Giwa hospital nan ne babban asibiti kuma mafi kusa, don haka ya garzaya da ita can cikin tashin hankali.
*****
Sannu a hankali ta buɗe idanunta tana kallon ko ina.. Anti Amina ce tsaye akanta, wanda ita kaɗai ta gani, a lokacin ne kuma ta ji murya sama-sama hakan yasa ta waiwaya tana kallon ƙofar ɗakin da zai sadaka da inda take kwance. Gwaggo ce ta shigo a ruɗe idanunta sun yi jazir saboda kuka.
Kai tsaye gadon ta tinkaro tana cewa,
"Innalillahi Wa Innaa ilaihirraji un... Husna! Husna!! Me ya sameki?"
Jikin Mu'azzam har wani. . .