Husna tana kwance a cinyar Gwaggo tun bayan da ta farfaɗo bata sake cewa uffan ba. Gwaggo ta kai dubanta ga Mu'azzam cikin sanyi ta ce,
"Babban mutum ina ka sami bindiga?"
Mu'azzam ya yi ajiyar zuciya, tare da kauda idanunsa daga cikin na Gwaggo ya ce,
"A wajen aikinmu aka ba mu, saboda yanayin lalacewar ƙasar, ban kai ga amfani da ita ba ma, sai da zan taho ne na cusa a cikin kaya kasancewar tafiyar dare ce. Kinsan babban dalilin bamu domin mu kare kawunan mune da na iyalanmu."
Gwaggo ta saki ajiyar zuciya, ko. . .