Bappa da Kabiru sun sami isowa, sun zauna sun tattauna da Gwaggo akan lallai ayi auren nan bayan Sati biyu, kasancewar barinta haka zai sa ta dinga yawan tunani da shiga damuwa. Gwaggo ta amince da wannan shawara. Kabiru ya nemi da ya ga Husna, Gwaggo ta nuna masa ɗakin da take ita kuma suka ci-gaba da tattaunawa.
Abinci ta tasa a gaba ta kasa ci, sai ruwan hawaye da ke tsiyaya a bisa kuncinta. Ko da ya yi sallama ta ji shi tsaf, amma ko uhumm bata ce ba. Ya nemi wuri ya zauna yana leƙen fuskarta.
“Husna.” Ya kirawo sunanta a hankali. Kamar ba zata ɗago ba sai kuma ta ɗago tana dubansa.
“Me ya sa ba zaki yarda da ƙaddara ba? Me ya sa ba zaki yi haƙuri ba? Kin ga yadda kika koma saboda damuwa? Ni ne wanda zan aureki, tunda ban juya maki baya ba, bai kamata ki shiga damuwa irin hakan ba.”
Husna ta ɗan ji sanyi a zuciyarta, har ma ta goge hawayen fuskarta tana dubansa kamar zata yi magana, sai kuma ta kauda kanta.
Ya jima yana mata nasiha da lallashi har ya samu takai cokalin abinci baki. Bayan sun koma ne, Gwaggo ta tara matan M.Y a falo tana dubansu duba na mamaki ta ce,
“Ku kam haka kuke yi a birni? Ku fita waje kuna kwalliya amma a muhallinku abin babu kyan gani? Ko ni da nake ƙauye bana iya zama ɗakina da datti, bare ku da kuke ganin kun fi kowa wayewa.”
Duk suka yi mata shiru har ta gaji da sababi ta bar masu falon.
*****
Da daddare misalin sha biyu, sawu duk ya ɗauke, baka jin komai sai kukan tsuntsaye. Ƙishin ruwa ya addabi Husna hakan yasa ta fito falon. Ji ta yi tana ɗan ganin jiri hakan yasa ta nemi wuri ta zauna shiru.
A lokacin ta ji motsin buɗe ƙofa. Da sauri ta waiwaya tana duban ƙofar. Amina ce ta fito ita da wani yaro da ba zai wuce shekaru ashirin ba. Kwata-kwata Amina bata kula da Husna ba, don haka suna fitowa falon ta sake rungume yaron tana bashi sumba. Wannan ke nuna mata alamun bankwana suke yi. Tunda take ganin mace mai ƙarfin hali bata taɓa ganin kamar Amina ba. Ita ta buɗe masa ƙofa ya fice. Shigowarta ya yi daidai da ganin Husna hantar cikinta ya kaɗa. A lokacin shi kuma M.Y ya fito daga ɗakinsa shi da Salima.
Abin da Husna ta fahimta a kwanaki biyun nan da ta yi a gidan, Salima kaɗai ke shiga sashen maigidan. Duk ta zuba masu idanu. M.Y ya dubi Amina da mamaki ya ce,
“Daga ina haka daga ke sai ɗaurin ƙirji?”
Yadda yake mata kallon tuhuma yasa ta kama rawar baki,
“Motsi naji shi… Shi ne naje in duba.”
Duk suka zaro idanu,
“Idan kinji motsi sai ki buɗe min ƙofa? Wannan wani irin rashin hankali ne?”
Amina ta ɗago idanunta cike da hawaye, a duk lokacin da ta aikata zina da aurenta daga baya tana kwana kukan danasani, sai dai tsananin sha’awa baya barinta tuba na har abada. Duk da matasan suna biya mata buƙatarta, amma har gobe ta kasa samun cikakken namiji kamar mijinta. Duk macen da ta yi sa’a ta same shi a shimfiɗa bata bukatar neman wani namiji, don ko ta ina cikakken namiji ne kuma lafiyayye. Sai dai kash! Sai da ya lasa mata zuma a baki sannan ya dawo ya janye kansa ya koma gun mace ɗaya. Idan ma ta matsa masa sai ya ce bai da lafiya neman magani yake yi, hakan nan zata haƙura.
Akwai ranar da ta afka ɗakinsa yana tare da Salima, yanayin da ta gansu ya ɗaga mata hankali. Da farko ya ji kunya, daga baya sai ya kama yi mata masifa akan shigo masa ɗaki, bata ce masa komai ba ta ƙyale shi.
Duk da ta sani Allah ne ya kamata, saboda son ta ga dukiyarsa ne ya kawo ta ga aurensa, da ta hakura ta maida kwadayinta ta auri daidai ita da hakan bai faru ba, da bata yi lalacewar da za ta nemi wani a gidan aurenta ba, sai gashi da ta shigo gidan ya rage bata komai da ya saba a waje, ya canja mata kamar ba M.K me hannun Alherin da ta sani ba.
Yadda take dubansa ne ya hana shi sake furta komai. Shi kansa bai kula da Husna a wurin ba, har sai da ya ƙaraso tsakiyar falon.
Sosai ya dubeta yana jin wani abu yana taɓa masa zuciya,
“Husna me kike yi anan a cikin daren nan?”
Tsananin tsanar da take yi masa a matsayinsa na ɗa namiji ya ƙaru. Gabaɗaya ƙyamarsu take ji. Gida ne mai cike da ƙazanta wanda duk wani ɗan kirki ba zai yi fatan ya tsoma kansa a cikin gidan ba.
Shi kuwa M.Y gabaɗaya baya cikin hayyacinsa tun ranar da aka sanar da shi ga Husna ankawota asibiti sakamakon fyaɗe, bai sake jin wani abu mai kama da farin ciki ba. Ya tuna kalaman da Kabiru ya yi masa washegarin ranar da abun ya faru,
“Kasan me ya fi ɗaure min kai ne Hamma? Duk sun kwashemu sun yi cikin daji da mu, daga baya da aka hasko fuskarmu ni da Husna sai aka tsaidamu daga tafiyar da muka fara yi cikin jejin. Can kuma Na ji suna ƙusƙus, shi ne suka tasa Husna, ni kuma suka tsaidani da bindiga. Sauran kuma aka tasa ƙyeyarsu. Abin ƙarin mamaki bayan sun gama ta’asar ashe sun ɗauketa sun kai cikin motata, daga bisani nima suka dawo da ni wurin motar. Ban taɓa ganin masu garkuwa da mutane irin waɗannan ba, tambayoyi ne akaina birjik! Amma na kasa samo amsoshinsu, babbar tambayar ita ce me Husnah ta musu? Idan mata suke so me yasa ba za su je inda lalatattun suke kamar jamfa”
Har ya gama bayaninsa M.Y bai ce da shi ci kanka ba, sai ma zuciyarsa da ke yi masa raɗaɗi.
Ajiyar zuciya ya ƙwace masa, ya dubeta ya tabbatar ba zata yi magana ba, don haka ya juya ya koma ɗakinsa. Salima tana shirin biyo shi ya rufe mata ƙofa a fuska. Dole kowaccensu ta koma ɗakinta.
Husna dai tana nan zaune ta kasa koda motsi. Ji ta yi ta sake tsanar gidan, don haka ta koma ɗaki da ninyar zata cewa Gwaggo su tafi kawai ta sami lafiya.
Da asuba bayan sun idar da Sallah Husna ta sanya mata rigima sai sun koma gida, babu shiri ta nemo M.Y ta ce gida za su tafi. Shi kansa yana buƙatar su yi nesa da shi, ko hakan zai sa fara’arsa da walwalarsa su dawo. Domin ƙiris yake jira ya fara ciwon hauka. Bayan ya sallamesu sun kama hanya, ya nufi gidansu da ke cikin dajin yana jin kamar ya fita daga ƙaya.
Jamilu ya samu a cikin ɗakinsa yana ta shaye-shayensa wanda ya riga ya zame masa jiki, bai cika sanya shi maye ba.
A karo na farko ya dubi kayayyakin dake gaban Jamilu ya ji wani abu ya darsu a zuciyarsa. A baya sun sha yin faɗa da Jamilu akan shaye-shaye har ya gaji ya zuba masa idanu.
“M.Y kana cikin hayyacinka kuwa? Ka ga yadda duk ka zama?”
M.Y ya riƙe kansa da ƙarfi yana jijjiga shi.
“Jamilu haukacewa zan yi Wallahi! Komai baya yi min daɗi, bana iya barci Jamilu, komai ya kwance min. Ka taimakeni ka gaya min abin da zan yi ko barcin insamu inyi, rayuwar nan ta isheni ta yi min ƙunci.”
Jamilu ya dube shi da jajayen idanunsa, da gaske M.Y ya bashi tausayi matuƙa. Wasu ƙwayoyi ya miƙa masa,
“Karɓi wannan kasha. Muddin kana son raba kanka da dogon tunanin da zai iya kasheka to ka dinga afa ƙwaya, zaka nemi duk wani tashin hankali ka rasa, kuma zaka dinga barcinka cikin natsuwa.”
Babu dogon tunani ya ɗibi ƙwayoyin ya zuba a baki ya taune su, daga bisani ya sha ruwa. Tuni barci mai ƙarfi ya yi awon gaba da shi. Jamilu ya dube shi cike da tausayawa. Allah ya ɗora masa son M.Y kwata-kwata bashi da ninyar cutar da shi, sai dai a ganinsa ta hanyar nan ne kaɗai zai samu hankalinsa da kowa ya kasa gane kansa. Bargo ya jawo masa ya fice zuwa falo yana gaya masu su rage sautin da suka kunna M.Y yana barci.
*****
Husna ce kwance a cinyar Gwaggo, a cikin motar da ke ta sharara gudu bisa kwalta. Bata san me ya sa take jin kamar kuskure mai girma suka tafka na barin gidan M.Y a irin wannan lokacin ba. Gabanta yana faɗi da ƙarfi, tana jin kamar wani abu ke shirin faruwa wanda bata fatan ya shiga cikin ahlin M.Y.
Ji take yi kamar shikenan ta baro Kaduna, bari na har abada. Ta tsani garin tsana mai tsanani.