Skip to content
Part 36 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Husna ta dinga juye-juye barcin ya gagari idanunta. Wata soyayyarsa ce take sake mamaye zuciyarta. Filonta ta sake jawowa ta rungume tana lumshe idanu. Wani irin yanayi ta shiga na tunanin mijinta. Ya kasance daban a cikin maza. Lallai aure sirri ne da da ba haka ba zata iya bugun ƙirji  ta ce a wajen soyayya mijinta ya yi wa sauran mazaje fintinkau.

Har gari ya waye Husna bata fito ba. Shi kuma yana can ya cika ya yi tam! Ita kanta Saliman ta kasa gane kansa. Ya fito cikin shirinsa yana ta kallon ƙofar ɗakin Husna ko zai ga fitowarta. Nan ma shiru. Haka ya gama karyawa ya fice daga gidan, babu wasu kalamai masu daɗi da ya samu yau. Duk sai ya ji babu daɗi, ya kasa aiwatar da komai.

Haka ya dawo gida, sai a lokacin ya ganta a falo tana zaune ita kanta babu wata walwala a tare da ita. Sannu da zuwa ta yi masa ya yi banza da ita, kawai sai ta yi murmushi.

A daddafe ya ƙarasa kwanaki biyunsa. Ita kuwa tana karɓar girki ta fara shirin tarban mijinta. Tana kula da shi yadda yake shan ƙamshi, ta ƙaraso ta sakala hannunta a cikin rigarsa tana murmushi.

“Uncle fushi kuma? Sorry ba zan ƙara ba.”

Ta ƙarashe tare da sunkuyawa ta riƙe kunnenta alamun ta tuba. Murmushi ya yi ya miƙa mata hannu ta kama ya jawota jikinsa,

“Kin horani da yawa baby me ya sa? Kinsan irin wahalar da kika bani kuwa?”

Tasa hannu ta ɗago haɓarsa ta sumbace shi, sannan ta ce,

“Sorry Uncle… Fushin Allah nake guje maka. Idan ranar girkina ne kayi duk abinda ka gadama da ni, ka cinyeni ma na baka izini.”

Gaba ɗaya suka yi murmushi. Salima tana tsaye a bayansu tana jin su, kawai ta yi kukan kura ta cafko wiyan rigar Husna tana bugu.

“Yau sai kin bar duniyar Wallahi! Ke kin isa! Waɗanda suka fi ki ma sun kasa bugawa da ni bare ke banza a banza.”

M.Y ya fara ƙoƙarin ƙwace Husna amma abin ya ci tura. Da ƙyar ya samu ta saketa. Husna ta yi kitchen da gudu ta ɗauko wuƙa. Tana jin gara ta zame mata mahaukaciya ƙila zata rabu da harkarta.

Da gudu ta biyo Salima wanda suka shiga tsere. M.Y sai ya gigice ya rasa me ke yi masa daɗi.

“Husna! Wai kema mahaukaciyar kika zama kamarta?”

Husna ta tsaya tana haƙi,

“Ka ƙyaleni Uncle! Salima mahaukaciya ce, dole sai angwada mata hauka sannan zata natsu. Wallahi da kin tsaya sai na farka cikinki, na shafe tarihinki a duniya. Idan kuma kina ganin ƙarya nake yi ki gwada sake taɓa jikina kisha mamaki.”

Da gaske Salima ta tsorata, domin duk haukanta ba zata iya kashe mutum ba. Lallai ta yarda ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka idanu. Bata taɓa tunanin akwai ranar da Husna zata iya razanata ba.

Da gudu ta shige ɗakinta ta rufe da key. M.Y ya yi murmushi domin ya sani sarai barazana ce kawai da ƙarfin hali irin na Husna. Hannunsa ya ware ya nuna mata ƙirjinsa, ta saki wuƙar ta ƙarasa ta rungume shi sai kuka. Ya dinga shafa kanta yana raɗa mata kalamai masu sanyi har ya samu ta yi murmushi, sannan ya ɗagota yasa hannu yana ɗauke hawayen fuskarta.

“I love You baby. Na yi kuskure da na dawo da Salima, ga shi nan yanzu tana so ta sa mini ciwon kai.”

Husna dai bata tanka ba, domin ta fahimci wasu mazan munafukai ne musamman masu mata fiye da ɗaya. Ƙila idan ya shiga girkinta ya gaya mata wani abun kuma daban.

  Tun daga wannan rana Salima ke tsoron Husna, haka zalika ta sakar mata mara. Shi kansa M.Y sai ya fi samun kwanciyar hankali.

  Kwanaki biyu zazzaɓi da ciwon kai suka addabi Husna. Da ƙyar ta amince ya kaita asibiti. Gwajin farko aka tabbatar da ciki gareta. M.Y ya dawo gida bakinsa har kunne. A falo ya ɗagata sama yana ta juyi da ita. Daga ƙarshe ya kira Gwaggo ya gaya mata. Saboda farin ciki sai da Gwaggo ta kai goshinta ƙasa ta yi godiya ga Ubangiji akan amsa mata addu’arta da ya yi.

Salima ta gigice da jin abin da M.Y yake gayawa Gwaggo. Shi kenan komai ya gama lalacewa. Shi kenan Husna ta shiga gabanta. Kuka sosai ta koma ɗaki tana rusawa. Ta ci alwashin sai ta zubar da cikin nan ko ta halin ƙaƙa. Da ace bata san halin Husna ba sai ta ce bin maza take yi, ta yaya shekara da shekaru ko ɓatan wata babu wacce ta taɓa yi a gidan M.Y sai Husna da ta zo daga baya baya? Ita da take tunanin M.Y bai haihuwa? Ƙawarta Shukra ta kira akan lallai ta zo ta rakata gidan wani malami da aka tabbatar mata da aikinsa tun kafin ka bar wurinsa yake ci.

A falo ta same su Husna tana ta shagwaɓa shi kuma ya lalace agurin tattalinta. Ko kallo basu isheta ba ta kama hanyar fita. Cikin kakkausar murya ya ce,

“Ina zaki je?”

Wani irin kallo ta yi masa, domin shi kansa haushinsa take ji.

“Ka damu da ni ne da zan gaya maka inda zanje?”

M.Y ya haɗiyi wani abu, a duniyarsa ya tsani raini ko ƙanƙani don haka ya ce,

“Ok. Idan kika fita kada ki dawo.”

Cak! Ta ja ta tsaya daga ci gaba da tafiyan da ta yi. Cikin rauni ta ce,

“Haba M.Y da wanne zan ji? Kasan uzurina ne da zaka sa min takunkumi? Gidanmu zanje Babana bai da lafiya.”

Husna bata son ta sanya masu baki a maganarsu, don haka ta dube shi da idanunta ta yi masa magana. Sai da ya yi shiru, daga bisani ya ce.

“Ki tafi. Kada ki daɗe.”

Bata tsaya jiran wata-wata ba ta sa kai ta fice.

Sun yi tafiya mai nisa sannan suka isa bukkan bokan. Ta zayyane masa komai ya gama abubuwansu na tsubbu ya ɗago ya ce,

“Idan kika ga yaron nan bai zo duniya ba, ki tabbata kashe uwar kika yi.”

Salima ta dafe ƙirji,

“Namiji zata haifa?”

Bokan ya gyaɗa kansa. Ta zauna dirshen a gabansa ta ce,

“Ka kasheta kawai. Bana son Jin ko da sunanta a kasheta.”

Bokan ya yi ta sheƙa dariya, daga bisani ya bata wani magani ya ce ta zuba mata akan gadonta idan ta yi hakan shikenan angama kuma…

Suna hanyar dawowa farin ciki ya rufe Salima. Gudu kawai take shararawa kasancewar bata mance umarnin da M.Y ya bata ba. Tana cikin gudu wata babbar mota ta afka masu babu zato babu tsammani.

Da ƙyar aka samu aka cirosu kai tsaye akayi babban asibiti da su.

Dokto Salim ya kira M.Y a waya ya gaya masa halin da Salima take ciki da kuma inda ta yi hatsarin a hanyar Zaria. Mamaki ya kama M.Y ya ce shi ai gidansu ta ce masa zata je. Dokto dai ya roƙe shi akan ya zo ɗin ya ganta dan yana tunanin sai ancire ƙafafunta, dan gara ma ƙawarta da ita.

M.Y ya kira Babanta a waya yana tambayarsa ko Salima ta je gidansa? Ya ce bai ganta ba. Ya gaya masa halin da ake ciki. Don haka duk suka dugunzuma zuwa asibitin. Bai so ya taho da Husna ba, sai dai yadda ta gigice masa ne yasa ya taho da ita.

Dukkansu suna tsaye akan Salima da take cikin azaba. A lokacin Allah ya bata iko ta buɗa bakinta ta fara gaya masu tuggunta da kuma amso maganin da ta yi dan ta kashe Husna.

M.Y ya girgiza kai, yana jin takaici ashe asiri ta yi masa har ya dawo da ita. Shi ya sani, indai yana hayyacinsa babu dalilin da zai sake shigo da Salima cikin gidansa.

“Salima kin fahimci duniya ba abakin komai take ba ko? Ina amfanin ki dage sai kin ga bayan wani? Shi Allah ba azzalumin bawansa bane sai wanda ya zalunci kansa. Kije na sakeki saki uku, ko sunana kika sake ambata ban yafe maki ba. Na jima ina addu’a Allah ya bani haihuwa, a zatona zaki tayani murna, sai kika gwammace gara ki kashe min uwar da ɗan. Allah ya fiki ya kuma nuna maki ishararki.”

Ya juya yana neman Husna. Ganinta ya yi ta kafe Salima da ido tana ta kuka. Bai ce komai ba ya ƙarasa ya kamo hannunta suka fice daga wurin. Ita kuwa ihu take tana cewa ya taimaketa ya yafe mata.

Yana komawa gida ya kira Abba ya gaya masa komai. Abba kuma ya sanar da Gwaggo, duk suka yi shiru suna jinjina ƙarfin rashin imani irin na Salima.

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya, M.Y yana kulawa da cikin Husna. Ita kuma Salima ta zama gurguwa hatta iyayenta basu bin ta kanta ta zama abar tausayi. Yau ɗin ma Husna ce a gaban motar M.Y sai rigima take sa masa, gaba ɗaya cikin nan ya maidota rigimammiya. Gani ta yi ya tsaya a gefen hanya ya kafe wani wuri da idanu. Ta waiwayo tana dubansa,

“Uncle menene?”

Da hannu ya nuna mata wani mahaukaci, ta jima tana kallonsa bata gane wanene ba, don haka ta waiwayo,

“Waye shi?”

Sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce,

“Alhaji Mu’azu ne. Kinsan ranar da muka je ɗauko Abba mun ƙona zoben nan. Ance da yawa sun mutu, amma manyan duk haukacewa suka yi. Shi dai Oga Saleh da yaransa hukuncin kisa aka yanke masu. Shi kuma Alhaji Mu’azu kin ga dai ƙarshensa. Shiyasa yana da kyau ka aikata alkhairi musamman saboda gaba.”

Husna ta jima tana kallonsa cike da al’ajabi. Tunanin ‘ya’yansa yasa hawaye zubo mata.

Kwanaki biyu tsakani yake gaya mata ya biya duk basussukan da ake binsa, yanzu ya buɗewa Yunusa ƙaton kanti don ba zai mance alkhairin yaron ba.

Cikin hukuncin Allah Husna ta santalo ƙaton yaronta namiji, mai kama da ubansa. Gwaggo da Abba sun kasa haƙuri don haka suka tattaro suka zo ganin jika. Har Salma ba abarta abaya ba.

Yaro ya ci Sunan Abba wato Yusuf ana kiransa da Ashraf.

Wani sabon shafin soyayya ne ya buɗu a tsakanin M.Y da Husnarsa ta zama ‘yar gata ‘yar lele, da ita da ɗanta. Tuni ta koma Makaranta shi kuma kasuwancinsa yana ta sake haɓaka. Ga kamfaninsu suna ƙara ririta shi.

Alhamdulillahi! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Na kammala wannan labari mai suna MU’AZZAM. Ina roƙon duk wani kuskurena a yafe min, duk ɗan adam da ajizi ne.

Don Allah duk wa’azin da ke cikin labarin nan a ɗauke shi wanda bai da amfani kuwa a watsar da su..

Na sadaukar da labarin nan gaba ɗaya agun ‘yar uwar da babu kamarta,

Aisha Ibrahim Garba (Ɗan Borno)

ALLAH YA SAKA MASU DA ALKHAIRI YA SANYA MIN SU A CIKIN ALJANNA DA SAURAN AL’UMMAR MUSULMAI.

Ni Fatima Ibrahim Garba ɗan Borno nake yi maku fatan alkhairi. Sai mun sake haɗuwa a sabon labarina mai suna HAƘƘI!

<< Mu’azzam 35

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.