Husna tana tsaye tana kallon irin wannan ƙauna da ke tsakanin Gwaggo da M.Y haƙiƙa idan ta gansu a cikin irin wannan yanayin nata iyayen sukan faɗo mata a rai, harma ta yi kuka. Allah kenan baya barin wani dan wani, da ya bar iyayen Husna ko dominta. A hakan ta gode Allah da samun uwar riƙo kamar Gwaggo. Kullum nuna mata take yi, bata rasa iyaye ba, ita ce uwarta ita ce ubanta.
M.Y ya ɗago suka haɗa idanu, irin kallon da ya yi mata yasa ta yi saurin barin wurin, dan gaba ɗaya tsoronsa take ji.
A can ciki kuwa Mu’azzam ne ya tara matansa yana huci. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, zuciyarsa har wani ɗaci take yi. Daga ƙarshe ya nuna Bilki da yatsa ya ce,
“Ban taɓa raina iyayen wani ba, ba zan bari a raina min nawa iyayen ba. Da zan aureku Gwaggo tana da daman da zata hanani kuma inhanu, amma sai ta bini da addu’a. Dama a tunaninku da mata uku zan zauna? Mata huɗun nan sai na yi su insha Allahu. Ku ɓace min da gani.”
Duk suka kama hanya kowaccensu ta tsorata da yanayinsa. Salima ta rage a falon, ta ƙaraso cikin kissarta ta ce,
“Sai da na hana Bilki zuwa ta yi magana amma ta yi min kunnen shegu. A cewarta ƙarƙarinta dai ka ce zaka saketa sai kuma me? Amma kayi haƙuri don Allah.”
Mu’azzam ya sake fusata da abin da Salima ta gaya masa, hakan yasa ya sake bin Bilki har cikin ɗakinta. Sai dai yana zuwa ya sameta tana kuka, hakan yasa jikinsa ya yi sanyi, ya ja tsaki ya fice.
A zaune ya sami Gwaggo tana jin Radio idanunta ɗauke da hawaye. Da sauri ya ƙaraso yasa hannu ya goge mata hawayen ya ɗauke Radion ya kashe yana sake dubanta,
“Gwaggo idan naga hawaye a idanunki, bana sake samun natsuwa.”
Gwaggo ta ɗago ta ƙura masa idanu,
“Allah ya yi maka albarka babban Mutum. Ko bayan babu raina kada ka kusanci munanan ayyuka. Mahaifinka yana can kwance a ƙabari duk abubuwan da kake aikatawa yana ganinka. Na tabbata yana can yana alfahari da kai, nima yana sa min albarka da na iya riƙe amanar da ya bar min.”
Gwaggo ta numfasa sakamakon ruwan hawaye da ya cika mata idanu. Mu’azzam ya zauna a gefenta kansa a ƙasa ya ce,
“Gwaggo duk me ya kawo waɗannan maganganun kuma?”
Wannan karon kallon tausayawa take yi masa,
“Babu komai, yanzu nake ji a radio ankama masu garkuwa da mutane. Mahaifiyar yaron da aka kama take bani tausayi. Ko yaya zata ji? Wannan uwa da tasan abin da zata haifa kenan babu shakka da ta gwammace ta yi ɓarin cikinsa fiye da fitowarsa. Na taya ta jin ciwon wannan abun, musamman ma da yaron ya tabbatarwa hukuma iyayensa suna bakin ƙoƙarinsu akansa. Babban mutum, na gode maka Allah ya yi maka albarka.”
A karo na farko da kunya ta lulluɓe shi, a karo na farko da ya fara tunani mai zurfi a rayuwarsa. Tausayi kansa da mahaifiyarsa ya dira a zuciyarsa.
Miƙewa ya yi ya fice yana jin tarin damuwa danƙare a zuciyarsa. Da zai iya da a yau ne yafi dacewar ya bar wannan aikin tun kafin ranar da uwarsa za ta yi danasanin haihuwarsa. Yana roƙon Allah kada Allah yasa ya riski wannan ranar yana raye. Da ya ga wannan baƙar ranar gara ya ga ranar mutuwarsa.
Kamar ance ya dubi gefensa, Husna ya gani ta yi tagumi tana dubansa kamar tana son tambayarsa abinda ke damunsa, sai kuma ya ga ta sunkuyar da kanta. Idan bai yi ƙarya ba a haɗa idanun da ya yi da ita hawaye ke kwance a idanunta. Ji ya yi kamar ya je ya tambayi dalilin kukanta. A lokacin Salma ta ƙaraso, wannan karon ta rage kunyarsa da take ji. Ta ɗan dube shi,
“Uncle M.Y wai kun kusa tafiya?”
Mamaki ne ya kasa barinsa don haka ya tsaya kawai yana dubanta. Hakan yasa Husna itama ta kafe su da idanu tana mamakin ƙarfin hali irin na Salma.
“Uncle kamar kada ku tafi.”
M.Y ya rasa me zai ce mata sai kawai ya sake dubanta sama da ƙasa ya ce,
“Wai ke! Shekarunki nawa?”
Sai da ta ɗan yi jim, kafin ta ce,
“Goma sha tara.”
A duniyarsa ya tsani ƙananan mata masu ƙananun shekaru. Yarinya tana shekaru ashirin da biyar ma, baya ɗaukarta ta girma, bare wannan ‘yar tatsitsiyar.
“Kinsan menene aure?” Ya tambayeta yana kallon tsakiyar idanunta. Sunkuyar da kanta ta yi, saboda kwarjininsa da yake dukanta.
Za ta yi magana Salima ta fito. Ai sai Husna ta sake gyara zama ta tsura masu idanu.
“Ke me kike yi anan?”
Salima ta buƙata cikin ɓacin rai. Nan da nan Salma ta ruɗe ta fara kame-kame. Kafin wani lokaci ta ɓace a wurin. Husna ta saki murmushi tana jin wannan aure ba mai yiwuwa bane muddin Gwaggo tana son rayuwar Salma ya yi kyau. Baiwar Allah za a cusata cikin manyan mata waɗanda suka fita wayo da gogewa.
Salima ta saƙalo hannunta wuyansa, hakan yasa Husna ta miƙe da sauri har tana tuntuɓe. Mu’azzam ya kauce yana dubanta cike da wani tunani,
“Ke baki jin kunyan mutane ne?”
Tana dariya ta ce,
“Kunyar me zan ji? Mijina ne fa.”
Shima murmushin ya yi ya wuce wajen motarsa cike da wani tunani da yake ganin ba mai bullewa bane.
‘Yar mutan Borno