Husna ta dinga juye-juye barcin ya gagari idanunta. Wata soyayyarsa ce take sake mamaye zuciyarta. Filonta ta sake jawowa ta rungume tana lumshe idanu. Wani irin yanayi ta shiga na tunanin mijinta. Ya kasance daban a cikin maza. Lallai aure sirri ne da da ba haka ba zata iya bugun ƙirji ta ce a wajen soyayya mijinta ya yi wa sauran mazaje fintinkau.
Har gari ya waye Husna bata fito ba. Shi kuma yana can ya cika ya yi tam! Ita kanta Saliman ta kasa gane kansa. Ya fito cikin shirinsa yana ta kallon ƙofar ɗakin Husna ko. . .