Salima ce kawai matarsa. 

A wannan daren Salima ta murji M.Y yadda take so.

Ita kuwa Husna yana ficewa ta farka, sai dai raɗaɗin da take ji a zuciyarta ta ragu, don haka kawayen ne kawai ya kasa tsayuwa. Tana da buƙatar ganawa da Mahaliccinta domin tasan sharrin Salima tasan bata shigo gidan nan ba sai da ta shirya.

To muje zuwa dai…Taku har kullum Fatima Ɗan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 31Mu’azzam 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×