Gwaggo tana zaune shiru, ta rafka tagumi. Ita kaɗai tasan irin tunanin da take yi. Husna da Salma suka shigo da Sallamarsu. Duk suka dubeta, a lokaci guda suka ƙara so suna tambayarta ko lafiya. Wannan karon babu murmushin da takan yi masu idan tana son kauda tunaninsu.
“Lambar Babban mutum bata shiga, ga waɗannan tuma-tuman matan nasa sun isheni da ƙorafe-ƙorafensu da baya ƙarewa. Gaba ɗaya Babban mutum bai yi sa’an aure ba. Bana son ganinsu ko kaɗan.”
Husna ta yi zaman dirshan a wurin ta kama cire takalminta da safa, tana cewa
“Kema Gwaggo kin so ki damu ne. Ni nayi zaton wani abu ne.”
Gwaggo ta watsa mata harara. Salma ta dubi Gwaggo ta ce,
“Gwaggo da zaki amince da na koma gidan Uncle M.Y da zama a can Kadunan. Sai indinga kulawa da komai ina kiranki ina yi maki ƙarin bayani.”
Gwaggo ta girgiza kai,
“A’a Salma, aure zaki yi ba zuwa zaman gadin wasu ba. Ki bar abinda ba zai yiwu ba.”
Salma ta langwaɓe kai ta ce,
“Gwaggo ni da bani da ko mashinshini? Kawai ki barni intafi.”
Gwaggon ta ɗan yi shiru cike da wani tunani. Sai kuma ta dubeta ta ce,
“Ku je ku cire kaya ku ci abincin tukun.”
Babu musu suka ƙarasa ciki. Sai bayan sun kimtsa, Gwaggo ta dubi Salma ta ce,
“Salma zaki iya auren Babban mutum?”
Ba Salma ba, hatta Husna da take rubutu sai da ta razana. A lokacinne kuma ta dinga danna biron har ta dinga rubuta shirme ba tare da ta sani ba.
“Tambayarki na yi, ba cewa nayi ki zuro min idanu ba.”
Salma ta sauke ajiyar zuciya tana jin lokacin cikar burinta ya kusa. Tabbas Allah baya barci.
“Gwaggo ke kaɗai gareni, ban taɓa musu da ke ba, duk yadda kika ce haka za ayi.”
Salima da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin Gwaggon ta ja tunga ta tsaya. Bata san lokacin da ta liliyo ashar ba. A lokaci guda ta ji jiri yana ɗibanta, dole ta ja da baya ta koma falonsu tana cewa,
“Bilki Amina ku zo ku ji, Gwaggo za ta yi wa M.Y aure.”
Dukkansu suka zaro idanu cike da firgici.
“Innalillahi… Yau mun ga ta kanmu. Ke waye ya gaya maki Salima? Shiyasa fa na tsani azo garin nan, dan nasan ƙofa ɗaya da ta rage ita Gwaggo ke harara.”
Bilki ta ƙarashe bayaninta da zaro idanu. Salima ta yi ajiyar zuciya ta ce
“Yanzu na ji tana cewa wai Salma ta aure shi. To ko zan yi yawo tsirara ne Salma bata isa ta shigo cikinmu ba. Kai ba ma Salma ba, Wallahi macen da za ta shigo a cikon ta huɗu ba ayita ba, bana jin kuma za a halicci uwarta bare ita.”
Amina dai bata ce ko uffan ba, don dukkansu haushi suke bata.
*****
Mu’azzam yana ta kwaso kayansa yana zubawa a wata ‘yar jaka. A lokacin ‘yar ƙaramar bindigarsa ta faɗo, ya dakata da shirya kayan da yake yi, ya ɗauki bindigar yana dubanta. A hankali ya manna mata sumba, sannan ya ɗauketa ya mayar cikin kayansa. Gidansu zai koma ba zai taɓa yarda ya yi tafiya da bindiga ba. Wani tunani kuma da ya yi, yasa ya ɗaukota ya cusa cikin jakarsa.
A lokacin Oga Saleh ya shigo da ƙaton tumbinsa yana duban Mu’azzam.
“Mu’azzam me yake damunka ne? Me ya sa kake da taurin kai?”
Mu’azzam ya dube shi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya fesar da zazzafan huci Yana dubansa ido cikin ido,
“Na gaya maka ni zan bar wannan sana’ar! Na tsaneku ne a ranar da kuka munafunceni. Anan gaba yaranka za su iya neman rayuwata. Don haka na haƙura ba don ina son inhaƙura ɗin ba. Akan me? Akan me zanje insiyar da rayuwata akanku, insiyar da ɗayar fuskata da babu mahaluƙin da ya sani, saboda infaranta maku, amma don butulci ni zaku renawa hankali?”
Ya ƙarashe yana ɗora ‘yar yatsarsa a ƙirjinsa alamun yana jin ciwo a duk lokacin da ya tuna.
Oga Saleh ya yi shiru, kamar ruwa ya ci shi. A lokacin kuma wasu mutane daga cikin tawagarsu suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya har su shida suka kewaye shi. Ɗaya daga cikinsu ya ƙaraso gaban Mu’azzam idanunsa jazir ya kama ƙafafunsa,
“Don Allah ka yafe min M.Y Wallahi anbani kuɗaɗenka dukka inbaka, ni ne na yi son zuciya na raba kashi uku na kai maka kashi ɗaya. Kuma… Kuma…”
Ya kasa ƙarasawa saboda yadda yaga Oga Saleh yana zazzaro jajayen idanu.
Bai tsira ba, daga irin tsawan da Oga Saleh ya daka masa,
“Zaka yi bayani ko sai na ɗauke numfashinka da bindigar nan?”
Tuni zufa ya dinga keto masa babu ƙaƙƙautawa ya ci gaba da cewa,
“Duk maganar da na kiraka na gaya maka ƙarya nake yi, kayi haƙuri. A ganina bai kamata inrigaka zuwa cikin harkar nan kai kuma ka fini ɗaukaka ba.”
Mu’azzam yana sane da akwai mutane da yawa da ke jin haushinsa, amma yafi amincewa sun fi jin tsoronsa akan shi kansa Ogan, kasancewarsa namiji mai zafin rai. Bai taɓa tunanin za su iya cire tsoro har su aikata masa haka ba, akan kuɗin da shi yasha wahala ya karɓo wanda ya ɗora burirrika akansu, daga ciki harda kai Gwaggo Hajji da dukka matansa.
Ji ya yi ƙarar bindiga ya cika ɗakin da suke, hakan yasa ya waiwayo da sauri yana duban gawan Mustapha a kwance. A hasale ya dubi Ogan ya ce,
“Akan me zaka kashe shi? Ni ya yi wa laifi kuma na yafe masa. Me ya sa ka kashe shi?”
Ya faɗa cikin hargowa kamar zai dake shi. Oga Saleh ya yi murmushi, kafin daga bisani ya ɗaure fuska kamar bai taɓa dariya ba,
“Ko kai ka ci amanata sakamakon da zaka samu kenan… Ya nemi ya jawo zubewan mutuncina a idanunka, shine kake tunanin inƙyale shi? Kana tunanin idan na ƙyale shi gobe yaran nan ba za su yi abin da yafi hakan ba?”
Ya sake dawo da murmushin fuskarsa, sannan ya fice daga ɗakin. Mu’azzam ya durƙusa yana duban Mustapha. Yanzu-yanzu yana numfashi yana magana, a cikin ‘yan mintuna ya tafi inda babu dawowa. Haƙiƙa Mustapha ya jima a wurin nan, yasha wahala, sai dai hakan bai amfana masa da komai ba, da ya wuce barin duniyar. Shikenan ya zo a banza ya koma a banza.
Ajiyar zuciya ya ƙwace masa a lokacin da suke ƙoƙarin ɗauke gawan. Ya dube su ya ce,
“Ina zaku kai shi?”
Ɗaya ya bashi amsa da,
“Oga ya ce mu kai shi daji mu ajiye shi angulu ya ci namansa.”
Mu’azzam ya girgiza kai ya miƙe ya ci-gaba da shirinsa hankalinsa yana gun Gwaggo…
A natse yake tuƙinsa yana jin kamar ya gama warware dukkan wata damuwa da ke cikin zuciyarsa. Yanzu burinsa kawai ya ganshi a cikin Gombe…
Cikin dare sosai ya iso, hakan yasa kai tsaye ya wuce sashen matansa. A falo ya same su duk suna zazzaune. Mamaki ya kama shi, musamman yadda basu yi farin ciki da isowarsa ba. Ya ɗan kalli Amina, wani lokacin takan bashi tausayi. Kowaccensu da abinda yafi so a wurinta, amma ya kasa tantance dalilin da yafi samun natsuwa da kasancewa da Salima.
Zama ya yi a gefen Salima yana faɗin,
“Wash Allah na… Lafiyarku ƙalau kuwa?”
Har Bilki ta buɗe baki zata koro masa jawabi, Salima ta kashe mata ido tare da taran numfashinsa,
“Hankulanmu ne duk ba a kwance ba. Bamu iya barcin kirki da baka nan.”
Ya dubeta duba na mamaki,
“Haba Salima har wata ɗaya ina yi, bana nan. Me ya sa baku taɓa kasa barci ba sai yanzu?”
Tana murmushi na kissa ta ce,
“Nan Gombe ne ba Kaduna ba. Yanzu dai sannu da zuwa.”
Ya yi murmushi, tare da sa hannu ya kirawo Amina kusa da shi. Nan da nan Salima ta murɗe fuska kamar bata taɓa dariya ba. A take ya ɗan daburce ya canza abinda ya yi ninyar gaya mata,
“Jeki ki kawo min fura don Allah.”
Ta ɗan yi shiru, dan ta zaci ko ya yi kewarta ne.
“Babu fura anan sashen sai dai ko wurin Gwaggo.”
Cikin natsuwarsa ya miƙe Yana faɗin,
“Bari inje da kaina kada ku tasheta.”
Abin mamaki hirarsu yake ji sama-sama alamun basu yi barci ba. Muryar Gwaggo ya ji raɗau tana cewa,
“Salma idan Allah yasa akayi aurenki da babban Mutum ki dage da kula da duk wani abu da yake so. Kinsani bayan mahaifinsa babu abinda nake so sama da shi.”
Husna ta ɗan turo baki ta kwantar da kanta a jikin Gwaggon ta ce,
“Gwaggo sai kuma ni… Bana so kina nuna kinfi son Uncle akaina, zaki raba kan ‘ya’yanki Allah.”
Gwaggo ta yi murmushi ta sake jawo Husna, yarinya mafi soyuwa agareta, idan aka cire M.Y
“Ke kuma ai ‘yar auta ce, yaushe zaki haɗa kanki da mutunin da ya zama babba?”
Sallamarsa yasa duk suka natsu. Fuskar Gwaggo Husna takaiwa duba yadda farin ciki ya lulluɓeta. Bata iya ɓoye ƙaunar da take yi masa ko a gaban waye. Yana tsaye yana ƙarewa Salma kallo yana kuma al’ajabin hirar Gwaggo akansa da Salma. Ya fi amincewa kansa tatsuniya take yi masu irin wanda ta saba yi, don haka ya ƙarasa jikin Gwaggo ya kwantar da kansa. Hakan yasa Husna ta yi sauri ta janye nata jikin, tana duban yanayin Salma.
Sun ɗauki a ƙalla mintuna biyar babu wanda ya iya magana,daga bisani ya kore shirun da cewa,
“Gwaggo kin yafewa ɗan marayanki?”
Ta yi murmushi irin na jin daɗi ta ce,
“Na yafewa babban mutum.”
Ya ɗago yana dubanta,
“Gwaggo fura zan sha.”
Husna tana jin hakan ta yi saurin rufe idanunta alamun barci, dan tasan Gwaggo za ta iya sanyata damun furar a daren nan.
“Buɗe idanunki ja’ira ki je ki damo masa fura. Ke kuma Salma ɗumama masa farfesun kayan cikin can ki kawo masa.”
Husna ta tashi ba dan taso ba ta damo furar ta kawo masa tare da gaida shi. Shi dai sai kallon Salma yake yi, yadda take jin kunyarsa. Hakan ya ƙara sanyawa ya ji kamar ya shaƙeta. Yana sha suna ‘yar hira, har ya fara jin idanunsa suna zafi. Dole ya yi mata sallama ya koma sashensa.
Wannan karon Salima ta sami abinda take so sosai a wurin M.Y domin kuwa a wurinta ya huce gajiyarsa.
Da safe, suna zaune dukkansu a falon suna karyawa, ya dubi yadda idanun Amina suka kumbura saboda kuka. Shi kansa ya sani, a matsayinta na amarya yafi ƙuntata mata.
Bayan ya kammala cin abincin ya miƙe zuwa sashen Gwaggo. Yau gaba ɗaya su Husna suna gida saboda babu Makaranta. Bayan sun gaisa ne ya dubi yadda Husna take gogawa Gwaggo maganin ciwon ƙafafu. Sai a lokacin ya tuna da maganin ciwon ƙafa da ya taho mata da shi. Ya dubi Husna ya ce,
“Ke jeki ki cewa Salima ta buɗe jakana zata ga maganin ciwon ƙafa ta baki ki kawo min.”
Da sauri ta fice zuwa inda ya aiketa. Salima tana zaune tana karkaɗa ƙafafu hannunta ɗauke da waya. Bayan ta koro mata aiken da akayi mata, bata sami amsa ba, sai da ta gama mulkinta sannan ta ce,
“Kije ɗakinsa jakar tana nan a gefen gado ki buɗe ki ɗauka. Ina hutawa babu wanda ya isa ya tadani.”
Jiki babu ƙwari ta kama hanya ta wuce.
Mu’azzam da ya tuna da bindigarsa, ya yi saurin miƙewa ya ce,
“Gwaggo ina zuwa.”
Bai jira jin Abinda za ta ce ba, ya yi gaggawan ficewa zuwa sashensa. A zaune ya sami Salima hakan ya ƙara faɗar masa da gaba ya dubeta a ɗan fusace,
“Ke ina maganin da nace ki ba Husna?”
Ta ɗago ta ɗan dube shi sannan ta ce,
“Ta shiga ta ɗauka da kanta.”
Bai jira komai ba ya afka ɗakinsa. A lokacin hannun Husna yakai kan bindigar, ta dinga shafata, daga bisani ta zaro domin ta ga menene. A razane ta miƙe ta yi jifa da bindigar bisa kan gado jikinta babu inda baya rawa. Ganin mutum a gabanta ya sake firgigita har ta yi ninyar saka ihu. Sai dai kamar ansa cingam anmanne bakin, sai hannu da ta cusa a cikin baki hawaye yana kwaranya. Abinda bai fahimta ba, tun fil azal Allah ya halicci Husna da tsoron bindiga. Ko Film ake kallo taga ana harbe-harbe zata gigice. Idan tafiya suke yi suka haɗu da soja ko ɗan sanda, muddin ta hango bindigar nan zata ruga da gudun gaske ta bar wurin.
Kuma ita ganin bindigar nan ta yi zaton Ɗan sanda ne kamar yadda Gwaggo ta yi mata gatse.
Yadda jikinta ke karkarwa yasa hankalinsa ya ƙara tashi. Kafin yasan abinyi ta fita da gudun gaske ta wuce Salima. Mamaki yasa Salima binta da idanu, daga bisani ta ja tsaki.
Tana shigowa ta ɓoye bayan Gwaggo, a lokacin da shi kansa ya biyo bayanta. Sai dai a bakin ƙofa ya tsaya ya kasa shiga sakamakon muryarta da ya ji tana magana cikin rawar baki,
“Gwaggo na shiga uku, bindiga na ɗauko a cikin jakar Uncle… Na shiga uku nasan mutuwa zan yi Gwaggo.”
Cikin tsananin gigicewa Gwaggo ta kama kafaɗunta dan tabbas tasan abinda zai iya sa Husna ta gigice har haka, babu shakka bindigar ce.
“Ke! Menene haɗin Babban mutum da bindiga da har zaki ganta a cikin jakarsa? Bana son shirme.”
Bakinta yana rawa ta ce,
“Wa… Wallahi bindiga ce Gwaggo mutuwa zan yi ko?”
Kafin ka ce me? Numfashinta ya koma sarƙewa, tuni ta sume a wurin. Ba Gwaggo ba, hatta shi kansa Mu’azzam ya shiga ruɗu.
‘Yar mutan Borno
I love d book
Very nice
I love the book too
Very nice
Very nice
Interesting
Nice one