Skip to content
Part 7 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Cikin ikon Allah Mu’azzam ya tarkata matansa suka bar Gombe cike da kewa.

Sai a lokacin Husna ta sami kanta cikin sakewa sosai, duk da lokaci zuwa lokaci matansa sukan faɗo mata a rai.

Yau Husna ta dawo Makaranta ta sami sunyi baƙi hakan yasa ta gaishe su ta koma gefe guda ta zauna tana sauraren maganganunsu.

“Husna ta girma Gwaggo.”

Ɗaya daga cikinsu ya furta, yana sake kallonta. Haka kawai take jin haushin irin kallon da yake mata. Gwaggo ta yi murmushi ta ce,

“Husna baki gane su ba ko? Yaron Gwaggonki Hajara ne. Shi ne wanda mahaifinki ya yi masa alƙawarin aurenki tun kina ƙarama. Yanzu ya sami aiki ya zo ne akan maganar aurenku.”

Gabanta ya faɗi da ƙarfi, bata san lokacin da ta ɗago tana dubansa ba. Yanzu dama tana da ɗan uwa kamar wannan bai taɓa zuwa ya dubata ba? Sai rana tsaka ya zo da maganar aure?

Girgiza kanta ta yi ta ce,

“Gwaggo kinyi alƙawarin barina inyi karatu mai zurfi. Me zai sa yanzu ace aure kuma? Shekaruna sha bakwai a duniya yaushe na isa aure?”

Gwaggo ta riƙe baki tana kallon Bappan Kabiru, ta ce

“Ikon Allah. Zamani kenan. To uwarki ma da aka tashi aurenta shekarunta goma sha biyu a duniya, kuma gashi ta haifeki.”

Kabiru kuwa a lokaci guda ya ji ya amince da wannan haɗi, domin Husna ta yi masa ko ta ko ina.

Gwaggo ta mayar da kallonta ga Bappa ta ce,

“Kana ji ko Basiru? Ba zamu tsaya jira su gama makaranta ba, sai a haɗa bikinsu da na Babban mutum. Nan da wata uku idan ya yi maka kawai sai a ɗaura.”

Duk suka yashe baki suna jinjina son zumunci irin na Gwaggo Hafsi. Husna kuwa tashi ta yi ta fice waje ta nemi wani wuri can ta zauna ta yi tagumi gabanta yana tsananta faɗiwa. A lokacin Salma ta ƙaraso kusa da ita ta cire mata tagumin tana dubanta,

“Me ya faru?”

Sai a lokacin ta ji hawaye mai ɗumi ya kwaranyo mata ta ce,

“Wai aure Gwaggo zata yi min.”

Salma ta yi murmushi ta ce,

“Don Allah kada wannan ya dameki. Ni yanzu tashin hankalina ma Sahabi. Ya ce Wallahi ba zai haƙura ba, wai naci amanarsa. Cikin ikon Allah kuma hankalina yafi kwanciya akansa Wallahi. Ina tsoron matan Uncle M.Y kada su kasheni.”

Ta ƙarashe kamar zata yi kuka. Husna ta dubeta,

“Nima tsoron da nake jiye maki kenan Yaya Salma. Matan Uncle dukka basu da kirki za su iya yin komai.”

Duk suka sake yin shiru, daga bisani Salma ta kamo hannayenta ta ce,

“Mu ci gaba da addu’a. Kuma zan ja maki kunne, duk rintsi kada ki yarda kiyi musu da Gwaggo. Ta cancanci kowane irin biyayya ne mu yi mata. Gwaggo tana da hawan jini da likita ya yi gargaɗi akan ɓata mata. Don Allah ki guji dalilin ɓacin ran Gwaggo don Allah.”

Husna ta share hawayenta tare da gyaɗa kai,

“Insha Allahu zan kiyaye.”

Kaduna

Mu’azzam ne yake kaiwa da komowa a falonsa cikin damuwa. Abubuwa sun yi masa yawa akai ta yadda ya rasa me ke yi masa daɗi. Ga ɓacin ran yadda gidansa kaca-kaca kaman wanda ya tara garke a gidan. Ya tsani ƙazanta, sai ya yi dace da dukka matan basu damu da gyaran cikin gidan ba. Masu aikin ma da su da babu su duk ɗaya. Komai suka gadama shi suke yi saboda sun rasa mai kwaɓa masu. A haka Salima ta dawo daga unguwa ita da wata ƙawarta da gani kasan ‘yar duniya ce. Kamar jira yake ya dira kanta da masifa,

“Ku wasu irin ƙazamai ne? Yanzu don Allah gidan nan yana maku kyan gani kenan? Gaskiya ba zan ɗauki shashancin nan ba. Akan me? Ko kunya baku ji?”

Salima ta ɗan yi yaƙe saboda kunya, bata iya ce masa komai ba har ya fice yana ci gaba da mita.

Can gidansu da ke cikin dokan dajin ya nufa, anan ya ɗan sami sassauci ganin komai a gyare tsaf… Jamilu ya shigo yana dubansa sannan ya ce,

“Ka tashi ka je Oga yana son ganinka.” Kamar yace ba zai je ba, sai kuma ya miƙe ya tafi.

“M.Y kana da taurin kai ko? Me ya sa zaka saki yaran can bayan babu wanda ya kawo kuɗin fansarsu?”

Shiru ya yi, dan yasan za a rina. Ogan ya yi ta faɗa amma ya kasa cewa komai har ya ƙarashe da cewa,

“Zan hukuntaka Akan abinda ka aikata, da abu mafi muni a rayuwarka, idan kuma ka kasa aiwatarwa Wallahi sai kayi danasani, don kuwa akan mahaifiyarka zai ƙare.”

Zuciya ce take cinsa, sai dai ya yi alƙawarin ba zai taɓa tankawa ba. Shi gaba ɗaya ya rasa meke yi masa daɗi. A can gida yana ganin babban laifinsa da ya kasa tsayawa ya zama namiji a gidansa, ya kasa sauke hakkin da ke kansa akan iyalansa, don hakane yake ganin komai ba bisa daidai ba.

A karo na farko tausayin Amina ya dirar masa. Yaushe rabon da ya bata hakkin aure? Gara Bilki ƙila zata fita dauriya. Yasa hannu ya shafi suman kansa, yana son ya gyara kuskurensa amma ta yaya? Ko ya yi ninyar gyarawa baya taɓa iyawa. Kiran wayar Gwaggo ne ya shigo wayarsa. Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe su, a duk lokacin da yake cikin wani hali sai ya ga kiran mahaifiyarsa, haka zalika bata kashewa sai ta tabbatar hankalin ɗanta a kwance yake. Yana son mahaifiyarsa baya haɗa sonta da na kowa.

Bayan ya gyara Muryarsa  ya amsa kiran yana mai jin nishaɗi tare da warwarewar dukkan matsalarsa.

“Gwaggon ɗan maraya.”

Ya kirawota cikin wani shauƙi. Ta amsa da fara’arta. Bayan gaisawa da suka yi ta gaya masa duk yadda akayi akan auren Husna. Bai san dalilin da yasa ya damu da auren da Gwaggo zata yi wa Husna ba, duk da yasan ƙanƙantarta yake dubawa. Baya jin ko ‘yar shekaru ashirin da biyar zai iya kallonta a matsayin mace har ya kwanta da ita, gani yake kamar ba ƙaramin zalunci bane. Ba zai iya cewa Gwaggo komai ba da ya wuce Allah ya sanya alkhairi. A ƙarshen maganarsu ta jefe shi da kalaman nan da ya kamata ace ya zame masa jiki, sai dai ya kasa sabawa da su.

“Kaji tsoron Allah a dukkan abubuwan da ka sanya a gaba. Ka guji haram domin baka da sabulu da ruwan wanke dattinsa.”

Jiki a sanyaye ya ajiye wayar yana jujjuya kalamanta.

Bindigarsa ya ɗauka yana shafata a hankali. Yau yasan za su fita aiki, ya zama dole ya nemawa kansa natsuwa tun kafin ya ƙara ɓatawa ogansa.

*****

Idan ƙirgan da Husna take yi daidai ne saura sati biyu a ɗaura aurenta da Kabiru, Salma kuma da Uncle M.Y Gwaggo kaɗai take rawar ƙafafunta, sai kuwa Kabiru da ya zama maye akan Husna. Daga nan kuwa M.Y baisan ma suna yi ba. Domin a ‘yan kwanakin ya zama busy sosai, da ƙyar yake samun kansa. Duk da hakan yana ƙarfafawa Gwaggo guiwa akan yana tare da ita.

A lokacinne kuma Gwaggo ta matsa dole sai Kabiru ya ɗauki Husna ya kaita gidan Mu’azzam domin ya sa mata albarka tunda shi ya ƙi zuwa. Shima sai aka ci sa’a a lokacin zai je Kaduna bikin wani abokinsa.

Bayan Gwaggo ta gayawa M.Y ya ce a’a ta bari zai zo da kansa kafin bikin, amma Gwaggo ta ce a’a bata yarda ba tasan halinsa. Dole Husna tana ji tana gani Kabiru ya ɗauketa a motarsa suka kama hanyar Kaduna. Duk yadda yaso ko ‘yar hira su dinga yi abin ya faskara. Gabanta kuwa sai tsananta faɗiwa yake yi, tana jin wani irin ƙunci wanda bata taɓa jin irinsa ba.

Tunda aka gayawa M.Y su Husna suna hanya hankalinsa ya gaza kwanciya, shi kansa ya rasa dalilin da baya farin ciki da wannan tafiya.

A hanya motar ta sami matsala sai da akayi ta gyarawa. Ita kuwa Husna daga ruwa sai Biskit suka shiga bakinta, ta ƙi cin komai, sai ma zazzaɓi da ke ƙoƙarin rufeta. Dare ya riga ya yi masu a hanya, a lokacin kuma sun daina magana da M.Y sai Matarsa Bilki da suke ta magana da ita. Suna gab da shiga garin Kaduna suka ga antare hanya, a zatonsu jami’an tsaro ne sai dai suna yin parking suka tabbatar da sun shiga hannu.

Ƙarar bindiga da ya cika kunnuwanta, da kuma yadda aka saita su da bindiga yasa ta ji ƙwaƙwalwarta tana juyawa. Salati kawai Kabiru yake yi cikin tsananin ruɗewa.

A lokacin kuma aka kwashe su akayi cikin daji da su. Husna kuwa tafiya kawai take yi bata san inda take sa ƙafafu ba.

A lokacin ta ji tashin maganganu da bata fahimtar duk abubuwan da suke cewa, har zuwa lokacin da ta ga ana haskota da tocila, ɗayan su yana nunata.

Kabiru ya riƙe hannunta yana girgiza kai, amma suka fincikota suka yi wani wurin da ita. Abin da zata iya tunawa taga mutum a tsaye akanta, ba zata sake tunawa da abin da ya faru ba.

Wani daga cikin su ya zo ya sami Kabiru da aka tsare shi da bindiga sauran kuwa tuni anyi gaba da su, ya jawo Kabiru suka fita bakin titi kusa da motarsa sai a lokacin ya waiwaya kawai yaga Husna a bayan motar a shimfiɗe bata motsi. Da ƙyar ya iya kunna hasken cikin motar, ya yi ido biyu da jini a ƙafafunta, hakan yasa ya tada motar cikin gigicewa ya yi cikin gari da ita ba tare da yasan wani asibitin zai je da ita ba.

<< Mu’azzam 6Mu’azzam 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×