Tana sauraren likitocin da suka tabbatarwa Alhajin babu abin da ya sameta da ya wuce jiri, ba mamaki tana ɗauke da yunwa. Hajiya Mami dai tana zaune ta zubawa Husna idanu. Alhajin ya jawo kujera yana dubanta sosai,
"Ke daga ina kike? Kuma ina zaki je?"
Husna ta dinga zazzare idanu tana dubansu, sai can ta buɗa baki ta ce,
"Nima bansan inda zanje ba. Nasan dai a hannun kishiyar Innata nake. Na mance sunan garinmu."
Jikin Hajiya Mimi ya yi sanyi, don ba zata taɓa mance izayar kishiyar uwa ba. Zuhura ma ta ji tausayinta matuƙa. . .